Iran Tace Wani Dan Sako Daga UAE Ne Zai Isar Da Sakon Trump Zuwa Tehran
Published: 12th, March 2025 GMT
Wani jami’an gwamnatin kasar UAE ne zai isar da sakon shugaban kasar Amurka Donal Trump zuwa Tehran.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baghani ya na fadar haka. Ya kuma kara da cewa a halin yanzu mai bawa shugaban kasa shawara na kasar UAE Anwar Gargash yana kan hanyarsa ta zuwa Tehran dauke da wasikar, don isar da ita ga jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaei.
Labarin ya kara da cewa Gargash zai hadu da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi da farko bayan isarsa birnin Tehran.
Kafin haka dai Majid Takht-Ravanchi mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan al-amuran siyasa, wanda ya je kasar UEA don halattar taron kwamitin siyasa na kasashen biyu ya gana da Gargash inda suka tattauna batun wasikar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Yaki Na HKI Yace Sojojin HKI Zasu Ci Gaba Da Zama A Kasar Siriya Har’abada
Minisyan yaki na HKI Israel Kazt ya bayyana cewa sojojin HKI za su ci gaba da zama a kasar Siriya har zuwa illa masha allah, don kare yahudawan da suke zaunwa a tuddan Golan na kasar Siriya da suka mamaye a yakin kwanaki 6 a shekara ta 1967.
Tashar talabijin ta Presstv TV ta nakalto ministan yakin ya na fadar haka a jiya Talata, a lokacinda ya kai ziyara kan ‘Jabal Sheikh’ wani tsauni mai muhimmanci a fagen tsaro, wanda sojojin HKI suka mamaye bayan faduwar gwamnatin Bashar Al-Asad da yan kwanaki. Da kuma bayan da Abu Mohammed al-Julani shuga kungiyar Deash ya shiga fadar gwamnati a Damascus.
Jabal sheikh dai yana da tsawo sosai ta yadda ana iya kallon dukkan yankunan da ke kusa da shi a cikin kasar Lebanonn da kuma cikin birnin Damascus babban birnin kasar ta Siriya.
Jabal Sheik dai yana tazarar kilomita 20 kacal daga fadar gwamnatin kasar ta Siriya.
Daga karshe yace sojojin Israila sun dawo kasar Siriya ne, ba ranar da zasu bar fice daga kasar.