Aminiya:
2025-03-10@21:35:39 GMT

Yadda za a samu rufin asiri da sana’ar ɗinki — Muhammad

Published: 10th, March 2025 GMT

Wani matashi mai sana’ar ɗinki, Malam Muhammad Sani Tela ya bayyana cewar, ya shafe fiye da shekara 30 ya na ɗinki.

Ya ce wannan sana’a ta zama tamkar jini da tsoka a gare shi sakamakon yadda ya riƙe ta da hannu bibbiyu.

Ko dai Gwamna Fubara ya yi murabus ko a tsige shi — APC An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa

Ya ƙara da cewar, wannan sana’a ta ɗinki sana’a ce da ke da matuƙar albarka idan ka sa juriya a ciki domin kuwa ba sana’a ce da za ka tara kuɗi akai-akai ba nan take.

“Sai dai kuma muddin ka tsayar da gaskiya tare da cika alƙawari to lalle za ka samu babban rufin asirin da baya misaltuwa domin kuwa a kullum in ka fito to kuwa za ka samu abin da za ka yi cefanen gidan ka da sauran buƙatu.

A cewarsa, ya samu fa’ida sosai a wannan sana’a ta ɗinki, domin a cikin ta ya yi aure har ma da ‘ya’ya da sauran kadarori.

“Alhamdulillah, kuma babu abin da ya taimaka min na cimma nasara fiye da jajircewa a kanta.

“Kamar kowace sana’a ita ma sana’ar ɗinki t na da nata irin ƙalubalen domin kamar a shekarar da ta shude sakamakon matsalar rayuwa da al’umma suka samu kansu ciki sai da ta kai ga wannan sana’a ta mu ta samu tasgaro na rashin samun ɗinki.

“Domin lokacin ba ta kayan sawa ake yi ba, jama’a na fafutukar abin da za a ci ne ba’a batun ɗinka sutura.

“Amma a bana lamarin sai godiya domin ya kasance muna ɗinkin sosai idan an kwatanta da shekarun baya.

“Saboda yadda ake samun ɗinki tuni mun rufe karɓar ɗinkin sallah sakamakon al’umma sun fara dawowa hayyacin su saboda sauƙin rayuwa.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: wannan sana a ta

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda Al’ummar Kasar Sin Ke Tabbatar Da Hakkinsu Na Demokuradiyya 

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda Al’ummar Kasar Sin Ke Tabbatar Da Hakkinsu Na Demokuradiyya 
  • Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-Rufai
  • NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin Azumi
  • Sa’adatu Ali JC ta raba wa mata 150 injinan markaɗe a Gombe
  • Za Mu Bai Wa Maraɗa Kunya A Wasanmu Da Manchester United – Arteta
  • Makahon da ke sana’ar POS
  • Da A Ce Ni Ba Dan Fim Ba Ne, Da Na Zama Malamin Addinin Musulunci -Baba Rabe
  • Kwararru Sun Nuna Fargaba Kan Yadda Wasu Makiyaya Ke Bai Wa Dabbobinsu Magunguna Barkatai
  • Nijeriya Ta Samu Damar Karɓar Baƙuncin Taron Hulɗa Da Jama’a Na Duniya Na 2026