Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa
Published: 11th, March 2025 GMT
Gamayyar ƙungiyoyin manyan makarantu na gwamnatin Jihar Adamawa sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a yau Talata, 11 ga watan Maris.
Ma’aikatan manyan makarantun da suka haɗa da masu karantarwa da waɗanda ba sa karantarwa sun shiga yajin aiki ne bayan wa’adin yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da ya ƙare a jiya Litinin.
Cikin wata sanarwa da shugaba, Maryam Abdullahi da kuma sakataren ƙungiyoyin, Kwamared Musa Yakubu suka sanyawa hannu, sun alaƙanta yajin aikin a matsayin martani da halin ko-in-kula da gwamnatin jihar ta nuna kan buƙatunsu.
Dangane da hakan gamayyar ƙungiyoyin ke kiran dukkan mambobinta da su tsunduma yajin aikin na sai baba ta gani.
Aminiya ta ruwaito cewa, yajin aikin ya shafi manyan makarantu daban-daban ciki har da kwalejojin ilimi da fasaha da na lafiya da ke faɗin Jihar Adamawa.
Ƙungiyoyin dai na neman gwamnatin ta mayar da mambobinsu kan tsarin albashin manyan makarantu da kuma tsarin sabon albashi mafi ƙanƙanta da kuma janye tsarin zaftare albashinsu da ake yi da sunan haraji.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Adamawa manyan makarantu Yajin aiki manyan makarantu yajin aikin
এছাড়াও পড়ুন:
An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa
’Yan sanda sun cafke wasu mutum uku bisa zargin lalatawa da kuma satar wayoyin lantarki a ƙauyen Bororo da ke Ƙaramar Hukumar Michika ta Jihar Adamawa.
An cafke ababen zargin ne da wayoyin lantarkin yayin wani sintiri da jami’an ’yan sanda suka gudanar a ranar 9 ga wannan wata na Maris.
Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-Rufai ’Yan bindiga sun yi garkuwa da matashi a KanoMai magana da yawun rundunar ’yan sandan, Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce ababen zargin da ke hannu sun yi iƙirarin aikata laifin da ake zarginsu da shi.
Sai dai ya ce za a ci gaba da gudanar da bincike gabanin ɗaukar matakin da ya ce nan gaba kaɗan.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Dankombo Morris, ya yaba wa jami’an da suka yi ruwa da tsaki wajen cafke ababen zargin, yana mai jaddada aniyar ƙara ƙaimi wajen tsare dukiyoyin al’umma.
Rundunar ’yan sandan ta buƙaci mazauna da su ci gaba da ba ta haɗin kai wajen lura da duk wani motsi tare da kai rahoto duk wani abin zargi zuwa mahukunta mafi kusa.