Zelensky ya je Saudiyya domin tattaunawar zaman lafiya
Published: 11th, March 2025 GMT
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya isa kasar Saudiyya domin ganawa da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, gabanin wata muhimmiyar ganawa tsakanin tawagogin Ukraine da na Amurka domin share fagen shawarwarin zaman lafiya da Rasha a nan gaba.
Taron dai na nuni da wani gagarumin yunkurin diflomasiyya na magance rikicin da ke faruwa a Ukraine kuma zai iya ba da damar tsagaita bude wuta a cewar rahotanni.
Tattaunawar da za a yi a Jeddah ita ce ganawa ta farko tsakanin jami’an Ukraine da Amurka tun bayan ziyarar da Zelensky ya kai fadar White House a karshen watan Fabrairu da ya gabata, wanda ya haifar da cacar baki baki mai zafi tsakaninsa da shugaban Amurka Donald Trump.
Tun bayan hakan ne, gwamnatin Washington ta dakatar da taimakon soji ga Ukraine, lamarin da ya sa Kyiv ta nemi sulhu.
Zelenskyy ya bayyana cewa, “Muna fatan tattaunawa tare da amincewa kan shawarwari da ayyukan da suka dace,” yana mai jaddada cewa Ukraine na goyon bayan tattaunawa mai ma’ana tare da son a yi la’akari da muradunta.
Taron na ranar Talata zai mayar da hankali ne kan kafa tsarin zaman lafiya da tsagaita bude wuta tsakanin Rasha da Ukraine.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Miƙawa Gwamnatin Borno Mutane 75 Da Suka Ceto
Da yake jawabi a wurin taron, Maj.-Gen. Waidi Shuaibu, kwamandan OPHK, ya ce matakin na daga cikin kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya a yankin da kuma dawo da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.
Shuaibu ya jaddada aniyar rundunar na dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas ta hanyar kawar da barazanar masu tada kayar baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp