HausaTv:
2025-04-12@07:17:03 GMT

Iran ta soki matakin Amurka na hana shigar da wutar lantarki Iraki

Published: 11th, March 2025 GMT

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya soki matakin da sabuwar gwamnatin Amurka ta dauka na janye sassaucin da ta yi wa Iraki na shigo da wutar lantarki daga Iran.

Araghchi ya bayyana matakin da gwamnatin Trump ta dauka a matsayin “abin takaici.”

Ya kara da cewa gwamnatin Amurka ta na kokarin hana al’ummar iraki samun ababen more rayuwa kamar wutar lantarki, musamman gabanin watanni masu zafi na wannan shekara.

Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya sake jaddada goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga al’ummar Iraki.

Ya kara da cewa Iran ta tsaya tsayin daka kan kudurin ta ga gwamnatin Iraki na dakile ayyukan Amurka da suka sabawa doka.

Kalaman Araghchi sun zo ne bayan da Amurka ta sanar da janye sassaucin da ta yi wa Iran wanda ya bai wa Iraki damar shigo da wutar lantarki daga makociyarta ta gabas.

A martaninsa, shugaban kwamitin kudi na majalisar dokokin Iraki ya yi gargadin cewa duk wani mataki da Washington za ta dauka na takaita shigo da wutar lantarki daga Iran zai haifar da rugujewar wutar lantarki a Iraki.

A halin yanzu, kusan kashi 80 cikin 100 na makamashin da ake samu a Iraki ya dogara ne da iskar gas, wanda hakan ya sa kasar ta dogara sosai da Iran don ci gaba da samar da wutar lantarki.

A watan Yulin 2022, Iraki ta sanya hannu kan kwangilar shekaru biyar da Iran don samar da megawatt 400 na wutar lantarki.

A watan Maris din shekarar 2024, an cimma wata yarjejeniya ta kara yawan iskar gas din Iran zuwa mita cubic miliyan 50 a kowace rana, wanda darajarsa ta kai dala biliyan 6 a duk shekara.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: da wutar lantarki

এছাড়াও পড়ুন:

Iran: Akwai damammaki na diflomasiyya da za mu jarraba aniyar Amurka a kansu

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baqaei ya bayyana cewa, ma’a, kwana guda gabanin tattaunawar da ake jira a kasar Oman tsakanin Amurka da Iran kan shirin nukiliyar kasar Iran, damammaki da daman a diflomasiyya da Amurka za ta iya tabbatar da aniyarta a kansu

Baqaei ya rubuta a dandalin  X, “Ya kamata Amurka ta mutunta wannan shawarar da aka yanke duk da cewa ana fama da rikici.”

“Ba za mu yanke hukunci ba, Muna da niyyar tantance niyyar dayan bangaren kuma za mu tabbatar da hakan a wannan Asabar,” in ji jami’in diflomasiyyar na Iran, ya kara da cewa Iran “za ta yi tunani kuma ta mayar da martani ga kowane mtaki.”

A ranar Litinin shugaban Amurka Donald Trump ya ba da sanarwar cewa gwamnatinsa za ta shiga tattaunawa da Iran.

A ci gaba da tattaunawar da za a yi a ranar Asabar, bangarorin biyu  sun yi musayar kalamai masu zafi, inda Trump ya yi barazanar daukar matakin soji idan tattaunawar ta ci tura.

Dangane da gargadin na Trump, wani babban mataimaki ga jagoran Iran Ayatollah Sayyed Ali Khamenei ya ce Iran za ta iya daukar matakan da duk ta ga sun dace a kan wannan lamari.

Taron na ranar Asabar na zuwa biyo bayan wata wasika da Trump ya aikewa Sayyed Khamenei a watan da ya gabata, inda ya bukaci Tehran da ta shiga tattaunawa tare da yin gargadin cewa matakin soji na kan teburi idan Iran ta ki amincewa.

Tehran ta bayyana aniyar ta na shiga tattaunawar kai tsaye amma muddin Washington ta ci gaba da manufofinta na “mafi girman matsin lamba”.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilin Nijeriya Na Karbo Bashin Dala Biliyan 12 Daga Kasar Japan
  • Iran: Akwai damammaki na diflomasiyya da za mu jarraba aniyar Amurka a kansu
  • Mai damfarar fursunoni ya gurfana a kotu a Kano
  • Cutar Kwastomomi: NERC ta ci kamfanonin rarraba lantarki tarar N628m
  • Trump ya janye harajin da ya kara wa duniya, amma ya laftawa China 125%
  • Sin Ta Kara Wasu Kamfanonin Amurka 12 Cikin Jerin Wadanda Ta Dakatar Da Fitar Musu Da Wasu Kayayyaki Daga Kasar Sin
  • Sin Ta Kara Buga Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigarwa Kasar Daga Amurka Zuwa 84%
  • Tarayyar Turai Ta Yi Maraba Da Tattaunawa Tsakanin IRAN da Amurka Kan Shirinta Na Makamashin Nukliya
  • China Ta Karawa Kayakin Masu Shiga Kasar Kudaden Fito Har Zuwa Kashi 84%
  • Iran ba ta amince da Amurka ba, amma za ta gwada su (Araghchi)