Aminiya:
2025-03-12@06:20:26 GMT

Tsohon shugaban Philippines ya faɗa komar ’yan sanda

Published: 11th, March 2025 GMT

’Yan sanda sun cafke tsohon shugaban ƙasar Philippines,  Rodrigo Duterte a filin jirgin saman birnin Manila a wannan Talatar.

Mista Duterte ya faɗa komar ’yan sandan ne bisa sammacin Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, jim kaɗan da saukarsa daga birnin Hong Kong.

Jihohi 12 da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet Ainihin abin da ke kawo wa Manchester United koma baya

Hatsaniya ta ɓarke a filin jirgin saman lokacin da ’yan sanda suka kama Mista Duterte, sakamakon tirjiya daga masu tsaron lafiyarsa da likitansa da kuma lauyoyinsa, wadanda ke zargin cewa an take masa haƙƙinsa da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi.

Fadar shugaban ƙasar Ferdinand Marcos ta ce tsohon shugaban na fuskantar tuhumar kisan ɗimbin jama’a a lokacin mulkinsa, wanda ya fake da yaƙi da masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

A lokacin dai ya sha alwashin kawar da fataucin miyagun ƙwayoyi, amma ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’dama sun ce lamarin ya rikiɗe zuwa wani abu daban, inda ake zargin ’yan sanda da kashe dubban mutane, ciki har da waɗanda da ba su ji ba ba su gani ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kotun Duniya

এছাড়াও পড়ুন:

Ficewar El-Rufai Daga APC Babban Rashi Ne – Tsohon Hadimin Buhari

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • DAGA LARABA: Asalin Tashe Da Tarihinsa A Ƙasar Hausa?
  • DAGA LARABA: Ko Kun San Asalin Tashe Da Tarihinsa A Ƙasar Hausa?
  • EFCC Ta Kama ‘Yan China 4, Da Wasu Mutum 27 Kan Zargin Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Jos
  • Ficewar El-Rufai Daga APC Babban Rashi Ne – Tsohon Hadimin Buhari
  • ‘Yan Sanda Sun Fara Bincike Kan Kisan Shugaban Kungiyar Miyetti Allah A Kwara
  • El-Rufa’i ya sauya sheƙa daga APC zuwa SDP
  • Tsohon Gwamnan Kaduna El-Rufai Ya Koma SDP
  • An samu tsohon shugaban hukumar tsaron Faransa da zamba
  • Tsohon shugaban hukumar tsaron Faransa na fuskantar zargin zamba