‘Yansanda Sun Daƙile Yunƙurin Yin Garkuwa Da Mutanen 30 A Katsina
Published: 12th, March 2025 GMT
“Bayan samun rahoton, jami’in ‘yansanda reshen Faskari ya yi gaggawar tara tawagar jami’an tsaro zuwa wurin.
“Rundunar ta hanyar amfani da dabaru, ta yi kwanton bauna, inda ta rikita ‘yan bindigar da ruwan harsashi wanda ya hakan ya ta tilasta musu guduwa da raunuka daban-daban, an yi nasarar ceto dukkan mutanen 30 da aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji rauni ba, kuma an kwato dabbobin da suka sace.
“Kwamishanan ‘yansandan jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, ya yaba wa jami’an da suka nuna kwazo da jajircewa wajen gudanar da aikin ceto, ya bukaci jama’ar jihar da su ci gaba da bayar da hadin kai ga rundunar ta hanyar samar da sahihin bayanai a kan lokaci domin daukar matakin gaggawa kan masu aikata muggan laifuka,” In ji Sadiq
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Dan ta’adda zai biya tarar miliyoyi bayan shan dukan kawo wuka a Katsina
Wani dan bindiga da ya karya yarjejeniyar sulhu a Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina mai suna Bala Wuta na Garin Mazanya, na can kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai bayan ya sha dukan kawo wuka.
Tubabbun ’yan bindiga sun yi wa Bala wuta takakkiya ne har gida inda suka yi masa bugun dawa, bayan da ya yi garkuwa da wasu matafiya jim kadan bayan sulhun da aka yi, inda bayan sun lugwiwita shi, suka wajabta masa biyan tarar Naira miliyan uku.
HOTUNA: Fashewar tankar gas ta kashe gomman mutane a Legas HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin RibasAna iya tuna cewa, a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2025 ne aka yi sulhun, wanda ya samu wakilcin sojoji da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro da masu ruwa karkashin jagorancin shugaban karamar hukumar ta Jibiya Alhaji Maitan, kamar yadda su ’yan bindigar suka nema.
’Yan bindigar da suka halarci zaman a karkashin jagoransu Audu Lankai, sun hada da Kantoma da Ori da Tukur Dan Najeriya da Bammi da sauransu da suka fito daga yankin Zamfara.
Yarjejeniyar da aka kullaJama’ar yankin sun shimfida wa ’yan bindiga sharadin barin kai hare-hare a fadin karamar hukumar da hanyar Katsina zuwa Jibiya da hanyar Jibiya zuwa Gurbi da kuma wadda ke zuwa Batsari.
Za kuma su da daina kai hari ko barna a gonaki ko cikin daji ko guje-guje a kan babura a cikin garin ko nuna rashin da’a ko tarbiyya ga al’umma.
Kazalika, yarjejeniyar ta bukaci za su kiyaye duk dokokin gwamnati su kuma daina yawo da makamai a bainar jama’a.
A nasu bangaren, tubabbun ’yan bindigar dajin sun shardanta a daina kashe su ko kama dabbobinsu babu dalili da kuma tabbatar da adalci a tsakaninsu da sauran al’umma a matsayinsu na ’yan kasa.
Sa’annan sun bukaci a daina daukar doka da hannu a rika barin hukuma ta yi hukunci ga mai laifi.
Bayan nan ne suka sako mutane 10 na garin Daddara da ke hannunsu tare da mika bindiga kirar AK-49 guda biyu.
Sai dai duk da wannan yarjejeniyar sulhu da aka kulla, sai ga shi a ranar Alhamis da ta gabata, wani wanda bai shiga sulhun ba mai suna Bala Wuta na Garin Mazanya da ya addabi hanyar zuwa Jibiya, ya kayar da wata mota ya yi awon gaba da matafiya a Mallamawar Batsari — garin su Lankai.
A dalilin haka shi Audu Lankai jagoran sasanci ya taras da shi har gida ya yi mishi dukan kawo wuka sannan ya sanya masa tarar kudi har naira milyan uku.
Har zuwa yanzu, wakilinmu ya ruwaito cewa, Bala Wuta yana can kwance yana jin jiki a garin na Mazanya.
Labarin da muka samu daga garin na Jibiya an ce, a ranar Lahadi an ga Fulanin da ke cikin dajin sun shigo kasuwa mazansu da matansu cikin murna saboda samun wannan ’yanci.
Majiyarmu ta shaida mana cewa, Fulanin sun rika sayen lemon kwalba mai sunyi da ake sayarwa Naira 250, wanda suke cewa a can daji naira dubu ake sayar musu.