Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-04-12@17:04:51 GMT

Cutuka Biyar Da Ake Ɗauka A Lokacin Zafi

Published: 13th, March 2025 GMT

Cutuka Biyar Da Ake Ɗauka A Lokacin Zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗi a baya-bayan nan dangane da ƙaruwar yanayin zafi a sassan ƙasar, yayin da jihohi da dama suke fuskantar ƙarin matsanancin zafi.

Gargaɗin ya kuma nuna cewa, tsananin zafin da za a yi fama da shi cikin kwanaki uku ko huɗu masu zuwa wanda zai haddasa damuwar da yanayin na zafi kan haifar a jihohi goma sha tara na ƙasar daga yankin arewa ta tsakiya da yankin gabashin ƙasar.

Kan haka ne muka tuntuɓi likita domin ya yi mana ƙarin bayani game da cututtuka biyar da aka fi kamuwa da su a lokacin zafi da kuma hanyoyin kare kai.

Sanƙarau – Dakta Hassan Ibrahim, likita a asibitin Biba da ke jihar Kaduna ya ce cutar sanƙarau na faruwa ne galibi idan aka samu cunkoson jama’a a wuri ɗaya da ya haɗu da zafi.

A cewarsa, “ƙwayoyin cuta za su shiga jikin mutum sai su shafi ƙwaƙwalwa sai a samu irin wannan.”

Zazzaɓin cizon sauro – Likitan ya ce idan yanayin zafi ya zo, mutane suna yawan buɗe jikinsu domin su sha iska. Ya ce “mutane sun fi zama a waje lokacin faɗuwar rana, lokacin da sauro ke tasiri da tafiyar da maleriya.

Hakan yana yawan taso da cutar maleriya a jikin mutane, kamar yadda likitan ya faɗa.

Fesowar ƙuraje – A lokacin zafi ne ake yawan zufa lamarin da ke janyo fesowar ƙuraje a jikn mutane wanda a cewar Dakta Hassan, idan ba a kula da su ba, “aka yi irin wata sosawa, yana iya kawo ciwo da wata ƙwayar cuta za ta iya ratsawa.”

Amai da gudawa – Dakta Hassan ya ce a irin wannan lokaci na zafi ne aka fi samun ƙuda da ruɓewar abinci. Ya ce idan ba a kula da abincin da muke ci ba, aka bari ƙuda suka yi damalmala a kai, hakan zai iya kawo ciwo a ciki idan aka ci.

Ƙonewar ruwa a jiki – A irin wannan yanayin, jikin mutum na yawan bushewa musamman a tsakanin dattijai. A cewar likitan, abin da ke sa mutum ya ji ƙishirwa, idan mutum na da rauni, ba za su samu jikinsu ya ankarar da su cewa su sha ruwa ba, ana so a riƙa shan ruwa a kai a kai.

Hanyoyin kariya

Dakta Hassan Ibrahim ya ce muhimman matakan da ya kamata mutane su ɗauka wajen kare kansu daga kamuwa da cuta a lokacin zafi shi ne tabbatar da cewa ana samun yanayin “shiga da fita ta iska” ta hanyar buɗe taga a wuraren kwana da wuraren aiki da kuma rage cunkoson jama’a a wuri guda.

Ya kuma ce akwai buƙatar a riƙa amfani da gidan sauro idan za a kwanta domin kare kai daga kamuwa da cutar maleriya inda ya ce akwai buƙatar a taƙaita zama a waje da yamma.

A cewar likitan, babban matakin da ya kamata mutane su kiyaye shi ne na tabbatar da tsaftar abincin da za ake ci musamman ƴaƴan itatuwa da kuma tabbatar da tsaftar jiki.

Ƙarin wani matakin shi ne yawaita wanka a kai a kai domin rage yanayin zafi a jiki.

Sai kuma yawaita shan ruwa domin gujewa ƙonewar ruwa a jiki inda ya shawarci masu azumi da su yawaita shan ruwa da zarar sun yi buɗa baki.

Abin da ya sa aka fi kamuwa da cututtuka a yanayin zafi

Dakta Hassan Ibrahim ya bayyana cewa dalilin shi ne, galibin cututtuka sun fi haɓaka a lokacin zafi saboda yanayin tsaurin jiki da inda jiki ke tafiya.

“Jiki yana da yadda yake gyara kansa a duk yanayin da ya shiga, lokacin zafi yana zuwa masa da ƙarin matsi da yadda jikin zai fitar da zafi da inda zai riƙe daidai.” in ji likitan.

“A lokacin zafi, mun ƙara wa jikinmu aiki, saboda a ciki ɗumi gare shi kuma yana son ya riƙe ɗumi kuma a lokacin zafi, jikinmu yana ƙara aikin fitar da ɗumi waje yana kuma ƙoƙarin samun abin sanyi da zai iya daidaita yanayin da yake tafiyar da aikin.”

Likitan ya ce a irin wannan yanayi da jiki ke tsintar kansa a lokacin zafi, “akwai rauni da ke tasar da cutuka da za su yi tasiri.”

A cewar shi, kashi 90 na cututtuka a duniya yana da alaƙa da wani abu na sarari saboda akwai ƙwayoyin cuta da suka fi tasiri a yanayin zafi.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Kariya Nijeriya yanayin zafi irin wannan

এছাড়াও পড়ুন:

Sojojin Sama Na HKI Kimani 1000 Guda New Suka Bukaci A Kawo Karshen Yaki A Gaza

Sojojin HKI wadanda suka yi ritaya da kuma masu jiran aiki ko Reserv sun watsa wata bukata da suka rubuta ta kawo karshen yakin da Benyamin Natanyahu yake jagoranta a Gaza.

Sojojin sun kara da cewa a halin yanzu yakin yana cimma manufar Natanyahu ne kawai, ba don manufar HKI ake yins a ba.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa, kafin su watsa takardar bukatar a yau Alhamis, babban kwamnadan sojojin sama na HKI Major General Tomer Bar ya ja kunnen sojojin kan cewa kada su watsa takardan, kuma y ace duk wanda ya sanya hannu a kan takardan yana iya korarsa daga rundunar sojojin sama na HKI.

Amma sojojin sun kammala da cewa a halin yanzu yakin yana cinye rayuwar fursononin da hamas take tsare da su a gaza ne da kuma sojojin da suke fafatawa da su.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsohon Kocin Super Eagles, Christian Chukwu, Ya Rasu Yana Da Shekaru 74
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 108
  • Hanyoyi Biyar Na Kare Kajin Gidan Gona Daga Tsananin Zafi
  • Sin: Idan Har Amurka Na Son Tattaunawa, Ya Zama Wajibi Ta Dakatar Da Aiwatar Da Matakan Gangaci
  • Sin Za Ta Kara Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar Zuwa 125%
  • Darasi daga rayuwar Dakta Idris AbdulAzeez Dutsen Tanshi
  • Mutum Shida Sun Mutu A Hatsarin Jirgi Mai Saukar Ungulu A Amurka
  • Shugaban Kasar Amurka Yace Yana Kokarin cimma yarjeniya da kasar China Dangane da Tiktok
  • Sojojin Sama Na HKI Kimani 1000 Guda New Suka Bukaci A Kawo Karshen Yaki A Gaza
  • Babu Wani Saɓani Tsakanin Tinubu Da Shettima — Jigon APC