Aminiya:
2025-04-12@07:26:47 GMT

HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas

Published: 12th, March 2025 GMT

Rahotanni sun bayyana cewa Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta hana Gwamna Similanayi Fubara shiga cikinta a safiyar wannan Larabar.

Bayanai sun ce gwamnan ya ziyarci majalisar ne domin gabatar mata da Kasafin Kuɗin jihar na 2025.

Sai dai bayan isowar gwamnan tare da tawagarsa, ya tarar da ƙofar shiga majalisar a garƙame da kwaɗo kuma an ƙi buɗewa da ke tabbatar da alamar ba a maraba da shi.

Babu wani ƙwaƙwaran dalili da aka bayar, sai dai wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa an rufe wa gwamnan ƙofa ne saboda bai sanar da majalisar a hukumance cewa zai zo gabatar da Kasafin Kuɗin jihar ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Ribas Majalisar Dokoki Siminalayi Fubara

এছাড়াও পড়ুন:

UBEC Ta Bayyana Jihar Jigawa A Matsayin Abin Kuyi A Fannin Ilimi

Hukumar ilimin bai daya ta kasa wato UBEC ta yabawa Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa bisa jajircewar sa wajen inganta ilimi a matakin farko a Jihar.

Shugabar Hukumar, Hajiya Aisha Garba, ta bayyana hakan a yayin ziyarar gwamnan zuwa hedikwatar UBEC a Abuja.

Hajiya Aisha Garba ta bayyana jihar Jigawa a matsayin abin koyi ga sauran jihohin kasar nan.

Kazalika, ta jaddada irin yadda gwamnati ta zage damtse wajen zuba jari a harkar ilmi, tana mai cewa Jihar ta karɓi fiye da Naira biliyan 21 daga tallafin UBEC tun daga shekarar 2004, wanda ya sanya ta cikin jihohin da suka fi cika sharudan samun tallafin UBEC.

Ta kuma lissafa wasu daga cikin nasarorin da aka cimma a ƙarƙashin Gwamna Namadi wadanda suka hada da gina fiye da ajujuwa 3,000 da rijiyoyi 500 da daukar malaman makaranta fiye da 7,000.

Tace Gwamnatin ta kuma horas da malamai sama da 17,000 da kaddamar da Kungiyoyin Iyaye Mata da Ƙarfafa Kwamitocin Gudanarwar Makarantu wato SBMC da kuma kulla haɗin gwiwa da wani kamfani a shirin Jigawa UNITES.

A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya jaddada cewar, gwamnatin sa ta himmatu wajen sauya tsarin karatu da inganta sakamako ta hanyar amfani da bayanai da kuma haɗa kai da al’umma.

 

Usman Mohammed Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Namadi Na Jihar Jigawa Ya Cancanci Karramawar LEADERSHIP – Hamisu Gumel
  • UBEC Ta Bayyana Jihar Jigawa A Matsayin Abin Kuyi A Fannin Ilimi
  • Za a mayar da tubabbun ’Yan Boko Haram cikin al’umma – Gwamna Buni
  • Majalisar Kano Ta Yi Murna Da Lambar Yabo Da Jaridar LEADERSHIP Ta Bai Wa Abba
  • Gwamnan Zamfara Ya Yi Jajen Rasuwar Dan Majalisa Aminu K/Daji
  • Gwamna Lawal Ya Yi Jimamin Rasuwar Ɗan Majalisar Zamfara, Aminu K/Daji
  • Gwamnan Zamfara Ya Yi Jimamin Rasuwar Ɗan Majalisar Zamfara, Aminu K/Daji
  • Zuba Jari Daga Kasashen Waje A Noman Zamani: Jigawa Ta Baje Kolin Aikin Noma A Abuja
  • Majalisar Jihar Kaduna Ta Bude Bincike Kan Ginin Kasuwa da Aka Yi Watsi da Shi
  • Ibas ya naɗa kantomomin ƙananan hukumomin Ribas