Jagora : kiran Trump, na tattaunawa Da Iran yaudarar duniya ne
Published: 13th, March 2025 GMT
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce kiran da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na tattauanwa da Iran ba komai ba ne illa wani yunkuri na yaudarar al’ummar duniya.
“Mun zauna tsawon shekaru muna tattaunawa, mun zamna da su teburin tattaunawa, bayan hakan shi wannan mutumin ya yayyaga yarjejeniyar da aka sanya wa hannu,” kamar yadda jagoran ya bayyana yayin da yake jawabi ga taron dalibai a birnin Tehran a jiya Laraba.
“tunda mu ka ga baya girmama yarjejeniya, menene ma’anar yin shawarwari kuma ?”
“Saboda haka, kiraye-kirayen yin shawarwarin da tattaunawa na da nufin yaudarar jama’a na duniya.” Inji jagoran.
Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce “Idan manufar tattaunawar ita ce a dage takunkumin, yin shawarwari da wannan gwamnatin Amurka, ba za ta cire takunkumin ba. Hakan zai sa takunkumin ya kara tsananta tare da kara matsin lamba,” in ji Jagoran.
Yayin da yake mayar da martani kan zargin da kasashen yammacin duniya ke yi na cewa Tehran na neman makaman nukiliya, Jagoran ya sake jaddada cewa Iran ba ta son kera makaman kare dangi, inda ya kara da cewa da ta yi niyyar yin hakan da ta yi shi ya zuwa yanzu.
“An ce ‘ba za mu bar Iran ta samu makaman nukiliya ba.’ Da muna son kera makaman nukiliya, da Amurka ba za ta hana mu ba.
Gaskiyar ita ce ba mu da makaman nukiliya, saboda mu da kanmu ba ma son su saboda wasu dalilai.”
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: makaman nukiliya
এছাড়াও পড়ুন:
EU ta jadadda bukatar warware batun Iran ta hanyar diflomasiyya
Kungiyar tarayyar turai ta jaddada bukatar warware batun Iran ta hanyar diflomatsiyya.
Da taek sanar da hakan babbar Jami’ar kula da harkokin ketare ta kungiyar ta ce babu wata hanyar da za’a bi wajen warware matsalar Iran in ba ta diflomasiyya ba.
‘’ta hanyar diflomatsiyya ne za’a warware takaddamar da ake game da batun yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015 da iran, inji Kaja Kalas.
Da take magana a taron shekara-shekara na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan hadin gwiwa tsakanin EU da Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, babbar jami’ar ta Tarayyar Turai ta ce “ci gaba da fadada shirin nukiliyar Iran ya sabawa alkawurran da Iran ta dauka kamar yadda kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da shi.
“A lokaci guda kuma, hanyar da ta shafi bangarori daban-daban, kamar yarjejeniyar, tana da mahimmanci.
Ta ce, “Babu wata hanyar da za ta dore wajen warware matsalar sai ta diflomasiyya,” in ji ta, a cewar shafin yanar gizon EU External Action.
A kwanan ne dai shugaban AMurka Donald Trump, y ace ya aike da wasiga ga Iran, na ta bude tattaunwa ko kuma ya yi da karfin soji.
Iran dai ta musanya samun wata wasika daga Trump, kuma tana mai cewa babu batun tattaunawa bsia matsin lamba da barazana.