Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Na Cigaba Da Ba Da Rarar Kudi Ga Alhazan 2023
Published: 13th, March 2025 GMT
Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna tana kira ga dukkan alhazan da suka yi aikin hajji ta hannunta a shekarar 2023 da har yanzu ba a biya su rarar kudin da Hukumar Kula da aikin Hajji ta Kasa (NAHCON)ta dawo wa da Alhazan ba, cewa an rubuta masu takardar cek ta banki da za su je banki kai tsaye su karbi kudadensu.
Saboda haka, hukumar tana sanar da Alhazan da suka fito daga kananan hukumomin Kaduna ta Arewa da Kaduna ta Kudu da Kajuru, Igabi, Chikun, Birnin Gwari, su hallara a Cibiyar Musabakar Karatun Alkuráni a Kinkinau Tudun Wada Kaduna gobe Alhamis da Jibi Jumaáh 12 da 13 ga Maris don karbar wannan cek na kudadensu tun daga karfe 10 na safe.
Alhazan kananan hukumomin Ikara, Kubau, Kudan, Makarfi, Giwa, Soba, Sabon Gari da Zariya su hallara a hedkwatar Karamar hukumar Sabon Gari Ranar Asabar 14 ga Maris 2025 don raba masu cek na kudadensu na rara tun daga karfe 10 na safe.
Sauran alhazai da suka fito daga shiyya ta uku, wato Kudancin Jihar Kaduna, za su hadu a Cibiyar yi wa maniyyata Bita dake Kachiya ranar Lahadi 15 ga Maris don su karbi na su cek din.
Hukumar tana jawo hankalin alhazan cewa shaidar da take bukatar kowane alhaji ya gabatar it ace lambar kujera da kuma fasfo da suka yi aikin hajji a shekarar 2023.
Rel/Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Kamfanin Kasar Sin Zai Gudanar Da Aikin Farfado Da Muhallin Halittu Na Kogin Nairobi Na Kasar Kenya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp