Gwamnati: Farashin Kayan Abinci Na Raguwa, Tattalin Arziki Na Ingantuwa
Published: 13th, March 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta ce ‘yan Najeriya sun fara samun sauki yayin da farashin kayan abinci ke raguwa da farashin fetur ke daidaita, kuma naira ke karɓar ƙarfi.
Da yake magana a taron manema labarai na ministoci karo na huɗu a Abuja, Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohamed Idris, ya ce ci gaban, suna nuna cewa gyare-gyaren tattalin arziki na Shugaba Bola Tinubu na yin tasiri.
Ya amince da wahalhalun da ‘yan Najeriya suka sha amma ya tabbatar da cewa hakan ya fara wucewa.
Mohamed Idris ya ce Gwamnatin Tarayya tana nan daram wajen daidaita tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.
A jawabinsa, Ministan Ilimi, Dr. Maruf Alausa, ya ce kudaden da aka ware za su karfafa ilimin fasaha da sana’o’i a kasan nan.
Ya bayyana cewa za a samar da dakunan gwaji a manyan makarantu shida na koyar da aikin likitanci domin inganta horo. “Muna mai da hankali kan horo a aikace, musamman a fannin sauya injunan mota zuwa na CNG, kula da hasken rana, da kuma noma na zamani domin samar da karin ayyukan yi.”
Haka nan, Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya ce yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin Emirates da Air Peace za ta karfafa harkokin jiragen saman cikin gida.
Gwamnati na kuma aiwatar da sabbin manufofi don tallafawa kamfanonin jiragen saman cikin gida 13, domin su ci gaba da yin gogayya a da ire iren su a duniya.
Keyamo ya tabbatar da cewa an inganta tashoshin jiragen Hajj don kyautata tsarin aikin hajji.
A halin yanzu, Jami’ar Kimiyya da Fasahar Jiragen Sama ta Afirka ta fara aiki gaba ɗaya, kuma Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniya da Boeing domin inganta sayan jirage da matakan tsaro.
A fannin amincewar kasa da kasa, tashoshin jirgin saman Port Harcourt da Abuja sun samu matsayi mafi kyau a Afirka dangane da tsaron fasinjoji da shirin gaggawa, a cewar Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Duniya (ACI) a Afirka ta Kudu.
Radio Nigeria/Adamu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Arziki Gwamnati Farashin Kayan Abinci Ingantuwa Raguwa
এছাড়াও পড়ুন:
Yaya ‘Yan Siyasar Amurka Ke Kasafta Harajin Ramuwar Gayya?
Manufar “ramuwar gayya” ba za ta daidaita gibin cinikin da kasar Amurka take fuskanta ba, illa ta daga farashin kayan da ake shigarwa kasar daga kasashen waje, da haddasa hadarin hauhawar farashin kaya a kasar, da kawo illa ga zaman rayuwar jama’ar kasar. A karshe Amurka ba za ta cimma burinta na zama a matsayin koli a duniya ba. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp