Duniyarmu A Yau: Martani Jagora Ga Trump kan Shirin Nukliyar Kasar Iran
Published: 13th, March 2025 GMT
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau , shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakewa tsaro da sauransu, inda muke masu karin bayani sannan mu ji ra’ayin masana dangane da su gwagwadon lokacinda muke da shi da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
///… masu sauraro shirimmu nay au zai yi magana dangane da ‘Maida Martanin Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran ga zabin zabi biyun da shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bawa kasar dangane da shirinta na makamashin Nukliya na kasar, tattaunawa ko yaki’.
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan JMI ya maida martani ga shugaban kasar Amurka donal Trump wanda ya yi barazanar fadawa kasarsa da yaki idan taki da tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya.
Kamfanin dillancin labaran Parstoday ya nakalto jagoran yana fadar haka a ranar Laraban da ta gabata, a lokacinda yake ganawa da daliban Jami’o’ii daga yankuna daban-daban na kasar Iran.
Jagoran, da farko ya bayyana cewa, yadda shugaban kasar Amurka ya bayyanawa duniya cewa yana son tattaunawa da kasar Iran kan shirin na makamashin nukliya, yaudara ce, saboda ya nunawa duniya kan cewa Amurka tana son tattaunawa amma Iran bata son tattaunawa. Amma a gaskiya shi ne wannan shugaban ne ya yayyaga tattaunawar Iran da Amurka ta 2015 wanda ake kira JCPOA, ya fidda Amurka daga yarjeniya ta farko, ta yaya zamu tattauna da shi a yanzun bayan da shi ne ya yaga yarjeniya ta farko wanda ya nuna shi ba mutum ne mai mutunta al-kawali ba. Ta yaya zamu tattauna da shi al-hali ba zai mutunta sakamakon tattaunawa.
Imam Khaminaie ya kara da cewa tun farko, manufarmu tun farko ita ce don a dauke mana takunkuman tattalin arziki, amma tare da wucewar lokaci takunkuman tattalin arziki basu kaisu ga manufarsu ba.
Sannan dangane da zancen shugaban kasar Amurka na cewa ba zasu bar Iran ta mallaki makaman Nukliya ba, Imam Khaminaie, yace: Idan da muna son mallakar makaman Nukliya gwamnatin kasar Amurka bata isa ta hana mallakar makamin ba. Abinda ya sa bamu mallaki makaman nukliya ba, mu da radin kammu ne muka ce bama son makaman nukliya, mun ce bama son makaman saboda dalilan da muka bayyana a baya.
Dangane da barazanar farwa kasar Iran da yaki kuma, jagoran yace: ba abu ne na bangare guda ba, don iran tana iya maida martani kan Amurka, kuma tabbas Iran Amurka ta yi haka, JMI zata maida martani.
Jagoran ya kara da cewa: Idan Amurka ko wakilinta ya ya tabka wannan kuskuren su zasu fi cutuwa da shi.
Gaskiya ne, bawa neman yaki da kowa, don yaki bai da kyau, amma idan wani ya takalemu ya san cewa zamu rama.
Sannan yakamata duniya ta sani, sannan ita Amurka ta sani, a yau Amurka tana jada baya a al-amura da dama, kama daga tattalin arziki, tsarinta na kasashen waje, tafiyar da al-amuran cikin gida, zamantakewa, da wasu wurare da dama. Amurka tana kara rauni, Amurka a yau b aita ce Amurka a shekaru 20-30 da suka gabata ba.
Imam Khaminaie yace kada ku gani a cewa JMI ta rasa manya-manyan kawayenta a sheakra guda da ta gabata, ta yi rauni. Wannan ba haka yakeba, gaskiya ne mun rasah shugaba Ibrahim Ra’isi, mun rasa Sayyid Hassan nasarallah, mun rasa Isma’il Haniya, mun rasa Sayyid Safiyuddeen mun rasa Sinwar da sauransu, amma karfimmu ya karu bayan wannan rashin. Kada ku tsamman mun yi rauni.
Wannan duk tare da cewa rasa wadannan gwaraza kuma shahidan namu, abu ne wanda yake mana zafi a zukatammu, amma ko kanan bai sa mu rauni ba.
Kawancin masu gwagwarmaya a yankin suna da karfi sun kuma kara karfi idan an kwatanta da shekarar da ta gabata. Lebanon tana da karfi Falasdinu tana da karfi kuma zasu kara karfi kan karfi.
Banda haka yakamata ku gane kan cewa gwamnatin kasar Iran kama daga shugaban kasa da sauran jami’an gwamnatin kasar kansu a hade yakin kan matsayin da muka dauka. Hakama kansu a hade yake kan tallafawa kasashen Falasdinu da Lebanon tare da duk karfin da All..ya bamu, da yardarm All… mune da nasara.
Haka ma mutanen kasar Iran zasu ci gaba da goyon bayan shuwagabanninsu, kamar yadda suka yi a baya, wajen tallafawa wadanda aka zalunta a yanzu da kuma nan gaba. JMI ta dade tana gwagwarmaya da azzaluman shuwagabannin duniya. Kuma za ta ci gaba da wannan gwagwarmayan har illa ma sha’allah.
A wani wuri jagoran ya ce: Zaka ji suna magana suna cewa “Amerika da farko kafin kowa’ wanda yana nufin duk kasashen duniya, su sa bukatar A murka gaba da bukatunsu, sannan wannan son kai abu ne a fili kowa na gani, a ko wace rana.’.
Imam Khaminaei ya bayyana dalilan da suka sa kawancen masu gwagwarmaya suke kara karfi a ko wani lokaci a Iran da sauran wurare. Inda yace : Idan kasa tana da abubuwa 2 akida mai kyau sannan suna aiki tukuru, al-amuransu gaba daya ba zasu taba jada bay aba.
Ya ce: samun yardar All..ita ce manufar ko wani mutum mai hankali, sannan ya kara da cewa: samun nasara, samun ceto da tsira zai yu ne kawai karkashin shiryatarwan Ubangiji mahalicci All..wanda kuma shi ne sakamakon tsaron All..”
Jagoran ya kawo misalai guda biyu wadanda suke nuna irin gwagwarmayan da daliban makarantu a nan Iran suka faskanta a wannan zamani, da manya-manyan kasashe azzalumai, musamman Amurka.
Da farko yace a nan Iran kimani shekaru 100 da suka gabata, an yi lokacinda Iraniyawa sun kaskanta karkashin turawa wadanda suke daukar cewa sun ci gaba a kome, wannan hallin ya sa Iraniyawa sun zama mabiyan kasahsen yamma gaba daya sun mika kai, sun dauki mansu mabiya kawai.masu rauni. Basa iya bambanta tsakanin ci gaba na gaskiya da kuma na karya..
Imam Khomani (q) a siffanta wancan lokacin, wato a zamanin sarki Reza Phalawai, yace turawan ingila sun kawo shi kan gadon sarauta, sannan daga bayan suka cire shi a lokacinda suka ga dama. Suka dora dansa Muhamad Reza. A lokacin ya mika masu kai a kome. Ya mika masu Iran suna yi abinda suka ga dama da ita, Don raunin kasar a lokacin turawan ingila sun mamaye kudancin kasar a yayinda Rasha ta mamaye arewacin kasar. Sannan fara ya zo ya kashe dubban mutane, sun sashi ya danne mutane masu gwagwarmaya a cikin gida., sannan ya sanya hannun a yarjeniniya na kaskanci kamar, kamar yarjeniyar D’Arcy na man fetur. .
Jagoran ya bayyana cewa “gwagwarmayan kwace kamfanin manfetur a kasar Iran daga hannun turawa ne, ya fara farkar da mutanen kan mummunan niyya na turawa ga kasar Iran.
Wanda hakan ya rane matsayin da turawan suke da shi a wajen Iraniyawa kafin haka. Amma shuwagabannin lokacin, kamar Farai ministan Dr Mohammad Musaddik yana son taimako Amurka don ficewa da zaluncin Burtaniya, sai gashi Amurka ce ta kulla makirvin yi masa juyin mulki.
Yace juyin mulkin da Amurka ta yi wa Musaddik a shekara 1953 ya nuna cewa dogaro da kasashen yamma yana hana kasa ci gaba, kuma ko wanne daga cikinsu.
Ya kuma tabbatar da cewa kasashen yamma suna taimakon wani ne kawai idan akwai bukatarsu a ciki, kokuma idan akwai ibanda zasu amfana da shi.
Sannan aka sami daliban jami’o’ii suka fara farkawa suka fara tunkarar Amurka da kuma nuna rashin amincewarsu da ita. Da farko sun fito zanga zangar nuna rashin amincewarsu da ziyarar shugaba Nixson a ranar 7 ga watan Decemban shekara 1953. Inda sarka shay a sa aka kashe dalibai uku.
In ba don nasarar juyin juya halin musulunci a shekara 1979 ba, da kasar zata rasa kome, ta zama tana hannun turawannan, sannan mutanen sai kara cin baya zasu yi ta yi.
Ya ce Imam Khomaini(q) da kekkyawar jagorancin ya sami nasarar fahintar da mutane, munin shirin Amurka ga kasar da kuma hada kansu kan abinda zai basu yancin kai da dogaro da kansu. Sannan ya karfafa guiwarsu kan cewa zasu iya samun ci gaban da wadannan kasashe suka samu har ma su wucesu. Sai gashi jajircewar mutanen kasar da shuwagabanninsu ya kai ga inda Iran take a yau.
JMI ce kadai take iya sanya bukatunta a gaba kafin na ko wace kasa, a wannan yankin. Yace kokarin kasashen yamma a halin yanzu shi ne sake maida kasar zuwa yanayi kafin nasarrar juyin juya halin musulunci. Na kaskasci da mika kai da kuma ga bukatunsu.
Daga karshe jagoran ya bayyana cewa, Iran ba zata taba amincewa ta koma inda juyin juya halin musulunci ya fito da ita ba.
Saboda ta dandana dadin samun yenci da kuma ci gaban da ita take tsarawa kanta, ba tare da shishigin wata kasa ba.
Wannan duk tare da cewa bata kai inda ta kai, ba tare da fuskantar matsaloli wadanda wadannan kasashe masu girman kai suke haddasawa ba.
Daga karshe duk wata kasa da ta sami akida mai kyua, ta sanya samun yardarm All..shi a gaba, ba wanda ya isa ya sami nasara a kanta. Kuma da rayuwa da mutuwa a daidailun mutanensu duk daya ne, saboda hakan ba zai dakatar da ci gaban da suke yi a al-amuran duniya ba, ga kuma fatan samun ramahar All..a gobe kiyama. Jinin shahidan JMI bai tafi a banza ba, saboda da shi ne aka shayar da itaciyar musulunci, wanda a halin yanzu ana hangen rassansa a ko ina a duniya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: juyin juya halin musulunci shugaban kasar Amurka makaman nukliya tattalin arziki a kasar Iran
এছাড়াও পড়ুন:
Sharhin Dangane da: Atisayen Damarar Tsaro Ta 2025 Tsakanin Kasashen China, Rasha Da Iran
Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da ‘Atisayen sojojin ruwa mai taken (“damarar tsaro na shekara ta 2025”) wandake ke gudana a nan Iran. Wanda ni tahir amin zan karanta.
////.. A ranar litinin da ta gabata ce sojojin ruwa na kasashen China, Rasha da kuma Iran suka fara atisayen sojojin ruwa na hadin giwan kasashen uku, wanda suka sanya masa suna :damarar tsaro na shekara ta 2025″ wanda kuma ke gudana a halin yanzu a arewacin tekun Indiya da ke kudu maso gabacin kasar Iran da tekun farisa da kuma tekun Omman.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa atisayen wanda zai dauki kwanaki uku cur ana gudanar da shi, zai maida hankali wajen al-amuran da suka shafi tsaron ruwa na yankuna daban-daban a inda wadanda kasashe suke kula da su.
Labarin ya kara da cewa a yau talata sojojin kasashen uku sun gudanar da wani bangare na atisayen. Rear admiral Mostafa Tajeddine mataimakin kwamandan gudanarwa na sojojin Ruwa na kasar Iran ne ya bayyana haka. Ya kuma kara da cewa wannan bangaren daukar hotuna na atisayen ya kammala kamar yadda aka tsara.
Tajuddine ya kara da cewa ana daukar hotunan yadda atisayen ke gudana daga jirgin ruwa wanda yake kula da hakan daga cikin jiragen ruwan yaki sojojin ruwa na rundunar IRGC. Ya kuma ce JMI tana da shirin kula da zaman lafiya a yankunan ruwa daban –daban a kasashe yankin da kuma na sauran kasashen duniya.
Shi ma a jawabinsa Rear admiral Shahram Irani, babban kwamandan sojojin Ruwa na JMI ya bayyana cewa, yayi watsi da zancen shugaban kasar Amurka Donal Trump dangane da wannan atisayen na cewa, Amurka tafi taron kasashen Iran Rasha da kuma China, ya kuma bayyana cewa wannan kalaman ‘rudu ne’ kawai wanda shugaban ya shiga.
Kafin haka dai shugaban kasar na Amurka yace bai damu da atisayen kasashen uku suka yi a tekun faraisa, don ya san Amurka ta fi su karfi gaba daya. Irani ya ce manufar kasashen uku a wannan atisayen, mai suna ‘damarar tsaro na shekara ta 2025″ ita ce tabbatar da tsaro a yankin da kuma duniya, sabanin abinda Amurka take yi na samar da tashe-tashen hankula a cikinta.
Ya kuma kara da cewa, yakama ta gwamnatin Amurka ta sani, yawan kasashen da suke da karfin sojojin ruwa a duniya sun kara, kuma suna gwada karfinsu a wurare da dama a yankin Asiya da kuma wasu wurare a duniya. Ya ce kasashen kungiyar Shanghai da Brics da dama suna da karfin tabbatar da zaman lafiya a yankuna da dama a duniya. Suna da karfin ganin harkokin tattalin arziki na yankunansu da kuma kasashensu suna gudana da kyau.
Ya ce wasu kasashe banda wadannan uku, suna shirye-shiryen hadewa da wannan atisayen nan gaba. Wannan dai shi ne atisay karo na 7th wadanda wadannan kasashe uku China Iran da kuma Rasha, wanda yake karfafa kwarewarsu a tabbatar da tsaro a cikin ruwayen kasashen yankin, har’ila yau akwai wasu kasashe da dama daga yankin da kuma wasu kasashe daga nesa suna a matsayin masu kallo a wannan atisayen.
Banda haka wadannan atisayen zai hana kan wadannan kasashe don cimma manufa guda ta samar da zaman lafiya a dukkan hanyoyin zirga zirgan kasuwanci da hulda ta cikin ruwa a yankin da kuma duniya.
A cikin yan kwanakin nan ne shugaban kasar Amurka take barazanar kaiwa cibiyoyin nukliya na kasar Iran, don hanata, abinda ya kira makamin Nkliya. Ko kuma iran ta amince ta zauna da Amurka ita kadai don ta fada mata abinda zata yi, da abinda ba zatayi ba a fagen makamashin nukliya. Wanda Iran tace ba zata taba zama da Amurka don tattauna batun shirinta na makamashin nukliya ba.
Tun kafin ya sake dawowa kan kujerar shugabancin kasar Amurka, a karo na biyu, shugaban yake barzanar zai tursaswa iran ta amince don tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya.
Amma idan ta ki amincewa zai yi amfani da karfin don wargaza shirinta na makamshin nukliya don ba zata amince iran ta mallaka makaman Nukliya ba.