Aminiya:
2025-03-13@20:17:38 GMT

Kano: Gobara ta kashe mutum 7 da lalata kadarorin N50m a Fabrairu

Published: 13th, March 2025 GMT

Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu yayin da kadarori na sama da Naira miliyan 50 suka salwanta sanadiyyar gobarar a cikin watan Fabrairun 2025 a Jihar Kano.

Kakakin hukumar kashe gobara, Saminu Yusif Abdullahi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jihar.

Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu — Obasanjo Za a mayar da waɗanda Lakurawa suka raba da garuruwansu – Gwamnan Kebbi

Ya ce, a cikin watan Fabrairu, 2025, hukumar kashe gobara ta jihar ta samu jimillar kiraye-kirayen lambar wayar kashe gobara 77, da lambar kiran neman ceto 11 da kuma ƙararrakin gobara na ƙarya uku.

“Kimanin kadarori da gobara ta lalata a cikin watan Fabrairu sun kai darajar kuɗi N50,318,000 yayin da ƙiyasin kadarorin da jami’an kashe gobara na jihar suka ceto sun kai N180,318,000.

“Rayukan mutane bakwai ne suka salwanta sakamakon wata gobara da ta tashi yayin da kuma aka ceto rayukan mutum bakwai.”

Hukumar ta yi kira ga jama’a da su riƙa kula da wuta cikin kulawa domin gujewa afkuwar gobara yayin da aka shawarci masu ababen hawa da su riƙa tuka mota cikin kulawa tare da bin dokar hanya musamman a lokacin da suke tafiya kan manyan hanyoyi domin guje wa haɗurran mota.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Hukumar Kashe Gobara kashe gobara

এছাড়াও পড়ুন:

HOTUNA: Fashewar tankar gas ta kashe gomman mutane a Legas

Wata tanka ɗauke da gas ta yi bindiga a Jihar Legas da ke kudu maso yammacin Nijeriya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane da jikkata da dama.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata da dare a ƙarƙashin gadar mota ta Otedola, wadda tana daga cikin manyan hanyoyin da ke haɗe Legas da sauran sassan ƙasar.

HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas Ukraine ta amince da ƙudurin tsagaita wuta a fafatawarta da Rasha

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da tankar ke ƙoƙarin juyawa domin kai gas ɗin wani gidan mai, inda a nan ne ta faɗi ta yi bindiga.

Mutane da dama da suka shaida lamarin sun ce ya ƙazanta, sakamakon yadda wuta ta kama motoci da dama da kuma gidaje da ke kusa.

Wakilin kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya tattauna da wani mutum da ya tsira da ransa sakamakon lamarin.

“Tankar ta faɗo kan motata, inda ta tura ta gefen hanya. Sai na yi sauri na gudu bayan na gano cewa gas ne, sai tankar ta yi bindiga cikin ƙasa da minti uku,” in ji Ajayi Segun, wanda ya rasa motarsa ƙirar Sienna sakamakon faruwar lamarin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, a wani rahoto na wucin-gadi da ya fitar ya tabbatar da cewa lamarin ya rutsa da gidaje huɗu tare da haka kuma motoci 15 sun ƙone ƙurmus.

“Ana zargin hatsarin ya afku ne a lokacin da motar ke kokarin hawan hanyar Legas zuwa Ibadan ta gadar Otedola,” inji shi.

“Saboda haka, motar ta kife a kan hanya sannan ta yi bindiga nan take.”

“Har yanzu ana kididdige adadin rayukan mutanen da aka rasa, domin an gano gawawwaki biyu ne kawai.

“Lamarin ya kuma shafi wani asibiti mai zaman kansa, sai dai har yanzu babu cikakken bayani game da halin da waɗanda lamarin ya shafa a can.

“Za a ci gaba da bayar da rahoto a yayin da ake ci gaba da aikin ceto,” kamar yadda ya bayyana.

Jami’in Hukumar Agajin Gaggawa na Kasa (NEMA) shiyyar Kudu maso Yamma, Ibrahim Farinyole, ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa suna ci gaba da ƙididdige asarar da aka yi.

A cewarsa, mutum daya ya mutu yayin da wasu hudu suka jikkata baya ga motoci 14 da shaguna hudu da suka ƙone ƙurmus.

A cikin ‘yan watannin nan, an samu fashewar tankokin mai dama a Nijeriya inda kusan mutum 300 suka rasu a ƙasar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ruwan Sama Ya Lalata Gidaje Da Makarantu A Jihar Kwara
  • Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince Da Nada Kwamishina
  • ‘Yansanda Sun Daƙile Yunƙurin Yin Garkuwa Da Mutanen 30 A Katsina
  • ’Yan sanda sun ceto mutum 30 daga hannun ’yan bindiga a Katsina
  • HOTUNA: Fashewar tankar gas ta kashe gomman mutane a Legas
  • Mutum 1,010 Sun Mutu Sakamakon Hare-hare A Watan Fabrairu – Rahoto
  • Lakurawa sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Kebbi
  • An hana tashe bana a Kano — Nalako
  • ’Yan bindiga sun kashe manoma 14 a Ondo