Ministan Yaki Na HKI Yace Sojojin HKI Zasu Ci Gaba Da Zama A Kasar Siriya Har’abada
Published: 12th, March 2025 GMT
Minisyan yaki na HKI Israel Kazt ya bayyana cewa sojojin HKI za su ci gaba da zama a kasar Siriya har zuwa illa masha allah, don kare yahudawan da suke zaunwa a tuddan Golan na kasar Siriya da suka mamaye a yakin kwanaki 6 a shekara ta 1967.
Tashar talabijin ta Presstv TV ta nakalto ministan yakin ya na fadar haka a jiya Talata, a lokacinda ya kai ziyara kan ‘Jabal Sheikh’ wani tsauni mai muhimmanci a fagen tsaro, wanda sojojin HKI suka mamaye bayan faduwar gwamnatin Bashar Al-Asad da yan kwanaki.
Jabal sheikh dai yana da tsawo sosai ta yadda ana iya kallon dukkan yankunan da ke kusa da shi a cikin kasar Lebanonn da kuma cikin birnin Damascus babban birnin kasar ta Siriya.
Jabal Sheik dai yana tazarar kilomita 20 kacal daga fadar gwamnatin kasar ta Siriya.
Daga karshe yace sojojin Israila sun dawo kasar Siriya ne, ba ranar da zasu bar fice daga kasar.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Siriya
এছাড়াও পড়ুন:
China Ta Karawa Kayakin Masu Shiga Kasar Kudaden Fito Har Zuwa Kashi 84%
Gwamnatin kasar China ta bada sanarwan kara kodaden fito kan kayakin Amurka wadanda suke shigowa kasa har na kasha 80% sannan a shirye take ta ci gaba da yakin kasuwanci da gwamnatin shugaba Trump har zuwa karshe.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jami’an gwamnatin kasar China na fadar haka a yau Laraba sun kuma kara da cewa, idan gwamnatin Trump bata dakatar da wannan yakin kasuwanci ba to kasar China tana da hanyoyi da dama wadanda zata ci gaba da wannan yakin har zuwa karshe.
Kafin haka dai gwamnatin shugaba Trump ta karawa kayakan kasar China masu shigowa Amurka kudaden fito daga kashe 34% zuwa kasha 104 % kuma a yau Laraba ne dokar karin zai fara aiki. Amma karin da gwamnatin kasar China ta yi zai fara aiki ne a ranar 10 ga watan Afrilu da muke ciki wato gobe Alhamis.
A ranar laraban da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya kara kudaden fito ga kasashen duniya da dama daga cikin har da kasar China wacce ta maida martani bayan kwanaki biyu da kwatankwacin abinda Amurka ta kara mata.