Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da ‘Atisayen sojojin ruwa mai taken (“damarar tsaro na shekara ta 2025”) wandake ke gudana a nan Iran. Wanda ni tahir amin zan karanta.

////.. A ranar litinin da ta gabata ce sojojin ruwa na kasashen China, Rasha da kuma Iran suka fara atisayen sojojin ruwa na hadin giwan kasashen uku, wanda suka sanya masa suna :damarar tsaro na shekara ta 2025″ wanda kuma ke gudana a halin yanzu a arewacin tekun Indiya da ke kudu maso gabacin kasar Iran da tekun farisa da kuma tekun Omman.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa atisayen wanda zai dauki kwanaki uku cur ana gudanar da shi, zai maida hankali wajen al-amuran da suka shafi tsaron ruwa na yankuna daban-daban a inda wadanda kasashe suke kula da su.

Labarin ya kara da cewa a yau talata sojojin kasashen uku sun gudanar da wani bangare na atisayen. Rear admiral Mostafa Tajeddine mataimakin kwamandan gudanarwa na sojojin Ruwa na kasar Iran ne ya bayyana haka. Ya kuma kara da cewa wannan bangaren daukar hotuna na atisayen ya kammala kamar yadda aka tsara.

Tajuddine ya kara da cewa ana daukar hotunan yadda atisayen ke gudana daga jirgin ruwa wanda yake kula da hakan daga cikin jiragen ruwan yaki sojojin ruwa na rundunar IRGC. Ya kuma ce JMI tana da shirin kula da zaman lafiya a yankunan ruwa daban –daban a kasashe yankin da kuma na sauran kasashen duniya.

Shi ma a jawabinsa Rear admiral Shahram Irani, babban kwamandan sojojin Ruwa na JMI ya bayyana cewa, yayi watsi da zancen shugaban kasar Amurka Donal Trump dangane da wannan atisayen na cewa, Amurka tafi taron kasashen Iran Rasha da kuma China, ya kuma bayyana cewa wannan kalaman ‘rudu ne’ kawai wanda shugaban ya shiga.

Kafin haka dai shugaban  kasar na Amurka yace bai damu da atisayen kasashen uku suka yi a tekun faraisa, don ya san Amurka ta fi su karfi gaba daya. Irani ya ce manufar kasashen uku a wannan atisayen, mai suna ‘damarar tsaro na shekara ta 2025″ ita ce tabbatar da tsaro a yankin da kuma duniya, sabanin abinda Amurka take yi na samar da tashe-tashen hankula a cikinta.

Ya kuma kara da cewa, yakama ta gwamnatin Amurka ta sani, yawan kasashen da suke da karfin sojojin ruwa a duniya sun kara, kuma suna gwada karfinsu a wurare da dama a yankin Asiya da kuma wasu wurare a duniya. Ya ce kasashen kungiyar Shanghai da Brics da dama suna da karfin tabbatar da zaman lafiya a yankuna da dama a duniya. Suna da karfin ganin harkokin tattalin arziki na yankunansu da kuma kasashensu suna gudana da kyau.

Ya ce wasu kasashe banda wadannan uku, suna shirye-shiryen hadewa da wannan atisayen nan gaba. Wannan dai shi ne atisay karo na 7th wadanda wadannan kasashe uku China Iran da kuma Rasha, wanda yake karfafa kwarewarsu a tabbatar da tsaro a cikin ruwayen kasashen yankin, har’ila yau akwai wasu kasashe da dama daga yankin da kuma wasu kasashe daga nesa suna a matsayin masu kallo a wannan atisayen.

Banda haka wadannan atisayen zai hana kan wadannan kasashe don cimma manufa guda ta samar da zaman lafiya a dukkan hanyoyin zirga zirgan kasuwanci da hulda ta cikin ruwa a yankin da kuma duniya.

A cikin yan kwanakin nan ne shugaban kasar Amurka take barazanar kaiwa cibiyoyin nukliya na kasar Iran, don hanata, abinda ya kira makamin Nkliya. Ko kuma iran ta amince ta zauna da Amurka ita kadai don ta fada mata abinda zata yi, da abinda ba zatayi ba a fagen makamashin nukliya. Wanda Iran tace ba zata taba zama da Amurka don tattauna batun shirinta na makamashin nukliya ba.

Tun kafin ya sake dawowa kan kujerar shugabancin kasar Amurka, a karo na biyu, shugaban yake barzanar zai tursaswa iran ta amince don tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya.

Amma idan ta ki amincewa zai yi amfani da karfin don wargaza shirinta na makamshin nukliya don ba zata amince iran ta mallaka makaman Nukliya ba.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: a wannan atisayen sojojin ruwa na yankin da kuma kara da cewa

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Tace:Tattaunawa Tare Da Barazana Ba Tattaunawa Ba Ce, Sai Dai Tursasawa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa tattaunawa tare da barazana ba tattaunawa ake kiransa ba, sai dai tursasawa.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmael Baghaie  ya na fadar haka a yau litinin a jawabin mako-makon da ya saba gabatarwa a ko wace ranar litinin.

Baghaei ya kara da cewa JMI ba zata taba tattaunawa da Amurka tare da barazana da kuma takurawa kasar da takunkuman tattalin arziki ba.  Zabin tattaunawa ko kuma yaki, ba  tattaunawa sai dai tursasawa.

Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa JMI ba ta da zabi, ko ta shiga tattaunawa da Ita Amurka ko kuma ta shiyawa yaki. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ya kara da cewa takunkuman tattalin arziki mafi muni wanda Amurka ta dorawa kasar tun shekara ta 2018, sun yi illa da kuma tasiri kan rayuwar mutanen kasar Iran, amma wannan bai sa ta mika kai ga bukatun Amurka ba.  Ya kuma kara da cewa ko yakin ma, ba zai tilsatawa kasar Iran mika kai ga bukatunta ba.

Abinda Trump yake kira tattaunawa shi ne wakilan kasar Iran su zauna kan wani teburi, sannan Amurka ta ce, ga abinda zaki yi, ga abinda zaki bari, idan kunki yin haka, to ga makamai.

Ya ce, tattaunawa kam, Iran ta yi hakan a yarjeniyar JCPOA kuma an dauki shekaru biyu cur ina tattaunawa tsakanin kasashe 5 +1 da Iran, daga ciki har da ita Amurka.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Ghana ya bukaci Ecowas ta amince da kungiyar kasashen sahel da suka balle  
  • Iran Tace:Tattaunawa Tare Da Barazana Ba Tattaunawa Ba Ce, Sai Dai Tursasawa
  • Sojojin Ruwa Na Kasashen Rasha Da China Sun Shigo Kasar Iran Don Fara Atisayen Sojojin Ruwa Mai Suna “Damarar Tsaro 2025”
  • Rasha Ta Ce Babu Wani Abinda Zai Maye Gurbin  Yarjejeniyar JCPOA Ta Shirin Nukliyar Kasar Iran
  • Gwamnatin Kano Ta Bullo Da Sabbin Hanyoyin Kare Makarantunta Daga Kalubalen Tsaro
  • Shugaban Ghana ya ziyarci kasashen Sahel da suka balle daga Ecowas
  • Isra’ila ta katse wutar lantarki a zirin Gaza
  • Sharhin Bayan Labarai: Kasashen Afirka Sun Kori Sojojin Faransa Daga Kasashensu
  • A Gobe Litinin Za A Yi Atisayen Sojan Ruwa Na Hadin Gwiwa Tsakanin Kasashen Iran, Rasha Da China