Shugaban kwamatin duba rabon abincin azumi na majalisar dokokin jihar Jigawa a shiyyar Dutse kuma mataimakin Shugaban Majalisar, Alhaji Sani Isiyaku Abubakar ya bukaci masu aikin dafa abincin a karamar hukumar Gwaram da su dauki wannan aiki a matsayin turbar samun lada daga Allah Madaukakin Sarki ba wai hanyar neman riba kadai ba.

Alhaji Sani Isayku Abubakar ya yi wannan kiran ne lokacin da ya jagoranci Yan kwamatin domin duba aikin dafawa da kuma rabon abincin azumi a unguwar Sabon Layi da ke karamar hukumar Gwaram.

Ya ce rangadin duba rabon abincin azumi na daga aikin majalisa na duba ayyuka da shirye-shiryen gwamnati domin tabbatar da inganci da kuma shugabanci nagari.

Alhaji Sani Isayku Abubakar tare da Yan kwamatin sun bukaci mai aikin dafa abincin da ya kara yawan shinkafa da ake baiwa kowanne mutum daya, tare da kayan miya domin samun dandano mai gamsarwa.

A nasa jawabin, shugaban karamar hukumar Gwaram Farfesa Abdulrahman Saleem Lawan ya ce akwai cibiyoyin rabon abincin azumi guda 22 a mazabu 11, yayin da ya Samar da cibiya ta 23 a gidansa domin mara baya ga kokarin gwamnatin jihar na ciyar da jama’a a watan Ramadan.

Kwamatin ya kuma duba rabon abincin azumi a cibiyar da ke Babban Masallacin Juma’a na Gwaram da ke fadar Hakimin Gwaram.

Usman Mohammed Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: rabon abincin azumi

এছাড়াও পড়ুন:

Hisbah ta warware rigingimu 565 da lalata katan 51 na barasa a Yobe

Hukumar Hisbah ta Jihar Yobe ta ce, ta warware rigingimu 565 a cikin watanni 12 da suka gabata a jihar.

Wannan hukuma dai gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya kafa ta a watan Maris, 2024 a wani ɓangare na ƙoƙarin magance munanan ɗabi’u a jihar.

Trust Radio 92.7FM za ta fara shirye-shiryen gwaji An kama masu garkuwa da mutane biyu a Yobe

Shugaban Hukumar ta Hisbah, Dakta Yahuza Hamza Abubakar, ya ce matsalolin da aka warware sun haɗa da batutuwan da suka shafi: Harkar iyali da kasuwanci da gado da kuma basussuka.

Sauran matsalolin da hukumar ta Hisbah ke warwarewa sun haɗa da: Matsalolin da haddasa rikicin manoma da makiyaya da kuma rashin biyan kuɗin haya.

A cewarsa, an warware akasarin shari’ar ta hanyar sulhu da fahimtar juna.

Dokta Hamza ya ce, jami’an hukumar sun kuma ƙwace kwalayen barasa guda 56 da kuma 18 na sinadaran fosters na methylene chloride chemical (Madarar Sukurdai) a faɗin jihar.

Ya ce, addinin Musulunci da dokar da ta kafa hukumar a shekarar 2024 ta haramta sayar da barasa da sauran kayan maye a jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • 2027: Masu Shirin Yin Kawance Na Duba Yiwuwar Zakulo Dan Takarar Da Zai Yi Wa’adi Daya
  • Ruwan Sama Ya Lalata Gidaje Sama Da 240 A Kebbi
  • Babban Taron LEADERSHIP Karo Na 17: Tinubu Ya Kare Yadda Gwamnatinsa Ke Tafiyar Da Tsarin Rabon Arzikin Kasa
  • Hisbah ta warware rigingimu 565 da lalata katan 51 na barasa a Yobe
  • UBEC Ta Yaba Wa Jigawa Kan Inganta Harkar Ilimi A Jihar
  • Majalisar Kano Ta Yi Murna Da Lambar Yabo Da Jaridar LEADERSHIP Ta Bai Wa Abba
  • Al’ummar Karamar Hukumar Maigatari Sun Bukaci Gwamnatin Jigawa Ta Gina Musu Hanyoyi
  • Hajjin 2025: Jihar Kaduna Ta Yi Tanadin Masauki Na Musamman Ga Alhazan Bana
  • Zuba Jari Daga Kasashen Waje A Noman Zamani: Jigawa Ta Baje Kolin Aikin Noma A Abuja
  • Majalisar Jihar Kaduna Ta Bude Bincike Kan Ginin Kasuwa da Aka Yi Watsi da Shi