Aminiya:
2025-03-13@17:04:26 GMT

Za a mayar da waɗanda Lakurawa suka raba da garuruwansu – Gwamnan Kebbi

Published: 13th, March 2025 GMT

Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris ya tabbatar wa mutanen da hare-haren Lakurawa a ƙaramar hukumar Arewa ya raba da muhallansu cewa gwamnatinsa za ta ɗauki matakan gaggawa domin mayar da su garuruwansu.

Nasir Idris ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga mutanen da hare-hare ya raba da garuruwansu a sananin ƴangudun hijira da ke Kangiwa a jihar ranar Laraba.

Peter Obi na ganawar sirri da gwamnan Bauchi ’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani a Katsina

Sansanin ya tanadi waɗanda suka rasa muhallansu daga garuruwan Birnin Debe da Dan Marke, da Tambo, ne ke samun mafaka a sansanin inda wasu mahara ɗauke da makamai suka kai hari a ranar Asabar ɗin da ta gabata, inda suka kashe mutum 11 tare da ƙona gida ɗaya daga cikin ƙauyukan.

A wata sanarwa da mai baiwa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Yahaya Sarki ya fitar, ta ce Gwamna Idris ya kai ziyarar ne domin jajanta wa mutanen tare da ganewa idonsa halin da suke ciki, domin sanin matakin da gwamnatinsa za ta ɗauka.

Idris wanda ya bayyana alhininsa kan asarar rayuka da dukiyoyin da aka yi, ya yaba wa jami’an tsaro kan ƙoƙarin da suke yi na shawo kan rikicin.

Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ake yawan samun hare-haren daga Jihar Sakkwato da ke maƙwabtaka da Jamhuriyar Nijar.

“Na yaba wa Shugaban Ƙaramar Hukumar Arewa bisa gaggauta kafa sansanin ‘yan gudun hijira kamar yadda na umarce shi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gwamnan Jihar Kebbi Sakkwato

এছাড়াও পড়ুন:

Sanƙarau ta kashe mutum 26 a Kebbi

Aƙalla mutane 26 ne suka riga mu gida sakamakon ɓarkewar cutar Sanƙarau a wasu ƙananan hukumomi huɗu na Jihar Kebbi.

Da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar, Kwamishinan Lafiya, Yanusa Ismail, ya bayyana cewa an samu adadin mutane 248 da ake zargin sun kamu da cutar, inda daga cikin samfura 11 da aka gwada a ɗakin gwaje-gwaje, an tabbatar da cewa uku daga ciki kalau suke.

Ana fargabar ɓarkewar Sanƙarau a Sakkwato Lakurawa sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Kebbi

A cewar kwamishinan, ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Gwandu, Aleiro, da Jega, inda aka samu asarar rayuka 15 a Gwandu, shida a Jega, huɗu a Aleiro, ɗaya kuma a Argungu.

Ya ce an buɗe sansanonin keɓe waɗanda suka kamu, yayin da gwamnatin jihar ta soma ɗaukar matakan daƙile cutar ciki har da neman alluran rigakafin.

Kwamishinan ya gargaɗi jama’a game da shan magunguna da kansu, inda ya ce mutane su gaggauta zuwa asibiti mafi kusa domin yin gwaji a duk lokacin da ba su da lafiya don tabbatar da halin da suke ciki.

“Ya kamata mutane su guji yin barci a cikin ɗaki mai cunkoso. Su riƙa wanke hannayensu akai-akai bayan sun shiga bayan gida.

“Ya kamata su daina ziyartar sansanonin da aka keɓe marasa lafiyar kuma su tabbatar sun wanke ’ya’yan itatuwa da sauran kayan abinci kafin su ci don guje wa kamuwa da cutar Sanƙarau,” in ji shi.

Kwamishinan ya ce Gwamna Nasir Idris ya bayar da naira miliyan 30 domin siyan magunguna da sauran kayayyaki domin ɗaukar matakan daƙile cutar.

Sanƙarau wata cuta dai da ke janyo kumburi a wani rukuni na ƙwaƙwalwa ta kuma karya garkuwar ƙashin baya.

Alamomin cutar sun haɗa da sanƙarewar wuya, zazzaɓi mai zafi, rashin son haske, ruɗewa, ciwon kai da amai.

A bayan nan ne hukumar kula da yanayi ta Nijeriya NiMet ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar a fuskanci tsananin zafin rana a wasu jihohin ƙasar na tsawon kwanaki uku zuwa huɗu.

Cikin jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci ƙaruwar yanayi na zafin rana sun haɗa har da Kebbi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Peter Obi na ganawar sirri da gwamnan Bauchi
  • Gwamnan Zamfara Ya Haɗa Kai Da Kamfanonin Sin Don Habaka Tsaro
  • An Bada Umarnin Sake Tsugunar Da Wadanda Harin ‘Yan Bindiga Ya Rutsa Da Su A Kebbi
  • ‘Yansanda Sun Daƙile Yunƙurin Yin Garkuwa Da Mutanen 30 A Katsina
  • HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas
  • “Yan Ta’addan Syria Suna Boye Gawawwakin Mutanen Da Su Ka Yi Wa Kisan Gilla
  • Sanƙarau ta kashe mutum 26 a Kebbi
  • Lakurawa sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Kebbi
  • Abba zai naɗa sabon Kwamishina a Kano