Sojojin Iran Sun Ce A Shirye Suke Su Mayar Da Martani Akan Kowace Barazana Ga Tsaron Kasar
Published: 13th, March 2025 GMT
Kwamandan sojojin kasa na JMI Laftanar-Janar Kiyomars Haydari ya bada sanarwan cewa; A bisa umranin jagoran juyin musulunci Imam Sayyid Ali Khamnei , sojojin kasa na JMI suna cikin shirin ko ta kwana domin mayar da martani akan kowace irin barazana ga tsaron kasar.
Laftanar janar Haidari ya kuma ce: A halin yanzu da akwai rundunoni 11 da su ke cikin shiri a kan iyakoki kasar domin sanya idanu da tattara bayanai saboda tabbatar da tsaron kasar.
Kwamandan sojan kasa na Iran ya kuma ce; Saboda sojojin suna cikin shirin ko-ta-kwana ne, barazanar da ake fuskanta ta zagwanye, da hakan ya ke a matsayin kandagarko.
Har’ila yau Laftanar janar Haidari ya yi ishara da rawar dajin da sojojin kasa su ka yi, har sau uku a cikin shekarar hijira Shamshiyya ta 1403. Sannan da wadanda za su a sabuwar shekara da za ta shigo.
Ya ce za’a gudanar da wani atisayen wanda zai da ce da girman barazanar da ake fuskanta.
Haidari ya kammala da cewa a sabuwar shekarar Iran da za a shiga, za ta zama ta kara yawan karfin tsaron kasar ne, domin takawa makiya birki.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Hukumar Makamashin Nukliya Ta Kasar Iran Ya Ce Dukka Ayyukan Makamashin Nukliya A Cikin Gida Suna Tafiya Da Karfinsu
Shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran ya ce kasashen wamma suna son kebe kansu da fasahar nukliya a tsakaninsu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Muhammad Eslamu shugaban hukumar AEOI yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa kamfanin makamashin nukliya na kasar Iran ya kafa a kasar Iran kuma ba wanda ya isa ya kauda shi. Sabanin abinda kasashen yamma suke so na hana sauran kasashen duniya mallaka fasahar nukliya, da kuma dogara da su kadai, su bada abinda suka ga dama ko su hana gaba daya.
Ya ce JMI ta wuce wasu kasashen yamma a ayyuka da kuma sani da sarrafa makamashin Uranium, wanda ya tada hankalin wadannan kasashe, kuma suke sun han awasu kasashen duniya bin sawun kasar Iran na zama yentattu a wannan fage.
Islami ya kara da cewa kamfanin makamashin nukliya na kasar Iran ya kai wani matsayinda yana taiamakawa sauran kamfanoni na cikin gida ba tare da bukatar dogaro da kwararru ko kuma taimakon kasashen waje ba. Ya ce a halin yanzu iran na samar da wutan lantarki mai karfin magewats 20,000 tare da Makamashin Nukliya.