HausaTv:
2025-03-12@06:20:47 GMT

Fim Din “Habibullah” Na Iran Ya  Sami Kyauta Ta Koli A Poland

Published: 11th, March 2025 GMT

Fim din na “Habibullah” wanda Adnan Zandi ya fitar da shi, ya sami kyautar ne a wurin bikin baje kolin fina-finai karo na 28 a Poland.

Wannan bikin baje kolin na fina-finai mafi girma da ake yi a kasar Poland domin tsamo fina-finan masu kima ta fuskar fasaha.

Labarin fim din na “Habibullah’ an gina shi ne akan wani mutum da ya manyanta, amma yake jajurcewa wajen

.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Rasha Ta Ce Babu Wani Abinda Zai Maye Gurbin  Yarjejeniyar JCPOA Ta Shirin Nukliyar Kasar Iran

Jakadan kasar Rasha na din din din a cibiyoyin MDD da suke Vienna, ya bayyana cewa dakatar da aiwatar da yarjeniyar shirin Nukliya na kasar Iran wanda ake kira JCPOA, wacce kuma aka samar da shi a shekara ta 2015, da kasashen yamma suka yi, shi ne ya haddasa dukkan matsalolin da suka biyo baya.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto, Mikhail Awliyonov yana fadar haka a hirar da ta hada shi da jaridar Ezustiyo na kasar Rasha.

Jakadan ya kara da cewa a tsakanin shekara ta 2021 da kuma 2022 an tattauna da kasashen yamma kan yadda za’a aiwatar da yarjeniyar JCPOA da kasashen bayan da kasar Amurka ta fice daga yarjeniyar a shekara ta 2018, amma sai kasashen yamma suka yi watsi da  ita sannan suka dorawa kasar Iran sabbin takunkuman tattalin arziki. Jakadan ya kuma kara da cewa a halin yanzu ba za’a warware wadannan matsalolin da suke tasowa kan shirin Nukliyar kasar Iran ba, sai an dawo kan yarjejeniyar ta JCPOA, sannan wadannan kasashen su mayarwa Iran hakkokinta da suka take a cikinta, wadanda suka kaita ga maida martanin da ta yi.

Ya ce, a halin yanzu shekaru ukku sun gabata da yin watsi da yarjeniyar, sannan har yanzun kasar Iran bada sabawa yarjeniyar ba, wanda ya kai ga yarjeniyar zata mutu a cikin watan Octoban shekara ta 2025 da muke ciki. Jakadan ya ce har yanzun ba’a da wani abu da zai maye gurbin yarjeniyar ta JCPOA. Wanda ke samun goyon bayan kudurin kwamitin tsaro na MDD mai lamba 2231.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • EU ta jadadda bukatar warware batun Iran ta hanyar diflomasiyya
  • Araghchi: Gwamnatin Amurka ta haramta wa Irakawa samun wutar lantarki
  • Iran ta soki matakin Amurka na hana shigar da wutar lantarki Iraki
  • Iran Tace:Tattaunawa Tare Da Barazana Ba Tattaunawa Ba Ce, Sai Dai Tursasawa
  • Iran Ta Ce Shirinta Na Makamashin Nukliya Na Zaman Lafiya Ne, Kuma Ba Zata Tattauna Da Amurka Karkashin Barazana Ba
  • Rasha Ta Ce Babu Wani Abinda Zai Maye Gurbin  Yarjejeniyar JCPOA Ta Shirin Nukliyar Kasar Iran
  • Pezeshkian: Duk wani rikici a gabas ta tsakiya babbar illa ce ga duniya baki daya
  • Iran, Rasha da China, sun fara wani atisayin sojojin ruwa a kusa da tashar ruwa ta Chabahar
  • Iran : Wadanda Suka Dage Kan Tattaunawa Da Iran, Na Yi Ne Don Amfanin Kansu_ Jagora