Kimanin fararen hula 1,000 ne aka kashe tare da jikkata wasu daruruwa a hare-haren jiragen yaki marasa matuki a nahiyar Afirka, yayin da ake ci gaba da yin amfani da jirage marasa matuka a nahiyar.

A cewar jaridar The Guardian, masu sharhi da nazari na cewa , daga shekara ta 2021 zuwa 2024, jami’an tsaro a kasashe daban-daban na nahiyar Afirka sun yi amfani da jiragen yaki marasa matuka wajen kai hare-hare, wanda kuma sau tari ana kashe fararen hula ne, maimakon masu aikata laifuka.

Dole ne wannan ya kawo karshe, kuma dole ne kasashen duniya su dauki matakai da suka dace waje saka kaidoji kan amfani da jiragen yaki marasa matuka, domin rashin yin hakan zai ci gaba da yin sanadin salwantar rayukan fararen hula da basu bas u gani ba, in ji Cora Morris, jami’a a cibiyar sanya ido kan amfani da makamai ba bisa ka’ida ba da ke da mazauni a Burtaniya..

An tabbatar da cewa jirage marasa matuka masu dauke da makamai sun kashe fararen hula a kasashen Afirka masu yawa sakamakon tashe-tashen hankula, da hakan ya hada da kasashen  Sudan, Somalia, Nigeria, Mali, Burkina Faso, da Habasha, inda akasarin hare-hare sun faruwa ne a wadannan yankuna.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: jiragen yaki marasa marasa matuka fararen hula

এছাড়াও পড়ুন:

Kasashen Turai sun goyi bayan shirin Larabawa na sake gina Gaza

Manyan kasashen Turai, da suka hada da Burtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya, sun goyi bayan shawarar Masar na sake gina Gaza a matsayin mai adawa da shirin “riviera” na shugaban Amurka Donald Trump wanda ke ba da shawarar korar Falasdinawa da karfi daga yankin.

Duk da goyon bayansu da kuma wanke ayyukan kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tun farkon yakin a watan Oktoban 2023, ministocin harkokin wajen Birtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya sun sanar a cikin wata sanarwa a ranar Asabar cewa sun amince da shirin Masar wanda zai inganta “mummunan yanayin rayuwa da Falasdinawa suke ciki a Gaza.”

Sanarwar ta kara da cewa, “Shirin ya nuna wata hanya ta sake gina Gaza idan aka aiwatar da hakan cikin gaggawa.

A ranar Asabar ne kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC mai mambobi 57 ta amince da shawarar kungiyar hadin kan kasashen Larabawa a hukumance kan sake gina Gaza a wani taron gaggawa da ta gudanar a kasar Saudiyya.

OIC ta bukaci “kasashen duniya da cibiyoyin bayar da kudade na kasa da kasa da na shiyya-shiyya da su gaggauta ba da tallafin da ya dace ga shirin.”

Wani cikakken daftarin shirin sake gina Gaza da Masar ta gabatar ya hada da ware dala biliyan 53 don sake gina gina yankin, da kuma batun kafa kwamitin gudanarwa domin tafiyar da yankin zirin Gaza.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yemen zata sake kai hare-hare kan jiragen ruwan Isra’ila
  •  Ukraniya Ta Hai Wa Birnin Moscow Hari Da Jirage Marasa Matuki
  • Nijeriya Ta Shigo Da Man Fetur Na Naira Tiriliyan 12 A 2024 – Rahoto
  • Sojojin Ruwa Na Kasashen Rasha Da China Sun Shigo Kasar Iran Don Fara Atisayen Sojojin Ruwa Mai Suna “Damarar Tsaro 2025”
  • Alummomin duniya na ci gaba da yin Allah wadai da kisan fararen hula a Siriya
  • Sharhin Bayan Labarai: Kasashen Afirka Sun Kori Sojojin Faransa Daga Kasashensu
  •  Syria: Kungiyoyi Masu Dauke Da Makamai Suna Ci Gaba Da  Kai Wa Kauyukan Lazikiyya Da Tartus Hare-hare
  • Kasashen Turai sun goyi bayan shirin Larabawa na sake gina Gaza
  • Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto