Kasar Sin Ce Ke Kan Gaba A Matsayin Kasar Da Ta Fi Samun Jari Daga Ketare
Published: 14th, March 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta ce alkaluma sun nuna cewa, har yanzu kasar Sin ce ke kan gaba a duniya a matsayin wacce ta fi samun jari daga kasashen waje, kuma tana maraba da kamfanonin kasashen wajen su zo su kara zuba jari.
Mao Ning ta kara da cewa, ba tare da la’akari da sauyin da za a gani a duniya ba, kasar Sin za ta cika alkawarinta na fadada bude kofarta.
Da take amsa tambaya game da manufar kasar ta daukewa wasu kasashe neman visa, Mao Ning ta ce kasar ta soke neman visa ga kasashe 38 da kuma tsawaita lokacin yada zango a kasar ba tare da visa ba zuwa sa’o’i 240 ga kasashe 54. Ta ce a bara, sama da baki miliyan 20 ne suka shigo kasar ba tare da visa ba, adadin da ya karu da kaso 112 kan na shekarar da ta gabace ta. Ta kara da cewa, kasar Sin za ta kaddamar da karin matakai domin saukaka shigowa kasar. Haka kuma, tana maraba da baki abokai daga fadin duniya, domin su zo su ganewa idanunsu kasar Sin ta ainihi mai kyau da bude kofa. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Vladimr Putin Na Kasar Rasha Ya Amince Da Tsagaita Wuta A Yakin Ukraine
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bada sanarwan amincewa da tsagaita budewa juna wuta tsakanin Rasha da Ukraine na tsawon kwanaki 30, wanda shugaban kasar Amurka Donal Trump ya gabatar, sai dai akwai bukatar karin bayani filla-filla kan yadda hakan zai kasance. Sannan yana fadar wannan zai kai ga tsagaita budewa juna wata na din din din.
Shafin yanar Gizo na labarai Africa News ya nakalto shugaban yana fadar haka a yau Alhamis. Ya kuma kara da cewa akwai bukatar a kara tattaunawa da abokammu na kasar Amurka don kara fayyace yadda tsagaita wutan zai kasance.
Daga cikin abubuwan da za’a tattauna akwai yiyuwar sabawa yarjeniyar da kuma matakan da za’a dauka don hana hakan faruwa ko kuma idan ya faru matakan da yakamata a dauka, wa kuma zai kula da wannan bangaren.
Sannan ya kara da cewa shin kasar Ukraine zata yi amfani da wadannan kwanaki 30 don ta kara tara makamai da kuma shirin fara sabon yakin ne.
Shugaba Putin ya kara da cewa: Ya amince da tsaida yaki, da kuma fatan tsaida shi zai share hanyar samar da zaman lafiya na din din din tsakanin kasashen biyu da kuma yankin, tare da magance matsalolin da suka haddasa yakin.
Daga karshe shugaban ya godewa shugaban kasar Amurka Donal Trump saboda bada lokacinsa don kashe wutan da ke ci a kasar Ukraine fiye da shekari 3 da suka gabata.
Sannan yace kasar Rasha ba zata amince da sojojin tabbatar da zaman lafiya daga kasahsen kungiyar tsaro ta nato ba.