DAGA LARABA: Ko Kun San Asalin Tashe Da Tarihinsa A Ƙasar Hausa?
Published: 12th, March 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Bayan ɗimbin falala da yawan samuwar ibadun da ke ƙara kusanta bayi ga Ubangijinsu, da azumin watan Ramadan ke zuwa da shi kamar yadda malamai suka saba faɗa, Hakazalika kuma a watan na zuwa da wata al’ada mai ɗimbin tarihi da ke ɗebe wa al’umma musamman na Arewacin Najeriya kewa.
Wannan al’adar ita ce ta tashe da ake fara d zarar watan azumi ya kai kwanaki 10.
DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin AlbashiMaza da mata na gudanar da wannan al’ada ta hanyar yin shigar kwaikwayo tare da ɓatar da kama, su ringa zagayawa gidaje da kwararo-kwararo ɗauke da ganga da kayan kaɗe-kaɗe suna bugawa suna waƙa.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan wannan daɗaɗɗiyar al’adar, don jin inda ta samo asali, tarihinta da kuma yadda ake gudanar da ita.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Yadda Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Zai Shafi Rayuwar ’Yan Najeriya
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A Najeriya ana tafka muhawara a kan yadda farashin ɗanyen man fetur yake ƙara faduwa a kasuwannin duniya.
Wannan lamari dai ya haddasa damuwa a zukatan wasu ’yan ƙasar, kama daga masana tattalin arziki zuwa jami’an gwamnati, kasancewar ɗanyen mai ne mafi muhimmanci a cikin hanyoyin samun kuɗaɗen shigar ƙasar.
Sai dai tambayar da wasu ’yan kasar suke yi ita ce: shin yaya wannan faɗuwar ta farashin ɗanyen mai za ta shafi rayuwar talaka?
NAJERIYA A YAU: Tasirin ’Yan Uwantaka Ga Rayuwar Al’umma DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne kan yadda faɗuwar farashin ɗanyen man fetur zai shafi ɗan Najeriya.
Domin sauke shirin, latsa nan: https://www.buzzsprout.com/1822045/episodes/16955648-yadda-fa-uwar-farashin-anyen-mai-zai-shafi-rayuwar-yan-najeriya.mp3?download=true