HausaTv:
2025-03-12@12:38:35 GMT

Ukraine ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 30

Published: 12th, March 2025 GMT

Kasar Ukraine ta bayyana aniyarta ta amincewa da shawarar da Amurka ta gabatar, game da dakatar da bude wuta nan take tsakaninta da Rasha har tsawon kwanaki 30, biyowa bayan fara tattaunawa da tawagar Amurka a birnin Jeddah na kasar Saudiyya.

Wata sanarwar hadin gwiwa tsakanin wakilan Ukraine da na Amurka da aka fitar a jiya Talata ce ta tabbatar da hakan, bayan sassan biyu sun shafe sa’o’i suna tattaunawa.

Sanarwar ta ce akwai yiwuwar tsawaita yarjejeniyar, kuma Amurka za ta tuntubi Rasha kasancewar amincewarta zai tabbatar da cimma nasarar matakin.

Baya ga hakan, Amurka ta amince da dage matakin dakatar da musayar bayanan sirri, kuma za ta ci gaba da baiwa Ukraine tallafin tsaro, yayin da kuma sassan biyu suka tattauna kan muhimmancin aiwatar da matakan samar da tallafin jin kai, musamman a wa’adin tsagaita bude wutar.

Har ila yau, masu shiga tsakanin sun amince da samar da tawagogin da za su fara tattaunawa, da nufin cimma nasarar wanzar da zaman lafiya mai dorewa.

 A daya hannun kuma, Amurka ta jaddada aniyarta ta hawa teburin shawara da Rasha, yayin da Ukraine ta jaddada muhimmancin shigar sauran abokan hulda na Turai cikin tsarin na cimma daidaito.

Bugu da kari, jagororin Ukraine da na Amurka, sun amince da gaggauta kaiwa karshen cikakkiyar yarjejeniyar bunkasa cin gajiya daga muhimman ma’adanan Ukraine, ta yadda za a kai ga fadada tattalin arzikin kasar. 

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Isra’ila ta aike da tawaga zuwa Doha domin ci gaba da tattaunawar sulhun Gaza

Gwamnatin Isra’ila ta tura wa tawaga zuwa kasar Qatar a daidai lokacin da ake takun saka tsakanin Isra’ilar da masu shiga tsakani ciki har da Amurka.

Wannan ya biyo bayan tattaunawar kai tsaye da ba a taba yin irinta ba tsakanin Hamas da wakilin Amurka Adam Boehler dake kula da mutanen da akayi garkuwa da su.

Wakilin na Amurka ya sha bayyanawa a baya baya nan cewa Ya yi imanin cewa za a iya cimma yarjejeniya a makonni masu zuwa.

Ya kuma ce Hamas ta shirya tsagaita bude wuta na tsawon shekaru biyar zuwa goma sannan kuma kungiyar ta kwance damara.

Tunda farko dai kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, “suna kira ga masu shiga tsakani a Masar da Qatar, da kuma gwamnatin Amurka, da su tabbatar da cewa ‘yan mamaya sun mutunta yarjejeniyar, da ba da damar shigar da kayayyakin jin kai, da kuma ci gaba da tafiya mataki na biyu na tsagaita.

A nata bangaren dai Isra’ila na son tsawaita wa’adin zangon farko na tsagaita bude wuta har zuwa tsakiyar watan Afrilu, kuma ta bukaci ficewar Hamas daga yankin Falasdinu da ta ke mulki tun shekara ta 2007, da kuma dawo da ragowar mutanen da taka garkuwa da su.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ukraine ta amince da ƙudurin tsagaita wuta a fafatawarta da Rasha
  • Ukraine ta amince da kudurin tsagaita wuta a fafatawarta da Rasha
  • Fiye da Falasdinawa 130 ne Isra’ila ta kashe tun bayan da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta
  • Zelensky Ya Ziyarci Saudiyya Don Kawo Ƙarshen Rikicin Ukraine Da Rasha
  • Zelensky ya je Saudiyya domin tattaunawar zaman lafiya
  • Iran Tace:Tattaunawa Tare Da Barazana Ba Tattaunawa Ba Ce, Sai Dai Tursasawa
  • Rasha Ta Ce Babu Wani Abinda Zai Maye Gurbin  Yarjejeniyar JCPOA Ta Shirin Nukliyar Kasar Iran
  • Isra’ila ta aike da tawaga zuwa Doha domin ci gaba da tattaunawar sulhun Gaza
  • Masana A Iran Sun Samar Da Maganin Rashin Haihuwa Na Maza