HausaTv:
2025-04-12@07:06:20 GMT

 Ukraniya Ta Hai Wa Birnin Moscow Hari Da Jirage Marasa Matuki

Published: 11th, March 2025 GMT

Tare da cewa Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuki fiye da 60 da Ukiraniya ta harba, sai dai an sanar da mutuwar mutum daya a birnin Moscow.

Kantoman yankin Moscow  Andrey Vorobyov ne ya sanar da cewa mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu 3 su ka jikkata, sanadiyyar hare-haren da Ukiraniya ta kai wa birnin da makamai masu linzami masu yawa da safiyar yau Talata.

Kantoman Mascow ya rubuta a shafinsa na “Telegram’ cewa; “ ya zuwa yanzu an sami labarin mutuwar mutum guda da kuma jikkata wasu 3 a garin Fidnoveh a kudancin Moscow.”

Sai dai daga baya wasu kafafen watsa labarun Rasha sun ambaci cewa adadin wadanda su ka jikkata din ya karu zuwa 5.

Haka nan kuma Andrey Vorobyov ya kara da cewa; Wasu gidaje  bakwai sun illata saboda faduwar jirgin maras matuku a kansu.

 A garin Domodedovo kuwa an sanar da tashin gobara sanadiyyar faduwar jirgi maras matuki da Ukiraniya ta harba, kuma wasu baraguzan jirgin da su ka fadi a kusa da tashar jirgin kasa ya yi barna sai dai ba mai girma ba. Tuni aka dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a yankin.

Kantoman birnin Moscow ya kuma sanar da cewa, sojoji sun yi nasarar kakkabo jiragen sama marasa mutuki 73 da ukiraniya ta harba wa birnin.

Saboda wadannan hare-haren an dakatar da tashi da saukar jiragen saman a cikin filayen sama fiye da uku da suke kusa da Moscow.

A ranar Lahadin da ta gabata ma dai sojojin Rasha sun sanar da kakkabo fiye da jirage marasa matuki 88 a saman yankunan kasar mabanbanta.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

USAID Za Ta Dawo Aiki A Wasu Ƙasashen Duniya – Gwamnatin Amurka

A cewar mai magana da yawun Ma’aikatar Cikin Gida ta Amurka, Tammy Bruce, akwai damuwa kan taimakon da ke iya faɗa wa hannun ƙungiyoyin Taliban da Houthi, waɗanda ke iko da mafi yawan yankunan waɗannan ƙasashe.

A baya-bayan nan, Hukumar Yaƙi da Yunwa ta Duniya (WFP) ta bayyana cewa katse tallafin Amurka tamkar “hukuncin kisa ne” ga miliyoyin mutane da ke fuskantar matsananciyar yunwa a faɗin duniya, musamman a yankunan da ake rikici.

Masu fashin baƙi na ganin wannan mataki na iya taimaka wa dubban mutane, amma kuma har yanzu ana buƙatar a duba inda taimakon ke zuwa don tabbatar da cewa yana taimaka wa mabuƙata ba tare da faɗa wa hannun ‘yan tada ƙayar baya ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • UBEC Ta Bayyana Jihar Jigawa A Matsayin Abin Kuyi A Fannin Ilimi
  •  Amurka Ta Kai Hare-hare A Yankunan Kasa Yemen
  •  Sojojin HKI Sun Yi Kisan Kiyashi A Yankin Shuja’iyya
  • USAID Za Ta Dawo Aiki A Wasu Ƙasashen Duniya – Gwamnatin Amurka
  • Amurka ta laftawa Iran sabbin takunkumai gabanin tattaunawar Oman
  • An Sace Dalibin Jami’ar Tarayya Birnin Kebbi
  • Sin Ta Kara Wasu Kamfanonin Amurka 12 Cikin Jerin Wadanda Ta Dakatar Da Fitar Musu Da Wasu Kayayyaki Daga Kasar Sin
  • Sojojin Kasar Yamen Sun Maida Martani Ga Hare-Haren Amurka Kan Amurkan Da Kuma HKI
  • Jiragen Yaki Da Sojojin Kasa Na HKI Sun Kashe Falasdinawa 38 A Yankin Gaza Daga Safiyar Yau Zuwa Yanzu
  • ’Yan bindiga sun kashe masunta 3 a Sakkwato