Leadership News Hausa:
2025-03-13@00:58:25 GMT

Yawan Bishiyoyin Da Aka Dasa A Kasan Kasar Sin Ya Kai Kashi 25%

Published: 12th, March 2025 GMT

Yawan Bishiyoyin Da Aka Dasa A Kasan Kasar Sin Ya Kai Kashi 25%

Yau ce ranar dasa bishiyoyi ta kasar Sin, kuma albarkacin ranar ofishin kwamiti mai kula da harkokin dasa bishiyoyi na Sin ya gabatar da sanarwar karuwar yawan bishiyoyi da Sin ta dasa, wadda ta nuna cewa, Sin ta gabatar da manyan tsare-tsaren kiyaye muhalli, don daidaita harkoki masu nasaba da hakan a shekarar 2024, inda aka samu ci gaba mai armashi a bangaren dasa bishiyoyi.

Sanarwar ta nuna cewa, a wannan shekara Sin ta dasa itatuwa hekta miliyan 4.446, da ciyayi hekta miliyan 3.224, da kuma daidaita kasa mai rairayi hekta miliyan 2.783, hakan ya sa yawan fadin gandun daji ya kai kashi 25%.

Tun lokacin da aka kira taro karo na 18 na jam’iyyar JKS, hukumar lura da itatuwa da ciyayi ta Sin ta aiwatar da manyan ayyukan dasa bishiyoyi da habaka fadin gandun daji, da kyautata ingancin itatuwa da kiyaye albakatun bishiyoyi. Yawan itatuwa da Sin ta dasa a wurare masara shuke-shuke ya kai hekta miliyan 77.33, hakan ya sa Sin ta zama kasa mafi samun ci gaba wajen dasa bishiyoyi. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: hekta miliyan

এছাড়াও পড়ুন:

Matsin Amurka Ya Zama Zaburarwa Ga Kasar Sin Wajen Kara Samun Ci Gaba

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta soki kalaman sakataren baitul-malin Amurka da ya bayyana dangantakar tattalin arziki dake tsakanin kasashen biyu a matsayin zamba.

An shafe gomman shekaru ana huldar cinikayya tsakanin bangarorin biyu, a gani na, idan har akwai zamba a ciki, ba na jin huldar za ta kawo matakin da take kai a yanzu. Abun da Amurka ta kasa ganewa shi ne, ita kanta da sauran duniya sun fi bukatar Sin. Idan Amurka ta ci gaba da ta da yakin cinikayya, sai ta fi kowa dandana radadin matakanta, la’akari da yadda kayayyakin kasar Sin suka bunkasa sayayya a kasar. Kana masana sun yi hasashen munanan matakan, za su haifar da raguwar GDPnta da hauhawar farashin kayayyaki da rashin ayyukan yi a kasar da sauransu.

Bayan Shekaru 115 Manchester United Za Ta Gina Sabon Filin Wasa Zafin Rana Zai Tsananta A Wasu Jihohin Nijeriya – NiMet

Abun da ya kamata Amurka da kawayenta su gane shi ne, kasar Sin ta fi mayar da hankali kan habaka bukatun cikin gida domin karfafa tattalin arzikinta maimakon dogaro da kasashen waje. Matsin da Amurka ta dade tana yi wa kasar Sin, ya kara tabbatar da cewa, tattalin arzikin Sin ba ya dogaro da kasashen waje, bisa la’akari da yadda matsin bai sa tattalin arzikin ya durkushe ba, maimakon haka, ya zama wani karin zaburarwa ga kasar Sin ta nacewa ga habaka bukatun cikin gida da kirkire-kirkire, domin biyan bukatunta da na sauran kasashe duniya.

Yayin gabatar da rahoton aikin gwamnati ga majalisar dokokin kasa a makon jiya, firaministan Sin Li Qiang ya ce kasar na da burin habaka tattalin arzikinta da kaso 5 cikin dari a bana, lamarin da ya ja hankalin duniya matuka. Hakika wannan buri da ta sanya gaba, ya kara bayyanawa duniya kwarin tubalin tattalin arzikinta da kuma irin ci gaba da za ta samu. Har kullum na kan ce, ci gaban kasar Sin, ci gaba ne ga duniya baki daya. A matsayinta na babbar abokiyar cinikayya ta kasa da kasa, kuma cibiyar kirkire-kirkire a duniya, kana mai bayar da gudummawar kaso 1 bisa 3 na ci gaban tattalin arzikin duniya, karuwar tattalin arziki da ci gaban Sin babbar dama ce kuma abun murna ga kasashe musamman masu tasowa. (Faeza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ba Zata Karbi Umrni Daga Wani Kan Shrin Nukliyar Kasar Ba
  • NAHCON Za Ta Fara Jigilar Alhazai Ranar 5 Ga Watan Mayun 2025
  • Najeriya ta yi hasashen samun karuwar kashi 4.6 cikin dari na GDP a 2025
  • Matsin Amurka Ya Zama Zaburarwa Ga Kasar Sin Wajen Kara Samun Ci Gaba
  • A Cikin Shekara Daya EFCC Ta Kwato Dalar Amurka Miliyan 500
  • Majalisar Dokokin Kasar Sin Ta Rufe Zaman Taronta Na Shekara-shekara
  • Kasar Sin Ta Mayar Da Martani Kan Kalaman Sakataren Baitul Malin Amurka
  • Kasancewar “Taiwan A Matsayin Lardin Kasar Sin” Shi Ne Matsayin MDD A Ko Yaushe 
  • Rasha Ta Ce Babu Wani Abinda Zai Maye Gurbin  Yarjejeniyar JCPOA Ta Shirin Nukliyar Kasar Iran