An Bukaci Jama’a Su Rika Binciken Lafiyarsu Don Kare Kai Daga Cutar Koda
Published: 13th, March 2025 GMT
Babban Rajistara na Sashen kula da lafiyar Koda a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe (FTHG), Dr. Fidelis Linga, ya yi kira ga jama’a da su kula da lafiyarsu domin kaucewa kamuwa da cututtukan koda.
Ya bayyana hakan ga manema labarai a Gombe yayin bikin Ranar Koda ta Duniya.
Dr. Fidelis Linga ya jaddada cewa wasu munanan dabi’u kamar shan barasa, da taba, da cin abinci mara kyau, da zama babu motsa jiki na daga cikin dalilan da ke haddasa karuwar cututtukan da suka shafi Koda.
Ya yi nuni da mahimmancin yin gwaje-gwaje a asibiti akai-akai, da cin abinci mai kyau, da motsa jiki domin hana cutar koda.
Ya bayyana cewa, a duniya gaba ɗaya, mutane miliyan 850 na fama da cututtukan Koda, kuma daga cikinsu, mutane miliyan 11 ke mutuwa kowace shekara. Ya bayyana wannan matsala a matsayin abin damuwa.
Dr. Fidelis Linga ya ce Asibitin FTH Gombe na kokarin samar da karin na’urorin wanke koda da kuma ƙarin ma’aikatan lafiya domin kula da yawan marasa lafiya da ke zuwa asibitin don wanke Koda.
Ya ce wannan yunƙuri na da nufin inganta samun damar wanke Koda ga marasa lafiya da ke fama da cututtukan koda.
HUDU SHEHU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Cutar Koda
এছাড়াও পড়ুন:
HKI Ta Jefa Boma-Bomai A Kan Asbiti Tilo Da Ya Rage Yake Aiki A Arewacin Gaza
Jiragen yakin HKI HKI sun yi ruwan boma-bomai kan astin Al-Ahli, asbiti tilo da ya rage yake aiki a arewacin zirin Gaza, a safiyar yau Lahadi.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin HKI sun wargaza bangaren ’emagencu’ bukatar kula na gaggawa a asbitin da kuma kofar shiga asbitin. Har’ila yau hare-haren sun lalata bangaren Iskar Oxigen na kula da wadanda suke bukatar kula mai tsanani a asbiti. Kuma sanadiyyar haka mutane da dama sun rasa rayukansu awannan bangaren daga ciki har da wani yaro dan shekara 12 wanda ya ji rauni a kai.
Razan Al-Nahhas wani likita mai aiki a bangaren kula na gaggawa a asbitin ya fadawa kafafen yada labarai kan cewa wannan asbitin ne kawai dama yake aiki a arewacin Gaza, kuma a halin yanzu babu wani asbitin da ya rage a yankin.
Labarin ya kara da cewa bayan wadannan hare-hare kan asbitin na Al-Ahli, mutane da dama basu san inda zasu je don samun jinya ba.
Likitan ta kara da cewa kafin hare-hare na safiyar yau Lahadi dai marasa lafiya wadanda aka yankewa kafafu da kuma wadanda suka ji rauni a kai da kuma kirjinsu ne suka fi yawa a cikinsa. Sannan a halin yanzu babu inda zasu je sai wasu kananan asbitoci wadanda basu da kayakin aiki na kula da su. Kuma tuni wasu sun mutu bayan harin.