Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na tabbatar da gaskiya da adalci a shirin ciyarwa na azumin watan Ramadan da ke gudana a fadin jihar.

Shugaban kwamitin duba rabon abincin buda baki kuma wakilin mazabar Kiyawa, Alhaji Yahaya Muhammad Andaza, ya bada tabbacin haka lokacin da ya kai ziyarar bazata a wasu cibiyoyin ciyarwar.

A yayin ziyarar, kwamitin ya duba yadda ake gudanar da shirin a kananan hukumomin Birniwa da Kirikasamma da Guri da Hadejia, inda aikin kwamatin ya mayar da hankali ga tantance nasarar shirin da gano matsalolin da ke bukatar gyara.

A karshen ziyarar, Alhaji Yahaya Andaza wanda shi ne mataimakin mai tsawatarwa na majalisar, ya bayyana damuwa kan wasu kura-kurai da aka samu a cibiyar bada abincin buda baki ta garin Birniwa ta Farko, inda aka gano wasu matsaloli na rashin bin cikakken tsarin rabon abincin ga masu azumi.

Sai dai kuma, ya yaba da namijin kokarin wasu daga cikin masu dafa abinci a Kirikasamma da Hadejia, da Kasuwar Kofa, da Guri, inda shirin ke tafiya da yadda yakamata.

Wani matashi mai suna Abubakar Idris da ke kula da cibiya ta biyu a garin Guri ya samu kyakkyawan yabo daga ‘yan kwamitin, bisa tsarin da ya bi, inda a cibiyarsa ake samun dafadukar shinkafa mai kyau, hade da kifi da kwai, ko naman kaza, da kuma rarraba  kunu da kosai  a kullum ga masu azumi 300.

A cewar Usman Zakar Ayuba, jami’in kula da cibiyar Hadejia, sama da mutane 8,000 ne ake sa ran za su ci moriyar shirin a kullum a karamar hukumar Hadejia kadai.

Yana mai cewar, an kara cibiyoyi guda biyar a kan guda 22 da ke aiki a mazabu 11 na karamar hukumar.

Kazalika, Shugaban kwamatin Alhaji Yahaya Andaza ya bukaci duk masu dafa abincin azumi na Gwamnatin jihar Jigawan da su kasance masu gaskiya da adalci wajen gudanar da ayyukan su, tare da yin la’akari da darajar watan Ramadan ta hanyar tabbatar da cewa mabukata sun ci moriyar shirin yadda ya kamata.

A don haka, ya gargadi duk masu kokarin yin almundahana da kayayyakin abinci da aka tanada, yana mai cewar duk wanda aka samu da laifi na rage adadin kayan abinci kamar mudu 10 na gero don kunu, da mudu 10 na shinkafa don dafa-duka, da mudu 10 na wake don kosai, zai bandana kudarsa.

Radio Nigeria, ya bamu rahoton cewar, sama da naira miliyan dubu 4 ne gwamnatin Jigawa ta ware domin a ciyar da al’ummar musulmi da ke azumtar watan Ramadan a jihar.

Kwamitin ya kuduri aniyar ci gaba da sa ido a kan duk cibiyoyin ciyarwa a fadin jihar, domin tabbatar da cewar shirin yana tafiya yadda ya kamata.

Majalisar Dokokin ta kuma jaddada aniyarta na hukunta duk wanda aka samu da laifin yin almundahana, tare da daukar matakan da za su inganta shirin.

 

Usman Mohammed Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin Azumi

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Watan azumi lokaci ne da akan samu wasu ma’aikatu sun sassauta wa ma’aikata ta hanyar yi musu rangwame kamar rage musu yawan sa’o’in aiki.

Sai dai a lokacin da waɗannan mutane suke samun rangwame, akwai waɗanda suke ayyuka ko sana’o’in da suka dogara da su ciyar da iyalansu.

Sau da dama irin waɗannan mutane sai sun fita sun yi aiki a rana, duk da suna azumi, suke samun abin da za su saka a bakin salati.

NAJERIYA A YAU: Falalar Buɗa-baki Cikin Iyali A Lokacin Azumi DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana

Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin ladan da masu aikin ƙarfi suke samu yayin da suke azumi.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwamatin Majalisar Jigawa Ya Yi Rangadi A Cibiyoyin Ciyar Da Abincin Azumi
  • HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas
  • NNPC Da Dangote Na Shirin Ƙulla Sabuwar Yarjejeniya Kan Sayen Ɗanyen Mai
  • NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya
  • Rasha Ta Ce Babu Wani Abinda Zai Maye Gurbin  Yarjejeniyar JCPOA Ta Shirin Nukliyar Kasar Iran
  • Gwamnatin Kano Ta Bullo Da Sabbin Hanyoyin Kare Makarantunta Daga Kalubalen Tsaro
  • Ranar Mata: UNICEF Da Jihar Jigawa Sun Horar Sa Mata 600 Shirin Jari Bola
  • NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin Azumi
  •  Syria: Kungiyoyi Masu Dauke Da Makamai Suna Ci Gaba Da  Kai Wa Kauyukan Lazikiyya Da Tartus Hare-hare