UNRWA ta bukaci Isra’ila da ta bari a shigar da kayan agaji a Gaza
Published: 11th, March 2025 GMT
UNRWA ta yi kira ga Isra’ila da ta kawo karshen hana shigar da kayan agaji a zirin Gaza domin dakile bazuwar yunwa da wahala a yankin.
“Mun riga mun ga alamun farko na karin farashi a kasuwa,” in ji Kwamishinan UNRWA Philippe Lazzarini yayin taron manema labarai a wannan Litinin, ya kara da cewa yayin da lokaci yake kara kurewa, tasirin haramcin yana karuwa a Gaza.
Lazzarini ya kara da cewa “akwai hadarin komawa ga yanayin da muka fuskanta watannin da suka gabata, game da kara yaduwar yunwa a tsakanin mutanen zirin Gaza sakamakon matakan da Isra’ila take dauka.
“Isra’ila” ta sanar da dakatar da isar da kayayyakin jin kai zuwa Gaza a ranar 2 ga Maris, tare da yin barazanar kara matsin lamba kan Hamas, yayin da bangaren ‘yan gwagwarmayar Falasdinu ya ki amincewa da shawarar Amurka na tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta farko, maimakon shiga mataki na biyu kamar yadda yarjejeniyar tanada tun daga farko.
A wani mataki na baya-bayan nan na kara matsa lamba kan al’ummar zirin Gaza, Ministan Makamashi na Isra’ila Eli Cohen ya sanar da cewa, ya rattaba hannu kan wata doka ta katse wutar lantarki a yankin Gaza daga ranar 9 ga Maris, yana mai jaddada cewa “Isra’ila za ta yi amfani da dukkan kayan aikinta wajen dawo da mutanen da aka yi garkuwa da su, da kuma tabbatar da kawo karshen samuwar Hamas a cikin Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gidauniyar Marayu Riyadissalihin ta Funtua Ta Raba Kayayyakin Ramadan
Shugaban Kwamitin Tallafa wa Marayu na Riyadissalihin Funtua, Alhaji Lawal Mekaji (Madugun Kasuwar Funtua), ya yi kira ga al’umma, musamman iyaye da masu hannu da shuni, da su bada gudunmawa wajen tallafa wa marayu da inganta rayuwarsu.
Ya yi wannan kira ne yayin da yake raba kayan sutura da abinci ga marayu a Funtua a wani bangare na kokarinsa na yada albarkar watan Ramadan.
A cewarsa, kula da marayu ba kawai nauyin zamantakewa ba ne, amma wata gagarumar ibada ce da ke karfafa kyawawan dabi’u a cikin al’umma.
Da yake jawabi yayin taron rabon kayan, sakataren gidauniyar, Bashir Muhammad King, ya bukaci wadanda suka amfana da kayayyakin da su yi amfani da su ta hanyoyin da suka dace.
Ya kuma mika godiya ga duk wadanda suka bayar da gudunmawa domin nasarar shirin, yana mai jaddada cewa irin wannan karamci yana da matukar tasiri wajen kawo fata da sauki ga rayuwar mabukata.
Taron rabon kayan ya kasance mai cike da farin ciki da godiya daga marayu da masu kula da su, wanda hakan ya kara nuna muhimmancin hadin kan al’umma wajen daga darajar rayuwar marayu da marasa galihu.
COV/Magaji Yakawada