Aminiya:
2025-03-13@14:01:56 GMT

Da amincewar Buhari na fice daga jam’iyyar APC — El-Rufai

Published: 13th, March 2025 GMT

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya tabbatar da cewa ya bar jam’iyyar APC ne da sanin Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.

El-Rufa’i ya bayyana komawarsa jam’iyyar SDP a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani a Katsina ’Yan sanda sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga a Abuja

Ya ce bai gamsu da yadda ake tafiyar da APC ba cikin shekaru biyu da suka gabata.

Yayin da yake zantawa da BBC Hausa, El-Rufa’i ya bayyana cewa ya sanar da Buhari kafin ya fice daga APC.

“Na faɗa masa game da shawarar da na yanke a ranar Juma’a. Ina yawan tuntuɓarsa kan harkokin siyasata,” in ji shi.

El-Rufa’i ya kuma tuna cewa lokacin da yake gwamna, ya taɓa miƙa wa Buhari jerin sunayen kwamishinonin da zai naɗa domin ya duba su, don tabbatar da cewa babu wanda ya taɓa zaginsa.

Da aka tambaye shi ko yana da shugabannin siyasa da yake bi, El-Rufa’i ya ce, “Ina da mutanen da nake tuntuɓa kafin na yanke hukunci, kuma Buhari shi ne na farko a cikinsu.”

Game da ko yana nadamar goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, sai ya ce, “Ba na nadama, amma wasu abubuwa sun ba ni mamaki.

“Na goyi bayan Tinubu ne saboda wasu shugabannin Musulmi na Yarbawa sun faɗa min cewa an mayar da su saniyar ware a siyasa, kuma na yi imanin cewa dole a bai wa Kudancin Najeriya mulki domin yin adalci da daidaito.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Buhari tsohon gwamna El Rufa i ya

এছাড়াও পড়ুন:

Pakisatan: An Kubutar Da Mutane 155 Sannan Yan Ta’adda 27 Sun Halaka  A Garkuwan Jirgin Fasinja A Jiya Talata

Jami’an tsaro a kasar Pakistan sun kubutar da mutane 155 daga cikin fasinjoji kimani 450 wadanda yan bindigan daga kungiyar ‘Baloch Liberation Army (BLA) suke garkuawa da su tun jiya, wadanda suka yi barazanar kashesu, idan gwamnatin Islamabad bata biya masu bukatunsu ba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar jami’an tsaro na kasar ta Pakisatan na cewa ya zuwa yanzu sun halaka yan bindiga 27. Sannan suna shirin kubutar da sauran nan gaba. Labarin ya kara da cewa daga cikin wadanda aka kubutar akwai mata da yara.

Kafin haka dai a jiya Talata ce yan bindiga na kungiyar BLA suka tsare wani jirgin fasinja mai suna ‘Jaffar Express’ dauke da fasinjoji 450 daga garin Quetta zuwa Peshawar.

Manufar garkuwan dai ita ce neman gwamnatin Pakisatn ta bawa yankin Baluchistan na kasar Pakisatan yencin kanta a matsayin kasa mai zaman kanta.

Labarin ya ce yan bindigan sun ta da nakiya ne suka lalata layin dogon, kafin su tilastawa Jirgin tsayawa.

Ya zuwa yanzu dai yan bindigan sun kashe mutane 3 daga cikin har da direban jirgin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tambuwal Ya Raba Shinkafa Ga Gidaje Dubu 30 A Sokoto
  • Peter Obi ya kusa dawowa APC — Hadimin Tinubu
  • Pakisatan: An Kubutar Da Mutane 155 Sannan Yan Ta’adda 27 Sun Halaka  A Garkuwan Jirgin Fasinja A Jiya Talata
  • Fiye da Falasdinawa 130 ne Isra’ila ta kashe tun bayan da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta
  • Tsohon shugaban Philippines ya faɗa komar ’yan sanda
  • Ficewar El-Rufai Daga APC Babban Rashi Ne – Tsohon Hadimin Buhari
  • El-Rufai Ya Yi Alƙawarin Haɗa Abokan Hamayya Don Yaƙar APC A Zaɓen 2027
  • UNRWA ta bukaci Isra’ila da ta bari a shigar da kayan agaji a Gaza
  • An hana tashe bana a Kano — Nalako