HausaTv:
2025-03-12@12:08:02 GMT

EU ta jadadda bukatar warware batun Iran ta hanyar diflomasiyya

Published: 12th, March 2025 GMT

Kungiyar tarayyar turai ta jaddada bukatar warware batun Iran ta hanyar diflomatsiyya.

Da taek sanar da hakan babbar Jami’ar kula da harkokin ketare ta kungiyar ta ce babu wata hanyar da za’a bi wajen warware matsalar Iran in ba ta diflomasiyya ba.

‘’ta hanyar diflomatsiyya ne za’a warware takaddamar da ake game da batun yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015 da iran, inji Kaja Kalas.

Da take magana a taron shekara-shekara na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan hadin gwiwa tsakanin EU da Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, babbar jami’ar ta Tarayyar Turai ta ce “ci gaba da fadada shirin nukiliyar Iran ya sabawa alkawurran da Iran ta dauka kamar yadda kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da shi.

“A lokaci guda kuma, hanyar da ta shafi bangarori daban-daban, kamar yarjejeniyar, tana da mahimmanci.

Ta ce, “Babu wata hanyar da za ta dore wajen warware matsalar sai ta diflomasiyya,” in ji ta, a cewar shafin yanar gizon EU External Action.

A kwanan ne dai shugaban AMurka Donald Trump, y ace ya aike da wasiga ga Iran, na ta bude tattaunwa ko kuma ya yi da karfin soji.

Iran dai ta musanya samun wata wasika daga Trump, kuma tana mai cewa babu batun tattaunawa bsia matsin lamba da barazana.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas

Rahotanni sun bayyana cewa Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta hana Gwamna Similanayi Fubara shiga cikinta a safiyar wannan Larabar.

Bayanai sun ce gwamnan ya ziyarci majalisar ne domin gabatar mata da Kasafin Kuɗin jihar na 2025.

Sai dai bayan isowar gwamnan tare da tawagarsa, ya tarar da ƙofar shiga majalisar a garƙame da kwaɗo kuma an ƙi buɗewa da ke tabbatar da alamar ba a maraba da shi.

Babu wani ƙwaƙwaran dalili da aka bayar, sai dai wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa an rufe wa gwamnan ƙofa ne saboda bai sanar da majalisar a hukumance cewa zai zo gabatar da Kasafin Kuɗin jihar ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas
  • Pezeshkian: Babu Batun Tattaunawa Da Amurka A Karkashin Matsin Lamba
  • Natasha ta yi ƙarar Akpabio a Majalisar Dinkin Duniya
  • Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Karfafawa Duniya Gwiwa Ta Hanyar Fadada Bude Kofar Ta
  • Iran Ta Ce Shirinta Na Makamashin Nukliya Na Zaman Lafiya Ne, Kuma Ba Zata Tattauna Da Amurka Karkashin Barazana Ba
  • Pezeshkian: Duk wani rikici a gabas ta tsakiya babbar illa ce ga duniya baki daya
  • Alummomin duniya na ci gaba da yin Allah wadai da kisan fararen hula a Siriya
  • New York Times: Isra’ila ce ta kashe wasu fursunoninta da ake tsare da su a Gaza
  • Tawagar Majalisar Dinkin Duniya na rangadi a wuraren da aka aikata kisan kiyashi a Syria