Yadda ’yan Boko Haram suka sha da ƙyar a hannun tawagar Gwamna Zulum
Published: 13th, March 2025 GMT
Jami’an tsaro da ke rakiyar tawagar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, sun daƙile wani harin Boko Haram a kusa da garin Gujba a Jihar Yobe.
Gwamnan da tawagarsa na kan hanyarsu ta komawa Maiduguri daga Biu lokacin da suka haɗu da ’yan ta’addan, wanda hakan ya tilasta musu tserewa bayan musayar wuta.
Bayanai sun ce dakarun tawagar sun ƙwato bindigogi, harsasai, babur, tare da ceto wasu fasinjoji da aka sace.
Wani direba da aka ceto, Malum Ari, ya bayyana yadda maharan suka tare hanyar: “Sun karɓe motata suka tilasta mana kwanciya a ƙasa.
“Amma da suka hango tawagar gwamna, sai suka firgita suka tsere. Wani daga cikinsu ya faɗi a kasa sau biyu kafin ya tsere saboda tsananin firgici.”
Wani fasinja da aka ceto ya koka kan yadda hare-haren suka zama ruwan dare: “Boko Haram na tare hanya da tsakar rana. Ba mu da kwanciyar hankali kwata-kwata.”
Wannan na zuwa ne kwana uku bayan da ’yan ta’adda suka kai hari gari Gujba, inda suka kashe wani ɗan sa-kai mai suna Modu Bulama, tare da ƙone gidaje da shaguna.
Wani jami’in tsaro da ya shaida lamarin ya ce, “Waɗannan ’yan ta’adda sun ƙara samun ƙarfi sosai. Suna kai hare-hare ba tare da tsoro ba. Dole a ɗauki ƙwararan matakai don tabbatar da tsaro.”
A baya-bayan nan ne mayaƙan Boko Haram suka sace wani Farfesan Jami’ar Soji ta BIU da ke Jihar Borno (NAUB) da wasu fasinjoji.
Haka kuma sun sace wani alƙalin kotun Borno, wanda daga baya suka sako shi bayan biyan kuɗin fansa mai yawa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram Jami an Tsaro Tawaga
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ba Zata Karbi Umrni Daga Wani Kan Shrin Nukliyar Kasar Ba
Mohammad Reza Aref mataimakin shugaban kasa na farko a nan JMI ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran ba zata karbi umurni daga wata kasa dangane da shirin makamashin nukliya ta zaman lafiya na kasar ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Reza Aref yana fadar haka a jiya Talata, ya kuma kara da cewa, JMI ta na ci gaba da jajircewa da takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma suka dora mata, dangane da shirin kasar na amfani da fasahar Nukliya.
Sai dai har yanzun ba zata nemi shawara ko karbi umurni daga wata kasa a kan amfani da wannan fasaha mai dimbin amfani ba.
Mataimakin shugaban kasar ya ce, sinadarin Nukliya ya na da matukar amfani kuma mai yawa, bai kamata a haramtawa wasu kasashe amfani da shi ba.
Banda haka ya ce, fasahar nukliya ci gaba ne, idan an hada tsarin addinin musulunci da ke gudanar da kasar, ci gaba ne mai yawa. Yace kasar Iran tana da arziki mai yawa tare da wadannan abubuwa biyu.
Yace ammam wasu kasashe a duniya suna sun su takaita wannan fasahar garesu su kadai, don su rika bautar da mutane. Basa son ganin Iran ta kai ga wannan fasahar, don haka sun samar da ra’ayin kin iraniyawa a duniya.