Iran Ta Ce Shirinta Na Makamashin Nukliya Na Zaman Lafiya Ne, Kuma Ba Zata Tattauna Da Amurka Karkashin Barazana Ba
Published: 10th, March 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce shirin makamashin Nukliyar kasar Iran, na zaman lafiya ne, kuma babu wani shiri na samar da makaman Nukliya a cikinsa, sannan ya kara da cewa Iran ba za ta taba shiga tattaunawa da kasar Amurka mai cin zalin wasu kasashe ba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi ya na fadar haka a shafinsa na X a yau Litinin, ya kuma ce wannan ita ce martanin Iran a kan sakon da Amurka ta ce aikawa jami’an gwamnatin kasar Iran, na cewa su zabi tattaunawa ko yaki.
Kafin haka Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana hakan, ya kuma kara da cewa, kasashen yamma musamman Amurka ba su tuhumi Iran da kokarin mallakan makaman Nukliya ba, sai dai suna nufin tursasawa kasar ne, don ta mika kai garesu a kan dukkan al-amura.
Imam Khaminai ya kara da cewa, da Iran za ta mika kai dangane da shirinta na makamashin nukliya, da gobe kuma zasu ce, yaya batun makamanki masu linzami idan ta amin ce, sai su kawo batun siyasarta a gabasa ta tsakiya da sauransu. Don haka bukatunsu ba za su kare ba sai sun mamaye kasar gaba daya.
Ministan ya kammala da cewa, tattaubawan ta Trump yake kiran Iran zuwa gareshi tursasawa ne. idan da tana batun tattaunawa ne, da gaske. To da yarjeniyar JCPOA ya wadatar. Sai tunda wani abu ne daban, take amfani da tursasawa, wanda kuma yake iya kaiwa ga yaki.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran : Wadanda Suka Dage Kan Tattaunawa Da Iran, Na Yi Ne Don Amfanin Kansu_ Jagora
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce dagewar da wasu kasashe masu cin zarafi suka yi na yin shawarwari da Iran na yi ne don neman amfanin kansu.
Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da manyan jami’ai na bangarori uku na gwamnati a ranar Asabar.
Jagoran ya ce “Dagewar da wasu gwamnatoci suka yi kan yin shawarwari ba wai don warware al’amura ba ne, a’a yana nufin aiwatar da abin da suke so.”
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: ” Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta amince da abin da suke tsammani ba.”
Wadannan gwamnatocin da suke cin zalin ba sa neman yin shawarwari kan batun nukiliya kawai; A maimakon haka, suna amfani da shawarwari a matsayin “hanyar cimma manufofinsu” a fannoni kamar karfin tsaron Iran da karfin kasa da kasa, wadan ko shakka babu Iran za ta yi watsi dasu.
Ya kara da cewa, suna tabo batun tattaunawar ne domin matsa lamba kan ra’ayin jama’a, don haka Iran ta ki yin shawarwari da su, duk da cewa sun nuna a shirye su ke.