HOTUNA: Fashewar tankar gas ta kashe gomman mutane a Legas
Published: 12th, March 2025 GMT
Wata tanka ɗauke da gas ta yi bindiga a Jihar Legas da ke kudu maso yammacin Nijeriya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane da jikkata da dama.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata da dare a ƙarƙashin gadar mota ta Otedola, wadda tana daga cikin manyan hanyoyin da ke haɗe Legas da sauran sassan ƙasar.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da tankar ke ƙoƙarin juyawa domin kai gas ɗin wani gidan mai, inda a nan ne ta faɗi ta yi bindiga.
Mutane da dama da suka shaida lamarin sun ce ya ƙazanta, sakamakon yadda wuta ta kama motoci da dama da kuma gidaje da ke kusa.
Wakilin kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya tattauna da wani mutum da ya tsira da ransa sakamakon lamarin.
“Tankar ta faɗo kan motata, inda ta tura ta gefen hanya. Sai na yi sauri na gudu bayan na gano cewa gas ne, sai tankar ta yi bindiga cikin ƙasa da minti uku,” in ji Ajayi Segun, wanda ya rasa motarsa ƙirar Sienna sakamakon faruwar lamarin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, a wani rahoto na wucin-gadi da ya fitar ya tabbatar da cewa lamarin ya rutsa da gidaje huɗu tare da haka kuma motoci 15 sun ƙone ƙurmus.
“Ana zargin hatsarin ya afku ne a lokacin da motar ke kokarin hawan hanyar Legas zuwa Ibadan ta gadar Otedola,” inji shi.
“Saboda haka, motar ta kife a kan hanya sannan ta yi bindiga nan take.”
“Har yanzu ana kididdige adadin rayukan mutanen da aka rasa, domin an gano gawawwaki biyu ne kawai.
“Lamarin ya kuma shafi wani asibiti mai zaman kansa, sai dai har yanzu babu cikakken bayani game da halin da waɗanda lamarin ya shafa a can.
“Za a ci gaba da bayar da rahoto a yayin da ake ci gaba da aikin ceto,” kamar yadda ya bayyana.
Jami’in Hukumar Agajin Gaggawa na Kasa (NEMA) shiyyar Kudu maso Yamma, Ibrahim Farinyole, ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa suna ci gaba da ƙididdige asarar da aka yi.
A cewarsa, mutum daya ya mutu yayin da wasu hudu suka jikkata baya ga motoci 14 da shaguna hudu da suka ƙone ƙurmus.
A cikin ‘yan watannin nan, an samu fashewar tankokin mai dama a Nijeriya inda kusan mutum 300 suka rasu a ƙasar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Legas Tankar Gas
এছাড়াও পড়ুন:
Harin Lakurawa: An Kashe Mutane 15 Tare Da Kona Kauyuka 7 A Birnin Kebbi
Shugaban karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi, Alhaji Sani Aliyu, ya tabbatar da harin da ‘yan ta’addan Lakurawa suka kai a yankin, inda suka kashe mutane kimanin 15 tare da kona kauyuka 7.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga gidan rediyon Najeriya da ke jihar Kebbi, shugaban karamar hukumar ya ce an baza jami’an tsaro a yankin domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
A cewar wata majiya mai tushe, Malam Umar, maharan sun kara kona akalla wasu kauyuka bakwai da ke kusa da Birnin Dede, duk a cikin karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbin.
A wata tattaunawa ta wayar tarho, Malam Umar ya bayyana cewa, an kai harin ne domin ramuwar gayya kan kisan da jami’an tsaro suka yi wa shugaban nasu a makon da ya gabata, inda ya kara da cewa, maharan sun bar kauye daya ne kawai, wanda sojoji ke gadinsa.
“Harin na daren Lahadin da ta gabata tamkar ramuwar gayya ne biyo bayan kashe shugaban Lakurawa, Maigemu da hadin gwiwar jami’an tsaro suka yi a Kebbi”.
Sai dai Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi, SP Nafiu Abubakar, bai amsa kiran waya ko sakon waya da ake neman karin bayani kan lamarin ba.
Daga Abdullahi Tukur