Leadership News Hausa:
2025-03-12@12:04:26 GMT

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [4]

Published: 12th, March 2025 GMT

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [4]

Wannan umurni yana da tushen shari’a daga Alƙur’ani da Hadisi, kuma yana da hikima da fa’ida da dama. Allah Ta’ala Ya umurci Musulumi da yin isti’aza kafin karanta Alƙur’ani kamar yadda Ya labarta mana haka a cikin Suratul Nahli a aya ta 98. Inda Ya ce:” To idan za ka karanta Alƙur’ani sai ka nemi tsarin Allah daga Shaiɗan korarre (daga rahamar Allah).

” Wannan aya ta tabbatar da neman tsarin Allah kafin a fara karatun Alƙur’ani.

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [1] CIYARWA [Falalarta Da Muhimmancinta] Na 1

Ma’anar Isti’aza:

Isti’aza na nufin neman tsari da kariya da fake wa a wurin Allah Shi kaɗai ban da waninsa daga sharrin Shaiɗan. Domin ƙarin haske duba Ibnu Jarir; Jãmi’ul Bayãni [1/111], Ibnu Kasir; Tafsirul Kur’anil Azim [1/27], da Ibnul Ƙayyim; Badã’i’ul Fawã’id [2/200].

Yaushe ake Isti‘aza?:
Malamai sun yi saɓani dangane da lokacinda za a yi Isti‘aza, sai dai magana mafi ingani da malamai mafiya yawa suke a kanta shi ne ana yin Isti‘aza ne kafin a fara karatu. Domin ƙarin haske duba Ibnu Ibnu Juzai; Kitãbut Tashīl fi Ulūmil Kitãbi [1/30], da Bagawī; Ma’ãlumut Tanzīli [[5/42] da Ibnu Aɗiyya; al-Muharrul Wajizi [1/58], da Ibnul Jauzi; Zãdul Masīri [1/14].

Hukunci Isti‘aza Kafin Karanta Alƙur’ani:

Malamai mafiya yawa sun tafi a kan mustahabbi ne yin isti‘aza a lokacin karanta Alƙur’ani a wajen salla. Amma sun yi saɓani a wajen karatun salla, an hakaitu Imamu Malik ba ya isti‘aza a sallar farilla amma yana yi a sallar asham, shi sa ake yi a sallar nafila. Amma Imam Abu Hanifa da Imam Asshafi’i suna yi isti‘aza a sallar farilla. Akwai waɗanda suke ganin wajibi ne a yi isti‘aza a salla gaba ɗaya. Domin ƙarin haske duba Kitãbu at-Tashīlu fi Ulūmi at-Tanzil [1/30] da Ibnu Kasir; Tafsirul Kur’anil Azim [1/26] da al-Ƙurɗubi; al-Jãmi’u Li’ahkãmil Ƙur’ãni [1/86]

Hikimar Yin Isti’aza Kafin Karanta Alƙur’ani:

Akwai hikimomi masu tarin yaw na yin isti‘aza kafin karatu. Ga wasu daga cikinsu:

1. Kariya daga tasirin Shaiɗan: Shaiɗan yana hana mutum fahimtar Alƙur’ani kuma yana kuma sanya ruɗani. Yin isti’aza na kare mai karatu daga fitinarsa.

2. Tsaftace zuciya: Isti’aza kafin karanta karanta Alƙur’ani yana ba wa zuciya tsarki da nufin Allah a karatu da samin tsoron Allah, tare da tadabburi.

3. Bin sunnon Annabi (SAW): Domin Annabi (SAW) yana Isti’aza kafin ya fara karatu.

4. Tsaftace Baki: Yin isti‘aza yana tsaftace baki daga abuwan da ta aikata na wargi da yasasshen zance, domin shiga karanta maganar Allah cikin tsarki da tsafta.

Daga: Abu Razina, Nuhu Ubale Paki

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Abu Razina Nuhu Ubale Paki Ramadan isti aza kafin karanta Isti aza kafin karanta karanta Alƙur ani

এছাড়াও পড়ুন:

MDD, ta la’anci Isra’ila kan katse wutar lantarki a Gaza

Majalisar Dinkin Duniya, ta yi tir da matakin Isra’ila na kate wutar lantarki a Gaza, tana mai matukar gargadi game da ilan da hakan zai janyo wa Zirin.

Matakin da Isra’ila ta dauka na katse wutar lantarki a zirin Gaza da aka yi wa kawanya zai hana yankin Falasdinawa samun “ruwa mai tsafta,” in ji wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan yankunan Falasdinawa da aka mamaye.

Francesca Albanese ta fada a ranar Litinin cewa shawarar da Isra’ila ta dauka na yanke wuta a Gaza na nufin tsaida hanyoyin samar da ruwa a zirin.

Albanese ta kuma yi Allah wadai da rashin daukar mataki kan hakan daga kasashen duniya.

A ranar Lahadin da ta gabata ne, kafofin yada labaran Isra’ila suka mabato cewa ministan makamashi da ababen more rayuwa na gwamnatin Isra’ila Eli Cohen ya umarci Kamfanin Lantarki na Isra’ila da ya katse wutar lantarki zuwa Gaza “nan take.”

Isra’ila ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a Gaza tun a ranar 7 ga Oktoba, 2023 bayan harin ba zata na kungiyar Hamas, kuma tun lokacin ta kashe Falasdinawa sama da 48,400, baya ga lalata duk wasu cibiyoyi masu mahimmanci na Zirin kama daga asibitoci, sansanonin ‘yan gudun hijira, makarantu gidajen jama’a da dai saurensu tare da goyan bayan Amurka, lamarin da gwamnatocin kasashen duniya dama suka danganta da yunkurin share wata al’umma daga doron kasa.

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, ta fitar a bara da sammacin kame firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, da tsohon ministan tsaron kasar Yoav Galant, bisa zarginsu da aikata laifukan yaki a Gaza.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Matashin da ke kera jiragen sama da bindigogi daga robobi
  • MDD, ta la’anci Isra’ila kan katse wutar lantarki a Gaza
  • El-Rufa’i ya fice daga APC ya koma SDP
  • Tsohon Gwamnan Kaduna El-Rufai Ya Koma SDP
  • Alummomin duniya na ci gaba da yin Allah wadai da kisan fararen hula a Siriya
  • Sharhin Bayan Labarai: Kasashen Afirka Sun Kori Sojojin Faransa Daga Kasashensu
  • Ramadan: Ali JC ya bai wa jama’a tallafin kayan abinci a Gombe