Duk da raguwar hare-haren da kashi 2.19 idan aka kwatanta da Janairu, har yanzu matsalar tsaro na ci gaba da zama barazana ga al’umma a Nijeriya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Hare Hare Rahoto

এছাড়াও পড়ুন:

Tarkon Mutuwa a Katsina: Hanyar Funtua zuwa Ƙanƙara

Al’ummomin Jihar Kastina sun shiga sabon tashin hankali bayan da ’yan bindiga suka kai wasu munanan hare-hare a wasu yankuna biyu a Jihar Katsina a ƙarshen makon jiya, inda suka kashe mutane shida tare da yin garkuwa da wasu 59.

A daren Lahadi, kusan ƙarfe 10:30, ’yan bindiga ɗauke da makamai suka kai farmaki ƙauyen Layin Gara a Ƙaramar Hukumar Funtua, inda suka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu 16. Shaidu sun ce maharan sun ɗauki sa’o’i da dama suna cin karensu babu babbaka, ba tare da wani ƙalubale daga jami’an tsaro ba.

Kwana ɗaya kacal kafin hakan, a ranar Asabar, ’yan bindiga ɗauke da manyan makamai a bisa babura sun mamaye ƙauyen Maikuma, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin garkuwa da wasu kimanin 43.

Waɗanda suka tsira sun ce maharan sun kwashe sa’o’i suna shiga gida-gida suna ɗaukar mutane kafin daga bisani su yi awon gaba da su zuwa cikin daji.

Yadda masu safarar ɗan Adam ke yaudarar mutane ta intanet Bai wa ’yan bindiga kuɗin fansa na dagula sha’anin tsaro — Ribadu NAJERIYA A YAU: Tasirin ’Yan Uwantaka Ga Rayuwar Al’umma Tarkon mutuwa

Hare-haren na daga cikin ayyukan ta’addanci da suka addabi al’ummomin da ke kan hanyar Funtua zuwa Ƙanƙara a Jihar Katsina a baya-bayan nan. Wannan lamari ya sa mazauna sun bayyana hanyar a matsayin tarkon mutuwa saboda yawan hare-haren ’yan bindiga.

Tsakanin watan Yunin 2024 zuwa Afrilun 2025, an samu rahotannin kashe-kashe da yin garkuwa da jama’a da dama a kan wannan babbar hanyar.

Wannan matsala tana ci wa wannan yanki tuwo a ƙwarya ne a daidai lokacin da wasu ƙananan hukumomin da a baya suka fi fama da hare-haren ’yan bindiga suka samu raguwar hare-hare, bayan yarjejeniyoyin zaman lafiya da suka ƙulla da wasu manyan ’yan bindiga.

Sai dai a gefe guda kuma al’ummomin da ke tsakanin hanyar Funtua zuwa Ƙanƙara suna ci gaba da zama wurin da ’yan bindiga suka fi zama.

Ƙanƙara na da wani babban daji da ta yi iyaka da Jihar Zamfara, yayin da Funtua, har zuwa Faskari, ke iyaka da Jihar Kaduna. Tun da daɗewa, al’ummomin da ke gefen dazuzzuka a yammacin Ƙanƙara sun zama maɓoyar ’yan bindiga waɗanda suke kai-komonsu ba tare da wata turjiya mai yawa ba.

A Ƙaramar Hukumar Kankara ne aka yi garkuwa da ɗalibai sama da 200 a watan Disambar 2020 — lamarin da ya jawo fushin duniya da kuma Allah wadai.

Hare-haren baya-bayan nan

A watan Yunin 2024, ’yan bindiga ɗauke da makamai sun kashe mutane 26, ciki har da ’yan sanda hudu, a wani hari da suka kai kauyen Gidan Boka a Ƙaramar Hukumar Kankara.

A cewar ’yan sanda, maharan sun mamaye ƙauyen, inda suka kashe mutane 15 tare da raunata wasu biyu.

Wata tawagar ’yan sanda da ke sintiri a cikin motar sulke ta faɗa cikin kwanton ɓaunar ’yan bindiga a kusa da ƙauyen Kurmeji bayan da farko ta yi makuwa,

Kwanton ɓaunar ya kai ga musayar wuta, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar jami’ai hudu da kuma wasu mambobi biyu na kungiyar sa kai ta Jihar Katsina.

Yayin da suke tserewa ta ƙauyen Ɗan Nakwabo, ’yan bindigar sun kuma kashe wasu mutane biyar, wanda ya kawo adadin mamatan zuwa 26.

A watan Janairun 2025, ’yan bindiga sun kai hari kan Babban Asibitin da ke Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara, inda suka harbi wani likita tare da sace ma’aikata biyar, ciki har da wani ma’aikacin jinya mai suna Yusuf Mohammed Mairuwa.

Lamarin ya fusata Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Kasa, reshen Jihar Katsina har ta yi barazanar shiga yajin aiki. Bayan kwanaki 45 ’yan bindigar suka saki ma’aikacin bayan an biya kudin fansa.

A baya, a ranar 8 ga Disambar 2024, ’yan sanda sun yi nasarar daƙile yunƙurin yin garkuwa da mutane a wurare biyu daban-daban a Ƙananan Hukumomin Jibia da Faskari, inda suka ceto fasinjoji 20.

A Jibia, ’yan bindiga sun yi wa wata motar haya kwanton ɓauna a kan hanyar Katsina zuwa Magamar Jibia, amma jami’an tsaro suka fatattake su a wata musayar wuta, inda suka ceci duk fasinjoji 10 da ke cikin motar.

Rana guda kafin nan, a kan hanyar Funtua zuwa Gusau, ’yan bindiga suka kai hari kan wata mota ɗauke da fasinjoji 10.

Mun duƙufa yaƙi da ’yan bindiga — Gwamnati

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Gida na Jihar Katsina, Dakta Nasir Mu’azu, ya jaddada ƙudirin gwamnatin Dikko Raɗɗa na kare al’ummar Jihar Katsina da ma ƙasa daga ’yan ta’adda.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ta ce an yi da nasarar ceto mutane 10 da aka yi garkuwa da su, mata shida da maza hudu, waɗanda aka sace a yankunan Kiroro, Kabbi da Dogon Marke.

Sanarwar ta ce, “Bisa sahihan bayanan sirri da al’umma suka bayar, an gudanar da wani aikin haɗin gwiwa tsakanin kungiyar sa kai ta Katsina (C-Watch) da rundunar ’yan sandan Najeriya a Ƙaramar Hukumar Musawa a ranar 8 ga Afrilu, 2025.

“Aikin, wanda aka gudanar a Gidan Marke, ya kai ga kashe wani ɗan bindiga da kuma ceto waɗanda aka yi garkuwa da su lafiya, kuma tuni aka sake haɗa su da iyalansu.”

Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan ya nuna ƙaruwar ingancin tattara bayanan sirri daga al’umma da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro a Jihar Katsina.”

Dakta Mu’azu ya jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da kuma ƙara zafafa kai hare-hare kan masu miyagun laifuka a faɗin jihar.

Ya ce, “Za mu ci gaba da amfani da dukkan hanyoyin da suka dace don tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a cikin al’ummominmu.”

Ya kuma buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa matakan tsaro goyon baya ta hanyar samar da sahihan bayanan da suka dace a kan lokaci.

Dalilin karuwar hare-hare

A cewar mazauna da masu lura da al’amura, akwai wasu dalilai da suka haddasa ƙaruwar hare-haren a kwanakin nan. Sun bayyana cewa babban dalilin shi ne rashin yarjejeniyar zaman lafiya, kamar waɗanda aka cimma a wasu ƙananan hukumomin.

Wani muhimmin dalili kuma shi ne rashin kyawun hanyar, wacce a baya Gwamnatin Tarayya ta bayar da kwangilar gyara ta kafin daga bisani aka soke kwangilar.

Wasu sassan hanyar sun zama wuraren da mazauna yankin suka bayyana a matsayin wurare da masu haɗari ko kuma “tarkon mutuwa,” musamman sassan Tudu-Marabar Dan-Ali da ’Yargoje-Burdugau.

Wani mai amfani da shafukan sada zumunta ya wallafa tare da hoton wata motar da aka kai wa hari a kan hanyar, cewa, “Ya kamata direbobi su yi matukar taka-tsan-tsan a kan hanyar daga Mararaba zuwa Ƙanƙara, musamman tsakanin Burdugau da ’Yargoje. Waɗannan ’yan bindiga sukan kafa shingaye na wucin gadi don kama motoci.”

Wani rubutu a Facebook ya ƙara da cewa, “Wasu ’yan kasuwa sun tsira da ƙyar, duk da cewa an kai wasu mutane biyu asibiti. Allah Ya ba su lafiya. Ameen. Muna kira ga hukumomin da abin ya shafa da su magance hare-haren da ke ci gaba da faruwa a kan wannan hanyar.”

Wani mazaunin Ƙanƙara ya lura cewa al’ummomi da yawa sun yanke ƙauna, har ma wasu mutane suna ba wa ’yan bindigar haɗin kai.

Ya ce, “Na san wani mutum da ya kasance yana yin ƙananan ayyuka kamar saran itace. A yau, yana da babur da bindiga kuma an ce ya kashe wani ɗan banga ɗan ƙauyensu.”

Wani mazauni, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce ’yan bindigar yanzu suna kai hari tare da kashe mutanen da ake zargin suna ba da bayanan sirri ga hukumomin tsaro.

Ya ce, “Yawancin al’ummomin da ke yammacin Kankara a zahiri suna ƙarƙashin ikon ’yan bindiga. Har ma ana kai musu labarin saɓanin cikin gida.”

Ya tuna lokacin da aka ’ya’yan wani mutum ta farko suka kai wa ’yan bindiga ƙarar sa saboda ya auro mata ta biyu ba da amincewar mahaifiyarsu ba.

Ya ce, “Shugaban ’yan bindigar ya gaya wa yaran cewa shi ma yana da ’yan sandarsa da hukumar tsaro ta farin kaya, kuma ya kamata su kai irin waɗannan kararrakin ta hanyarsu. Daga karshe, wadannan da ake kira jami’an sun ‘kama’ mutumin, kuma an ci shi tarar Naira miliyan biyu saboda auren mata ta biyu ba da amincewar uwargidan ba.”

Wani mazaunin ’Yargoje ya ce duk da cewa an samu kwanciyar hankali a watan Ramadan, amma lamarin ya ƙara tabarbarewa tun daga lokacin.

A ranar Lahadin da ta gabata, ’yan bindiga sun gargadi al’ummomin da ke yammacin Ƙanƙara kan yiwuwar dawowar hare-hare saboda gazawar ƙoƙarin samar da zaman lafiya.

Ya ba da labarin cewa, “A ranar Lahadi, an kai hari a yammacin ’Yargoje wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu. A wannan rana, an yi wa wata motar haya kwanton ɓauna tsakanin Yargoje da Burdugau, amma babu wanda ya mutu, duk da cewa an harbi motar. Sannan a daren Talata, a kusa da wurin, an sake kai hari kan wata motar haya, aka raunata ’yan kasuwa biyu.”

Ya kara da cewa yawancin al’ummomin da ke yammacin Ƙanƙara yanzu sun zama kufai, in banda Dankumeji da wasu wurare ƙalilan ds har yanzu mutane ke zaune.

Ya ƙara da cewa watsi da aikin gyaran hanyar Funtua zuwa Ƙanƙara da aka yi ya ƙara tsananta matsalar tsaro a yankin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • MDD: Mafi Yawancin Wadanda Yaki Ya Ci A Gaza Mata Ne Da Kananan Yara
  • Yemen Ta Maida Martani Kan Wasu Cibiyoyin Ajiyar Makamai A Yaffa Don Tallafawa Gaza
  • Abubuwa Da Yawa Na Faruwa Ba Tare Da Sanin Tinubu Ba – Tsohon Ma’aikacin Aso Rock
  • Najeriya Ta Jaddada Aniyar Aiwatar Da Sakamakon Taron FOCAC Na Beijing
  • Amurka Ta Sayi Kayayyakin Nijeriya Na Dala Miliyan 643 A Wata 2 – Rahoto
  • Hizbullah ta kirayi gwamnatin Lebanon da ta dauki mataki kan hare-haren Isra’ila
  • Mutum Shida Sun Mutu A Hatsarin Jirgi Mai Saukar Ungulu A Amurka
  •  Amurka Ta Kai Hare-hare A Yankunan Kasa Yemen
  • Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna da takwaransa na Masar kan halin da ake ciki a yankin
  • Tarkon Mutuwa a Katsina: Hanyar Funtua zuwa Ƙanƙara