Kamar yadda ta riƙa kasancewa a shekarun baya bayan nan, bana ma dai jami’an tsaro sun haramta al’adar nan ta tashe da aka saba gudanarwa daga zarar an kai azumi na goma a watan Ramadana.
Auwalu Sani Nalako, Sarkin Gwagwaren Kano kuma jagoran dabbaka al’adar tashe ne ya tabbatar hakan yayin hirarsa da manema labarai a ranar Litinin.
Nalako ya ce dalilai na tsaro da rundunar ’yan sandan jihar ta bayar ne ya sanya su ma suka dakatar da wasannin tashen na bana.
A cewarsa, jami’an tsaron sun tattaro bayanan sirri da ya tabbatar musu da cewa akwai miyagu waɗanda suke shirin fakewa da tashen domin tayar da hargitsi.
A shekarun baya dai an riƙa samun wasu ɓata-gari da ke ribatar lokacin gudanar da wannan al’ada suna kai hare-hare kan waɗanda ba su ji ba ba su gani ba.
Al’adar tasheBisa al’ada dai ana yin wasannin tashe ga wanda ya yi aure amma ya mutu, da gidajen masu kuɗi, sarakuna, da sauransu.
Tashe wata al’ada ce da ake gudanarwa daga kwana 10 na watan Ramadan har zuwa daren sallah.
Masu tashe, yawancinsu ƙananan yara, cikin shiga ta ban dariya, sukan zaga kwararo-kwararo a unguwanni da kasuwanni suna nishadantar da mutane da abubuwan barkwanci da ba’a da dai sauransu domin debe musu gajiyar azumi.
Aminiya ta binciko muku asali da tarihi da sauran muhimman abubuwa game da wannan al’ada da ke gudana a cikin watan Ramadan mai alfarma, a kasar Hausa.
Asalin kalmar tasheMasana sun bayyana cewa asalin tashe ana yin sa ne da dare, kuma bakuwar al’ada ce da malam Bahaushe ya samu daga baya.
Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza malami ne a Sashen Koyar da Harsunan Najeriya a Jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sakkwato.
Ya bayaya wa Aminiya cewa, “Kalmar tashe ta samo asali ne daga a tashi, wato a tashe su daga barci.”
Tarihin tasheIta dai wannan al’ada a cewar Farfesa Bunza, ba a san bahaushe da ita ba sai bayan zuwan Musulunci kasar Hausa.
Tashe “Ya samu tarihin Bahaushe ne a watan azumi na Ramdan; wannan ya nuna bakon abu ne, domin gabanin zuwan Musulunci babu,” inji shi.
Ya ce masana al’ada na ganin tashe ya samo asali ne daga Daular Andalus, “Can ne Musulmi suka kusa kusanta da al’adu, domin da kidin taushi da tashe duk daga can suka samo asali.”
Dalilin yin tasheFarfesa Bunza ya bayyana cewa asalin makasudin yin tashe shi ne a tayar da mutane daga barci su yi sahur a watan azumin Ramadan.
“Har yanzu [a Daular Andalus] suna yin tashen, wanda za a tayar da mutane da dare domin su samu su yi sahur.”
Daga baya “Abin ya koma wasan yara na jan hankalin jama’a da faranta musu rai da debe musu gajiya da takaici da wahala.”
Tashe a al’adar BahausheA ƙasar Hausa akan fara yin tashe ne a 10 na tilas, wato kwana 10 na biyu cikin watan Ramadan domin sanya wa mutane nishadi.
Bahaushe ya kasa watan azumin Ramadan zuwa gida kuna: ‘10 Na Marmari’, ‘10 Na Wuya’, da kuma ‘10 Na Ɗokin Sallah’.
Malamin ya bayyana cewa Bahaushe ya zaɓi ‘10 Na Wuya’ a matsayin lokacin fara tashe.
“A ‘10 Na Marmari Bahaushe ya ga bai ma kamata a yi tashe a lokacin ba, sai an shiga 10 Na Wuya, lokacin an ɗan fara gajiya da azumin.
“Saboda haka sai a riƙa yin tashe ana sa mutane fara’a da farin ciki, su kuma suna ba da kyauta da sadaka.”
Muhimmancin TasheGame da hikima da kuma amfaninsa, Farfes Bunza ya ce tashe kan nuna duk yanayi da mutane suke ciki a shekarar, kuma akwai darasi a cikinsa.
“Su yaran suna kokarin su bayyana halayya da duk wani yanayi da mutane suke ciki.
“Da za a saurari tashen yaran za a ga manyan maganganu ne da manya suka sa musu a baki.
Ya ce, “Cikin tashe ana gina wa yara kunya, kokari, kwazo, son gaskiya, son juna da sauransu.”
Tasirin tashe“Malamai sun gaya mana cewa tashe shi ne musabbabin samuwar wasu fitattun mawakan kasar Hausa; daga wakokin tashe suka samu shahara, maza da mata.
“Saboda haka tashe wani abu ne na sada zumunci da kokarin lurar da mutane [irin] halin da ake ciki, da yadda ya kamata a fuskance su.
“Don yanzu ga shi nan na ga wata yarinya tana tashe a kan bilicin, ba mamaki a samu wata kuma tana tashe a kana ta’addanci.
“Mu nuna wa mutane cewa ta’addanci fa ba zai yiwu ba, dole mu zauna lafiya; saboda haka yaran nan karatu ne suke mana mai zurfi.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Kano watan Ramadan Bahaushe ya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Sahayoniya ta hana Falasdinawa masu ibada yin I’itikafi a Masallacin Al-Aqsa
A yammacin ranar Alhamis da ta gabata ce sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka aukawa Falasdinawa masu ibada bayan sun gudanar da sallar tarawihi a masallacin Al-aqsa, inda suka kore su daga masallacin da karfi, tare da hana su yin I’itikafi a cikin masallacin.
Da yake tsokaci a cibiyar yada labaran Falasdinu, Ziad Abhais, mai bincike kan al’amuran birnin Kudus, ya jaddada cewa, matakin da gwamnatin sahyoniyawa ta dauka na hana masu ibadar I’itikafi a cikin masallacin Al-Aqsa wani mataki ne na cin zarafi da kuma muzgunawa hakkokinsu na addini.
Ya kara da cewa: Sojojin yahudawan sahyoniya suna amfani da hakan ne don shimfida ikonsu a kan masallacin Al-Aqsa, domin kuwa a shekara ta 2015 an ba da izinin yin I’itikafi a cikin wannan masallaci a duk ranakun watan Ramadan.
Hukumar bayar da agaji ta Musulunci a birnin Kudus ta sanar da cewa sama da masu ibada dubu 80 ne suka gudanar da sallar isha’i da tarawihi a harabar masallacin Al-Aqsa mai albarka a yammacin ranar Alhamis, wadanda akasarinsu mazauna birnin Kudus ne da yankunan da yahudawa suka mamaye a shekara ta 1948.
A daidai lokacin da watan Ramadan ya shiga, sojojin Isra’ila sun jibge dakaru masu yawa a birnin Kudus da kuma kewayen masallacin Al-Aqsa don hana Falasdinawa masu ibada shiga masallacin .