HausaTv:
2025-03-12@16:37:47 GMT

 Uganda ta tura dakaru na musamman zuwa babban birnin Sudan ta Kudu

Published: 12th, March 2025 GMT

Rundunar sojan Uganda ta sanar da tura dakaru na musamman domin tabbatar da tsaro a babban birnin Sudan ta Kudu bisa bukatar Juba, a daidai lokacin da ake fargabar sake barkewar yakin basasa, musamman a halin da ake ciki tsakanin shugaban Sudan ta Kudu da mataimakinsa na farko.

A wannan Talata rundunar sojin Uganda ta sanar da tura dakaru na musamman zuwa Juba, babban birnin Sudan ta Kudu.

Kakakin rundunar sojin Uganda Felix Kulayigye ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, batun tura sojojin na zuwa ne bisa bukatar gwamnatin Sudan ta Kudu.

An kara samun tashin hankali a ‘yan kwanakin nan a kasar Sudan ta Kudu mai arzikin man fetur, bayan da gwamnatin shugaba Salva Kiir ta kame wasu ministoci biyu da wasu manyan jami’an soji da ke kawance da mataimakin shugaban kasar na farko Riek Machar. Tuni dai aka saki minista guda.

Kamen da aka yi a Juba da kuma kazamin fadan da ya barke a kusa da garin Nasir na arewacin kasar ana ganin zai kawo cikas ga yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2018 da ta kawo karshen yakin basasa na tsawon shekaru biyar tsakanin dakarun da ke biyayya ga Kiir da Machar inda aka kashe kusan mutane 400,000.

Bayan barkewar yakin basasa a Sudan ta Kudu a shekara ta 2013, Uganda ta aike da dakarunta zuwa Juba domin tallafawa dakarun Kiir da ke yaki da Machar. Daga karshe dai sojojin Uganda sun janye a shekarar 2015. An sake tura sojojin Uganda zuwa Juba a shekara ta 2016 bayan da aka sake gwabza fada tsakanin bangarorin biyu, amma kuma aka janye su daga bisani.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Yemen zata sake kai hare-hare kan jiragen ruwan Isra’ila

Kasar Yemen ta sanar da cewa za ta ci gaba da kai hare-haren soji kan jiragen ruwan Isra’ila a wasu muhimman yankunan teku da ke gabar tekun kasar bayan cikar wa’adin da ta gindaya wa Isra’ila na ta sake bude mashigar zirin Gaza tare da bayar da damar kai agaji cikin yankunan Falasdinawa da yaki ya daidaita.

Rundunar sojin Yaman ta fitar da sanarwar a cikin daren jiya, inda ta ce za a ci gaba da kai hare-hare kan duk wasu jiragen ruwa masu alaka da ISra’ila kamar yadda Abdul-Malik al-Houthi shugaban kungiyar gwagwarmayar Ansarullah ta kasar ya bada umurni.

Tunda farko Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya bai wa gwamnatin Isra’ila kwanaki hudu ta bude hanyoyin kai kayan agaji Gaza ko ta fuskanci martini.

Sanarwar ta kara da cewa “Wannan haramcin zai ci gaba da kasancewa har sai an sake bude hanyoyin shiga Zirin Gaza kuma an ba da izinin shigar da agajin jin kai da suka hada da abinci da magunguna.

A karshe sojojin sun jaddada goyon bayansu ga al’ummar Falasdinawa masu tsayin daka a yankin zirin Gaza da kuma gabar yammacin kogin Jordan da ke mamaye da su, wadanda kuma suka fuskanci mummunar ta’addancin Isra’ila, tare da jaddada goyon bayansu ga gwagwarmayar Falasdinawa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yemen zata sake kai hare-hare kan jiragen ruwan Isra’ila
  •  Uganda Ta Aike Da Sojoji Zuwa Sudan Ta Kudun Domin Kare Babban Birnin Kasar
  •  Ukraniya Ta Hai Wa Birnin Moscow Hari Da Jirage Marasa Matuki
  • Tutocin Falasdinu Sun Yi Ta Kadawa A Birnin Sao Paulo Na kasar Brazil, A Gagarumin Gaggami Da Masu Goyon Bayan Falasdinawa Suka Shirya
  • Sojojin Ruwa Na Kasashen Rasha Da China Sun Shigo Kasar Iran Don Fara Atisayen Sojojin Ruwa Mai Suna “Damarar Tsaro 2025”
  • Kwallon Mata: Nijeriya Ta Nuna Wa Afrika Ta Kudu Kwanji A Pretoria
  • Blatter da Platini sun sake gurfana a kotu kan zargin cin hanci
  • Sharhin Bayan Labarai: Kasashen Afirka Sun Kori Sojojin Faransa Daga Kasashensu
  • PDP ta sake ɗage babban taronta zuwa Mayun 2025