Leadership News Hausa:
2025-03-11@18:25:14 GMT

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [3]

Published: 11th, March 2025 GMT

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [3]

Wannan magana ta al-imam Ibnu Juzai tana bayani ne kan abubuwa huɗu da ke hana mutum bin Allah da kuma yadda za a magance kowanne daga cikinsu. Ga ƙarin haske akan haka:

1. Shaiɗan: Shaiɗan shi ne abokin gaban mutum na ƙoli tun daga haihuwarsa har mutuwarsa. A matsayinsa na maƙiyi, burinsa shi ne ya ɓatar da mutum daga bin Allah.

Yana amfani da hanyoyi daban-daban kamar waswasi, da sanya shubuha, da ƙarya, da kawar da zuciya daga ibada, da sanya shakku a cikin imani, da sauran makirce-makircensa. Allah Ya umurce mu da kada mu bibiyi tafarkin shaiɗan a rayuwarmu.

Maganin Shaiɗan: Babban maganin Shaiɗan shi ne neman tsari da kariya a kansa a wurin Allah, da sɓa masa, Wato mutum ya yi ƙoƙarin yin akasin abin da Shaiɗan ke umarta. Idan Shaiɗan yana kiran mutum zuwa ga zunubi, ya yi ƙoƙarin kaucewa.

2. Son Zuciya: Zuciyar mutum tana da buƙatu da sha’awa, kuma tana iya karkatar da shi daga tafarkin gaskiya. Idan mutum bai kula ba, zuciyarsa za ta janyo masa son abin da bai dace ba, ko kuma nuna ƙyama ga abin da Allah ya shar’anta wanda hakan zai kai mutum da barin Allah da addinsa. Don haka; dole ne mutum ya kula da gyaran zuciyarsa.

Maganin Son Zuciya: Maganin son zuciya shi ne mutum ya fi ƙarfin ta, Wato mutum ya tilasta wa zuciyarsa bin gaskiya, ko da kuwa tana son akasin haka. Tanƙwara ta ta bi gaskiya, yana nufin horar da zuciya kan gaskiya da bin umurnin Allah. Hakan na faruwa ne ta hanyar tilasta wa kai yin biyayya, ta hanyar salla da azumi, da ambaton Allah, da kasancewa cikin kyawawan ayyuka tare da addu’a Allah Ya tsarkake ta.

3. Duniya: Duniya tana da ruɗi da ƙawanyar ƙyaleƙyale, tana janyo hankalin mutum zuwa ga jin daɗi kamar samun dukiya, ko matsayi, da sauran abubuwan da ke iya karkatar da shi daga bin Allah. Allah ya bayyana cewa duniya ruɗi a wurare daban-daban a cikin Alƙur’ani, hakanan Hadisai masu yawa sun yi bayani a kan ruɗin da duniya take yi wa mutane.

Maganin Duniya: Guje wa ƙyaleƙyalenta da ruɗinta, Wato mutum ya fahimci cewa duniya ba ta da daraja idan aka kwatanta da lahira, kuma bai kamata ya jefa kansa cikin ruɗinta ba, domin ba ta da tabbas. Mutum ya kasance mai tsoron Allah da ƙoƙarin bin dokokinsa a kowane hali.

4. Halittu (Mutane): Mutane na iya zama sanadin da zai hana mutum bin Allah, musamman idan yana koyi da su a kan abin da ba daidai ba. Akwai waɗanda za su janyo mutum cikin halayen banza ko su hana shi aikata alheri, ta yadda hakan zai lalata masa zuciya, domin zama da maɗaukin kanwa yana kawo farin kai.

Maganin Mutane: Karkata ga Allah Shi kaɗai, wato mutum ya yi ƙoƙarin maida hankalinsa ga Allah kaɗai, ba wai ya dogara da mutane ko kuma ya dinga yin abubuwa don faranta musu ba. Hakanan mutum ya nilisanci biyayya ga mutane idan a cikin abin da yake ɓata; Idan mutane suna jagorantar mutum zuwa ga ɓarna, ya kamata ya guje musu.

Zaɓar abokai nagari yana taimaka wa mutum wajen zama nagari. Ya zaɓi waɗanda za su taimaka masa wajen bin Allah, ba waɗanda za su janye shi zuwa ga halaka ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Abu Razina Nuhu Ubale Paki

এছাড়াও পড়ুন:

El-Rufa’i ya sauya sheƙa daga APC zuwa SDP

Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya tabbatar da sauya sheƙa daga jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar zuwa jam’iyyar SDP.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da ya wallafa ranar Litinin ne a shafukansa na sada zumunta.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da matashi a Kano Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi Patrick Adaba ya rasu

El-Rufai ya ce, “yanzu na yanke shawarar komawa jam’iyyar Social Democratic Party, kuma zan kasance a cikin ta wajen tafiyar da al’amurana na siyasa a nan gaba.

Kwanakin baya a lokacin tattaunawarsa da kafar talabijin ta Arise, El-Rufa’i ya bayyana cewa “jam’iyyar APC ta sauka daga kan manufofin da aka assasa ta tun fil-azal.”

Ya yi zargin cewa jam’iyyar ta gaza kiran taron shugabanninta na ƙasa tsawon shekaru, wanda ya ce hakan ya saɓa wa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

A yanzu dai wannan ya kawo ƙarshen raɗe-raɗin da ake yi na inda tsohon gwamnan zai nufa bayan raba gari da jam’iyyar APC.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gina Mutane Don Bunkasa Hazakarsu Na Daga Cikin Ajendar Sin Na 2025
  • El-Rufa’i ya sauya sheƙa daga APC zuwa SDP
  • El-Rufa’i ya fice daga APC ya koma SDP
  • New York Times: Isra’ila ce ta kashe wasu fursunoninta da ake tsare da su a Gaza
  • Sharhin Bayan Labarai: Kasashen Afirka Sun Kori Sojojin Faransa Daga Kasashensu
  • Muhimmancin Karfafa Iyali Wajen Sadaka A Watan Ramadan
  • Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [1]