Ranar Mata: UNICEF Da Jihar Jigawa Sun Horar Sa Mata 600 Shirin Jari Bola
Published: 10th, March 2025 GMT
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Jigawa, sun fara horas da mata 600 kan inganta muhalli ta hanyar bola jari.
Shugaban Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Jigawa JISEPA, Alhaji Adamu Sabo ya bayyana haka a wajen taron tunawa da ranar mata ta duniya da kuma fara horaswar da aka gudanar a Dutse.
Alhaji Adamu Sabo ya ce, baya ga jajircewa, da juriya, da nasarorin da mata suke da, bikin ya yi duba kan irin rawar da mata suke takawa wajen dorewar muhalli da bunkasar tattalin arziki.
Ya jaddada cewa ta hanyar shirin bola jari, watiWaste to Wealth Initiative, za su iya baiwa mata damar kare muhalli da kuma samar da kyakkyawan yanayi ga iyalansu.
Shugaban hukumar ya bayyana cewa, duk da kalubalen da ake fuskanta a duniya a fannin sarrafa shara, da kuma yadda ake zubar da shara ba bisa ka’ida ba, da ke barazana ga muhalli, har yanzu akwai damar da za a iya maida sharar da aka tara a gida zuwa dukiya.
Ya ce horon zai koyar da mata yadda za su yi kasuwanci da sharar da suka tara a gida, tare da tabbatar da karfafa tattalin arziki da kuma inganta muhalli.
Ya kara da cewa, hakan zai baiwa mata matasa damar ba da gudumawa wajen samun kudaden shiga a gida da kuma ci gaban tattalin arzikin kasa.
Bugu da ƙari, shugaban na JISEPA ya bayyana cewa horaswar za ta yi amfani da shirin da UNICEF ta fara na “Samun Damarar Kasuwanci ga Matasa” (YOMA), wani sabon tsarin na dandali ta yanar gizo, da ke haɗa matasa daga ko’ina a fadin duniya don koyon kasuwanci, da samun kuɗi, da tasirin zamantakewa.
Adamu Sabo ya yabawa masu ruwa da tsaki da suka goyi bayan wannan shiri da suka hada da kungiyar jari bola ta Najeriya WAPAN, da gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi bisa goyon bayan da suka bayar.
A jawabinta lokacin da take bayyana bude horaswar, uwargidan gwamnan jihar Jigawa, Hajiya Amina Umar Namadi, ta yaba da kokarin hukumar da sauran masu ruwa da tsaki da suka taimata wajan samun nasarar horon.
Ta ce shigar da mata cikin shirin inganta muhalli ba shakka zai samar da wani tasiri, ba a Jigawa kadai ba har ma a duniya baki daya.
Ta yi kira ga mahalarta taron da su yi amfani da damar da suka samu wajen inganta rayuwarsu, baya ga ba da gudummawa wajen tsaftace muhallinsu.
Taken ranar Mata ta Duniya ta 2025 shi ne, “Bayar Da Dama ga Mata da ‘Yan Mata: Hakkoki, Daidaito, da Ƙarfafawa, “wanda ke kira ga bai wa mata hakkokinsu, da samar musu da damarmaki, ba tare da an bar su a baya ba.”
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Ranar Mata
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Mene ne Tasirin Shirin NYSC Bayan Shekaru 50 Da Kafa Shi?
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Shirin bautar ƙasa wanda aka kafa tun a shekarar 1973, an ƙirƙire shi da nufin haɗa kan matasa daga kowane lungu da saƙo na ƙasar nan, domin fahimtar juna da kawar da wariyar yanki da ƙabilanci.
Amma a yau, bayan shekaru fiye da arba’in da biyar da fara wannan shiri, jama’a da dama na tambaya —ko har yanzu shirin na da tasirin da aka kirkire shi domin shi?
Ko har yanzu bautar ƙasa NYSC na ci gaba da samar da haɗin kai da ake buƙata a Najeriya?
NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Arewa Ke Tafiya Kudu FarautaShirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan ko har yanzu kwalliya na biyan kudin sabulu kan kafa shirin bautar kasa?
Domin sauke shirin, latsa nan