HausaTv:
2025-03-13@01:05:33 GMT

Iran Ba Zata Karbi Umrni Daga Wani Kan Shrin Nukliyar Kasar Ba

Published: 12th, March 2025 GMT

Mohammad Reza Aref mataimakin shugaban kasa na farko a nan JMI ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran ba zata karbi umurni daga wata kasa dangane da shirin makamashin nukliya ta zaman lafiya na kasar ba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Reza Aref yana fadar haka a jiya Talata, ya kuma kara da cewa, JMI ta na ci gaba da jajircewa da takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma suka dora mata, dangane da shirin kasar na amfani da fasahar Nukliya.

Sai dai har yanzun ba zata nemi shawara ko karbi umurni daga wata kasa a kan amfani da wannan fasaha mai dimbin amfani ba.

Mataimakin shugaban kasar ya ce, sinadarin Nukliya ya na da matukar amfani kuma mai yawa, bai kamata a haramtawa wasu kasashe amfani da shi ba.

Banda haka ya ce, fasahar nukliya ci gaba ne, idan an hada tsarin  addinin musulunci da ke gudanar da kasar, ci gaba ne mai yawa. Yace kasar Iran tana da arziki mai yawa tare da wadannan abubuwa biyu.

Yace ammam wasu kasashe a duniya suna sun su takaita wannan fasahar garesu su kadai, don su rika bautar da mutane. Basa son ganin Iran ta kai ga wannan fasahar, don haka sun samar da ra’ayin kin iraniyawa a duniya.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Najeriya ta yi hasashen samun karuwar kashi 4.6 cikin dari na GDP a 2025

Gwamnatin Najeriya a ranar Talata ta bayyana fatanta na ganin tattalin arzikin kasar zai karu da a kalla kashi 4.6 cikin dari a shekarar 2025, daga kashi 3.19 a shekarar 2024.

Da yake kaddamar da wani cikakken tsarin tattalin arziki na samun ci gaba mai dorewa a babban birnin tarayyar Abuja, ministan kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arzikin kasar, Wale Edun, ya ce har yanzu daidaita sassan tattalin arzikin kasa shi ne abin da aka fi sa a gaba, tare da samun daidaito a darajar musayar kudi, da rarar cinikayya, da karuwar samar da man fetur da ke sanya kasar a matsayin kasa mai karfi a duniya.

A sa’i daya kuma, hukumar kididdiga ta kasa a baya ta bayar da rahoton cewa, jimillar darajar kayayyakin cikin gida wato (GDP) ya karu da kashi 3.84 cikin dari a rubu’i na hudu na shekarar 2024, idan aka kwatanta da makamancin lokaci a 2023, inda jimillar ta karu daga kashi 3.46 a rubu’i na baya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Tace Wani Dan Sako Daga UAE Ne Zai Isar Da Sakon Trump Zuwa  Tehran
  • Yemen zata sake kai hare-hare kan jiragen ruwan Isra’ila
  • Najeriya ta yi hasashen samun karuwar kashi 4.6 cikin dari na GDP a 2025
  • Matsin Amurka Ya Zama Zaburarwa Ga Kasar Sin Wajen Kara Samun Ci Gaba
  • Araghchi: Gwamnatin Amurka ta haramta wa Irakawa samun wutar lantarki
  • An Gabatar Da Motar Asibiti Ta Farko Mai ISO Na Matsayin Kasa Da Kasa A Hukumance
  • Iran Tace:Tattaunawa Tare Da Barazana Ba Tattaunawa Ba Ce, Sai Dai Tursasawa
  • Iran Ta Ce Shirinta Na Makamashin Nukliya Na Zaman Lafiya Ne, Kuma Ba Zata Tattauna Da Amurka Karkashin Barazana Ba
  • Rasha Ta Ce Babu Wani Abinda Zai Maye Gurbin  Yarjejeniyar JCPOA Ta Shirin Nukliyar Kasar Iran