Shugaban kasar Ghana, John Darmani Mahama ya nemi kungiyar Ecowas da ta amince da kungiyar kawancen kasashen Sahel din nan guda uku da suka balle daga cikinta.

Mista Mahama, ya bayyana hakan a kafofin sada zumunta a ranar Litini jim kadan gabanin ya ziyarci kasar Burkina faso, bayan ya kai irin wanan ziyara kasashen Mali da Nijar.

Ci gaba da huldar tattalin arziki da kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso, na daga cikin jigon rangadin da shugaban Ghana ya kai a kasashen na AES.

Bayan birnin Bamako a ranar Asabar, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya je birnin Yamai a ranar Lahadi, inda wasu rahotanni ke cewa ya je ne da nufin dinke barakar da ke tsakanin kungiyar ta raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) da kasashen uku na Sahel.

Saidai a cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na Nijar, hukumomin kasar sun tabbatar da cewa kasashen sun tabbatar da aniyarsu ta karfafa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin kasashensu a fannonin siyasa, tattalin arziki da tsaro.

Kafin Nijar, John Dramani Mahama ya je Mali inda Janar Assimi Goïta ya tarbe shi. A cewar fadar shugaban kasar Ghana, ganawar da aka yi tsakanin mutanen biyu ta ba da damar fara tattaunawa kan karfafa hadin gwiwa a fannin tsaro.

Shugaban na Ghana ya kuma yi amfani da wannan dama wajen bayyana mahimmancin kasuwanci ta hanyar tashoshin jiragen ruwa na Ghana da ke Tekun Atlantika ga Mali.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Tarayyar Turai Ta Yi Maraba Da Tattaunawa Tsakanin IRAN da Amurka Kan Shirinta Na Makamashin Nukliya

Kungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da tattaunawa tsakanin Amurka da JMI dangane da shirinta na makamashin Nukliya, tare da kara jaddada cewa hanyar diblomasiyya kadai ta rage don warware wannan matsalar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a halin yanzu dai kungiyar tarayyar ta Turai ta na ci gaba da takurawa JMI da takunkuman tattalin arziki, masu  tsanani, a lokaci guda tana fadar cewa hanyar Diblomasiyya ce kadai ta rage wajen warware matsalar shirin makamashin nukliya na kasar Iran, wanda ya tabbatar da fuska biyu na kasashen na Turai.

Labarin ya kara da cewa, wani mai magana da yawun kungiyar ta EU wanda kuma baya son a bayyana sunansa, ya fadawa kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran kan cewa, babu hanyar da ta rage wajen warware matsalar shirin makamashin nukliya na kasar Iran sai hanyar Diblomasiyya.

Ya kumakara dacewa kungiyar tana maraba da duk wani ci gaba a wannan bangharen. Mai maganan ya kara da cewa wakilin EU a MDD ya yi wannan bayanin a gaban kwamitin tsaro na MDD a yan kwanakin da suka gabata.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Hukumar Makamashin Nukliya Ta Kasar Iran Ya Ce Dukka Ayyukan Makamashin Nukliya A Cikin Gida Suna Tafiya Da Karfinsu
  • Xi Jinping Zai Ziyarci Kasashen Vietnam Da Malaysia Da Cambodia
  • Tawagogin gwamnatin Kongo da kungiyar M23 sun isa  Doha domin tattaunawa
  • Shugaban Kasar Amurka Yace Yana Kokarin cimma yarjeniya da kasar China Dangane da Tiktok
  • ECOWAS ta damu da takun-tsaka tsakanin Aljeriya da Mali
  • Yadda Kasashen Afirka Za Su Iya Rage Illar Harajin Amurka
  • Sharhin Bayan Labarai: Yakin Kasuwanci Tsakanin Amurka da Kasashen Duniya
  • Shugaban Kasar Iran Ya Ce Iran Ba Zata Jada Bayan Ba A Kan Shirinta Na Makamashin Nukliya
  • Tarayyar Turai Ta Yi Maraba Da Tattaunawa Tsakanin IRAN da Amurka Kan Shirinta Na Makamashin Nukliya
  • Majalissar Dokokin Rasha ta amince da yerjejeniyar huldar ta shekara 20 da Iran