Ƙasar Sin Ta Yi Alƙawarin Ƙarfafa Hulɗar Da Ke Tsakaninta Da Kano
Published: 14th, March 2025 GMT
A cewar Dunbai, gwamnatin kasar Sin tana kara inganta alakarta da jihar Kano a fannonin samar da abinci, kayayyakin more rayuwa, ilimi, tare da kasuwanci da gwamnatin jihar.
A fannin aikin gona, wakilin kasar Sin ya yi nuni da muhimmancin samar da abinci a jihar Kano, inda ya ce, jihar da ke da dimbin al’umma kamar kasar Sin, ta cancanci amfani da fasahohin zamani a fannin noma don karfafa samar da dimbin abinci.
A cikin sanarwar, Mista Dunhai ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta ci moriyar damar da kasar Sin ta samar na zuba jari a Nijeriya na sama da dala tiriliyan 20, domin farfado da ci gaban masana’antu da kasuwanci.
A nasa jawabin, Gwamna Yusuf, wanda ya tarbi tawagar jama’ar Sinawa da hannu biyu, ya kara da cewa, a shirye gwamnatinsa ta ke ta kara himma wajen hadin gwiwa domin ci gaban jihar baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Bahrain Ta Kara Kaimi Wajen Kama Yan Adawa Daga Ciki Har Da Yara Kanana
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama a kasar Bahrain ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kara yawan kama mutane yan adawa daga ciki har da yara kanana saboda shiga cikin zanga-zanga, ko kuma bayyana ra’ayinsu na siyasa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar kare hakkin bil’adama ta ” The Americans for Democracy & Human Rights in Bahrain (ADHRB), ta kuma kara da cewa, bayan afwar da gwamnatin Bahrain ta yi wa yan adawar kasar kimani 1,584 a cikin watan Afrilun shekara ta 2024 da ya gabata, daga ciki har da yara 40, amma daga baya ta fara kama yan adawan tana tsaresu. Suna kama dukan wanda ya nuna kiyyarsa, ko ya bayyana ra’ayinsa na siyasa, ko kuma ya fito zanga-zanga a cikin kasar, daga ciki har da yara kanana. Musamman a tsakanin watannin Augusta zuwa watan Decemban shekara ta 2024.
Shugaban kungiyar kare hakkin bil’adama ta ADHRB Hussain Abdullah yayi allawadai da kama yan adawa musamman yara kanana kimani 11 da mahukuntan kasar ta Bahrain suka tsare, ba tare da gabatar da su a gaban kotu ba. Har’ila yau tare da hana iyayensu ziyartarsu, ko kuma sanin inda suke.
Sannan akwai rahoton azabtar da wasu daga cikinsu, da hanasu abinci mai gina jiki da kuma rashin kula da lafiyarsu ko basu magani.