Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mai juna biyu da wasu mutum 10 a Nasarawa
Published: 12th, March 2025 GMT
Wasu ’yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai hari garin Farin Duse da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa, inda suka kashe wata mata juna, Azumi Allah Gaba, tare da wasu mutum 10.
Binciken Aminiya ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne lokacin da wani makiyayi ke kiwon shanunsa, ya yanke wata bishiyar mangwaro domin ciyar da dabbobinsa.
Wani mazaunin yankin ya yi ƙoƙarin hana shi, lamarin da ya haifar da cacar baki a tsakaninsu.
Makiyayin ya harbe mutumin nan take, wanda hakan ya haddasa mummunan rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoman Gwari.
Wani ganau da ya buƙaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa: “Rikicin ya fara ne da misalin ƙarfe 6 na safe a ranar Lahadi, 9 ga watan Maris, 2025, har zuwa yammacin Talata.
“Jami’an tsaro sun tabbatar da zaman lafiya, amma har yanzu garin Gwari babu kowa, kuma ana jin harbe-harbe a Farin Ruwa Duse.”
An ƙone gidaje sama da 20 tare da lalata wani ofishin ’yan sanda da ke yankin.
Wasu bayanai sun nuna cewar an lakaɗa wa DPO duka, sannan aka lalata babur ɗinsa.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa, ta tabbatar da mutuwar Azumi Allah Gaba da jaririnta da ke cikinta, tare da wasu mutane.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Nansel Rahman, ya fitar, ya bayyana cewa an kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a rikicin.
Ya tabbatarwa da jama’a cewa jami’an tsaro sun shawo kan lamarin, kuma ana ci gaba da bincike don kama waɗanda suka aikata laifin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Makiyaya Nasarawa
এছাড়াও পড়ুন:
Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Kano, Sun Sace Mutum Ɗaya
Wasu ‘yan bindiga sun farmaki gidan Alhaji Yusha’u Ma’aruf, mamallakin wani asibiti mai zaman kansa, a garin Zakirai da ke ƙaramar hukumar Gabasawa a jihar Kano, inda suka sace wani matashi mai shekaru 20 tare da jikkata ɗan uwansa.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan uku ɗauke da bindigogi da adduna sun afka wa gidan da misalin ƙarfe 2:15 na dare, suka sare yatsan hannun Abubakar Yusha’u mai shekaru 23 sannan suka sace ɗan uwansa, Mohammed Bello Yusha’u.
Daily Trust ta ruwaito cewa, sun kwashe wayoyi da kuɗaɗe kafin su tsere.
Tinubu Ya Buƙaci A Mayar Wa BUK Filin Rimin Zakara Da Ake Taƙaddama A Kai Ɗan Uwan Gwamnan Kano Da Malaman NNPP Sun Koma APCKakakin rundunar ‘yansandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an tsaro sun fara bincike don ceto wanda aka sace da kuma kamo waɗanda suka aikata harin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp