’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani a Katsina
Published: 13th, March 2025 GMT
’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani, Abdulsalam Rabi’u Faskari, tare da mahaifinsa da ’yan uwansa a Jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata a kusa da Labin Bangori, yayin da suke dawowa Faskari bayan Abdulsalam ya samu lambar yabo wadda Gwamna Dikko Radda ya ba shi saboda nasarar da ya samu a gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa karo na 39 da aka gudanar a Birnin Kebbi, a Jihar Kebbi.
Wani jami’in gwamnati a Faskari, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da sace su.
“Malam Rabe da ’ya’yansa biyar, ciki har da Abdulsalam, wanda aka sace su a Bangori a kan titin Yankara. Har yanzu ba mu ji komai daga gare su ba.”
Abdulsalam, wanda ɗalibi ne a sashen likitanci na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, ya samu matsayi na farko a gasar a ɓangaren maza bayan ya haddace Alƙur’ani.
Har yanzu ’yan sanda a Katsina ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Gasar Karatu Gwarzo hari
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga na neman N100m kafin sakin Faston da suka sace a Kaduna
Wasu ’yan bindiga sun nemi a ba su Naira miliyan 100 kafin su sako wani fasto da suka yi garkuwa da shi a Jihar Kaduna.
Faston, mai suna Samson Ndah Ali, mai shekaru 30, yana aiki da cocin Evangelical Church Winning All (ECWA) da ke Mararaba Aboro, a Ƙaramar Hukumar Sanga.
Mutanen da suka saba ba ni abinci yanzu na neman taimako — Obi ’Yan bindiga sun mamaye garuruwa 64 a Filato — Gwamna MutfwangAn sace shi da misalin ƙarfe 1 na daren ranar Litinin, lokacin da ‘yan bindigar suka shiga gidansa.
Faston ya fara aiki a cocin ne ƙasa da makonni biyu kafin wannan lamarin ya faru.
Sakataren cocin, Yusuf Ambi, ya ce yana tare da Faston a daren da lamarin ya faru.
Ya ce washegari an kira shi a waya aka sanar da shi cewa faston ya ɓace.
Da ya isa gidansa, ya tarar ƙofofin a buɗe babu kowa a ciki.
Daga bisani, maharan suka kira, suka nemi a ba su Naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansa.
Ambi ya ce har yanzu suna tattaunawa da maharan.
Dakarun tsaro da suka haɗa da sojoji, ’yan sanda da jami’an DSS sun fara aiki tare don ceto faston.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ce zai yi bayani daga bisani.