Aminiya:
2025-03-12@12:11:37 GMT

DAGA LARABA: Asalin Tashe Da Tarihinsa A Ƙasar Hausa?

Published: 12th, March 2025 GMT

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Bayan ɗimbin falala da yawan samuwar ibadun da ke ƙara kusanta bayi ga Ubangijinsu, da azumin watan Ramadan ke zuwa da shi kamar yadda malamai suka saba faɗa, Hakazalika kuma a watan na zuwa da wata al’ada mai ɗimbin tarihi da ke ɗebe wa al’umma musamman na Arewacin Najeriya kewa.

Wannan al’adar ita ce ta tashe da ake fara d zarar watan azumi ya kai kwanaki 10.

DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi

Maza da mata na gudanar da wannan al’ada ta hanyar yin shigar kwaikwayo tare da ɓatar da kama, su ringa zagayawa gidaje da kwararo-kwararo ɗauke da ganga da kayan kaɗe-kaɗe suna bugawa suna waƙa.

Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan wannan daɗaɗɗiyar al’adar, don jin inda ta samo asali, tarihinta da kuma yadda ake gudanar da ita.

Domin sauke shirin, latsa nan

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Hausawa Ramadan

এছাড়াও পড়ুন:

Sheikh Qassem: Duk da wahalhalun, Hizbullah tana da karfinta

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya bayyana cewa, gwagwarmayar al’ummar kasar Lebanon na nan da karfinta, duk da asarorin da ta yi da kuma sadaukarwa.

A wata hira da yayi da tashar talabijin ta Al Manar, Sheikh Qassem ya bayyana cewa, ‘yan gwagwarmaya a kasar Lebanon sun yi nasarar cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta kawo karshen hare-haren da Isra’ila a lokacin da suke kara jajircewa.

Ya jaddada cewa “a koyaushe ana ci gaba da tuntubar juna tsakaninsu da shugaban majalisar Nabih Berri, kuma ba mu yi wata tattaunawa a cikin rauni ba.”

Sheikh Qassem ya tabbatar da cewa, muddin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta ci gaba da mamayar yankunan Lebanon, to dole ne a tunkare ta ta hanyar gwagwarmaya da ayyukan soji.

Shugaban na Hizbullah ya yi nuni da cewa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma tsakanin Isra’ila da Lebanon a fili take, babu wata boyayyiyar yarjejeniya da aka kulla, komai a bayyane yake.

Ya yi nuni da cewa, yarjejeniyar ta yi magana karara a kan “kudancin kogin Litani” sau biyar, yana mai cewa, “Wannan shi ne tsarin da ya kamata mu bi.”

“Wannan yarjejeniya wani bangare ne na kuduri mai lamba 1701 na Majalisar Dinkin Duniya na dakatar da ta’addancin Isra’ila,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • DAGA LARABA: Ko Kun San Asalin Tashe Da Tarihinsa A Ƙasar Hausa?
  • Kamfanin Kasar Sin Zai Gudanar Da Aikin Farfado Da Muhallin Halittu Na Kogin Nairobi Na Kasar Kenya
  • Tsohon shugaban Philippines ya faɗa komar ’yan sanda
  • An hana tashe bana a Kano — Nalako
  • NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya
  • Sheikh Qassem: Duk da wahalhalun, Hizbullah tana da karfinta
  • NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin Azumi
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [2]
  • Sharhin Bayan Labarai: Kasashen Afirka Sun Kori Sojojin Faransa Daga Kasashensu