’Yan bindiga sun sace mutum 10 da raunata 2 a Kaduna
Published: 13th, March 2025 GMT
Wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu ’yan ƙauye su goma daga wasu unguwanni uku da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne a daren ranar Larabar, da misalin ƙarfe 2 na tsakar dare inda wasu gungun ’yan bindiga suka kai farmaki a unguwar Unguwan Yashi-Maraban Kajuru tare da yin garkuwa da mutane shida.
Waɗanda aka sace su ne: God-Dream Ladan, Lady God-Dream, Philip Mudakas, Mercy Philip, Bitrus Philip, da Gmen Philip.
Hakazalika, a ƙauyen Makyali, wasu mutane biyu sun samu raunuka na harbin bindiga, kuma a halin yanzu ana jinyarsu a asibitin Maraban Kajuru bayan ’yan bindiga sun kai wa unguwar hari.
An kuma yi garkuwa da wasu mata biyu Rahina Yahaya da Zulai Yahaya a ƙauyen. Waɗanda suka jikkata dai sun haɗa da: Ubale Yahaya da Abdullahi.
An samu rahoton cewa gungun ’yan bindigan sun koma Ungwan Mudi Doka da misalin ƙarfe 4 na asubahi inda suka yi garkuwa da wasu mutane biyu – Amos Michael da Samita Amos.
Muƙaddashin Hakimin Kufana, Stephen Maikori ya tabbatarwa Aminiya faruwar lamarin a ranar Alhamis, inda ya ce a baya-bayan nan an samu raguwar kai hare-haren, amma kuma a cikin makon nan ne suka sake kunno kai.
“Ya zuwa yanzu, an tafi da mutane goma, yayin da biyu suka samu raunuka, yanzu suna karɓar magani. Muna roƙon a ƙara ɗaukar matakan tsaro cikin gaggawa da ɗaukar matakin ceton rayuka da dukiyoyi a cikin wannan yankin,” in ji shi.
Ya kuma ƙara da cewa an kai rahoton faruwar lamarin ga hukumomin tsaro a kan lamarin. A halin da ake ciki dai har yanzu gwamnatin jihar da rundunar ’yan sanda ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan, an kasa samunsa ta wayar tarho har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutum Ɗaya A Bauchi, Wasu Sun Jikkata
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp