Natasha ta yi ƙarar Akpabio a Majalisar Dinkin Duniya
Published: 12th, March 2025 GMT
Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya da aka dakatar, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi ƙarar Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio a Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ta gabatar da kokenta a zaman taron mata da aka gudanar a hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) a birnin New York, inda ta nemi ƙungiyoyin kare dimokuraɗiyya na duniya su bi mata haƙƙinta.
Natasha, ta ce dakatar da ita daga Majalisar Dattawan Nijeriya da aka yi ba bisa ƙa’ida ba ne, kuma ta nuna damuwa kan cewa za a iya ƙoƙarin tsare ta saboda yin magana a fili.
Taƙaddamar da ke tsakanin Sanata Natasha da Sanata Akpabio ta ƙara tsanani bayan rigimar sauya mata wajen zama a zauren majalisa da ta faru a ranar 20 ga watan Fabrairu, 2025.
Ta zargi Akpabio da cin zarafinta da kuma amfani da muƙaminsa ta hanyar da ba ta dace ba, zarge-zargen da duk ya musanta.
Bayan lamarin ya yi ƙamari, Natasha ta maka Akpabio a kotu kan zargin ɓatanci, tana neman diyyar Naira biliyan 100.
A makon da ya gabata ne dai Majalisar Dattawan ta sanar da dakatar da Sanata Natasha Uduaghan tsawon watanni shida bayan kwamitin ladabtarwa na majalisar ya zarge ta da karya wasu daga cikin dokokinta.
Kwamitin ya yi zargin cewa Sanata Natasha ta yi magana ba tare da izini ba, kuma ta ƙi komawa sabon wurin zaman da aka sauya mata a zauren majalisar.
Har ila yau, an dakatar da albashinta da sauran haƙƙoƙinta na kuɗaɗe har tsawon lokacin dakatarwar, kuma an hana ta gabatar da kanta a matsayin Sanata.
Dambarwar Natasha da Akpabio na ci gaba da ɗaukar hankali a ciki da wajen Najeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: dakatarwa Ƙara Majalisar Dattawa Majalisar Ɗinkin Duniya a Majalisar
এছাড়াও পড়ুন:
HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas
Rahotanni sun bayyana cewa Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta hana Gwamna Similanayi Fubara shiga cikinta a safiyar wannan Larabar.
Bayanai sun ce gwamnan ya ziyarci majalisar ne domin gabatar mata da Kasafin Kuɗin jihar na 2025.
Sai dai bayan isowar gwamnan tare da tawagarsa, ya tarar da ƙofar shiga majalisar a garƙame da kwaɗo kuma an ƙi buɗewa da ke tabbatar da alamar ba a maraba da shi.
Babu wani ƙwaƙwaran dalili da aka bayar, sai dai wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa an rufe wa gwamnan ƙofa ne saboda bai sanar da majalisar a hukumance cewa zai zo gabatar da Kasafin Kuɗin jihar ba.