Aminiya:
2025-03-14@08:14:52 GMT

Muƙarraban Uba Sani ne suka sace tsohon Kwamishina na – El-Rufai

Published: 14th, March 2025 GMT

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya fasa baragurbin ƙwai kan zargin sace Jafaru Sani, tsohon Kwamishina a gwamnatinsa.

El-Rufai, wanda ya mulki Jihar Kaduna daga 2015 zuwa 2023 kafin ya miƙa mulki ga Sanata Uba Sani, wanda shi ne ɗan takarar da ya fi so ya gaje shi, ya bayyana wannan batu ne a shafinsa na Facebook da aka tantance sahihancinsa a ranar Alhamis.

Tsaro: Shugaban Ƙaramar Hukuma ya tabbatar da haɗa kai da Sarakuna Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu — Obasanjo

A cewarsa, an tsare tsohon Kwamishinan na shi ne a kurkuku ba bisa ƙa’ida ba.

El-Rufai ya ce, yana da tabbacin ana cin zarafin abokin nasa ne saboda ya fice daga Jam’iyyar APC zuwa SDP.

“An sace abokin aikinmu kuma tsohon kwamishina mai ƙwazo a zamanin mulkin El-Rufai, Malam Jafaru Sani, an sace shi ne a Kaduna da rana tsaka, yana ta hannun ‘yan fashin dajin Uba Sani da ke cewa su ’yan sanda ne!

“An tsare Jafaru a kurkuku ba tare da wata takardar sammaci daga ‘yan sanda ko ta tuhuma daga Ma’aikatar Shari’a ta Jiha ba.

“Bayan bincike, mun gano cewa ana zarginsa da safarar kuɗi. Amma ainihin laifin Jafaru shi ne ficewarsa daga APC zuwa SDP.

“Wannan salon zaluncin iri ɗaya ne da wanda aka taɓa yi wa wani abokinmu, Bashir Saidu, wanda aka sace a ranar 31 ga Disamba, 2024, aka tsare shi na tsawon kwanaki 50 kafin a bayar da belinsa!

“Rawar da wasu alƙalai ke takawa a shari’ar Kaduna abu ne mai matuƙar damuwa. Muna sa ido kuma muna jira domin babu wani yanayi da zai dawwama, kuma ranar hisabi za ta zo.”

Har yanzu gwamnatin Jihar Kaduna ba ta mayar da martani kan waɗannan zarge-zargen da El-Rufai ya yi ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gwamna Uba Sani

এছাড়াও পড়ুন:

Tsohon shugaban Philippines ya faɗa komar ’yan sanda

’Yan sanda sun cafke tsohon shugaban ƙasar Philippines,  Rodrigo Duterte a filin jirgin saman birnin Manila a wannan Talatar.

Mista Duterte ya faɗa komar ’yan sandan ne bisa sammacin Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, jim kaɗan da saukarsa daga birnin Hong Kong.

Jihohi 12 da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet Ainihin abin da ke kawo wa Manchester United koma baya

Hatsaniya ta ɓarke a filin jirgin saman lokacin da ’yan sanda suka kama Mista Duterte, sakamakon tirjiya daga masu tsaron lafiyarsa da likitansa da kuma lauyoyinsa, wadanda ke zargin cewa an take masa haƙƙinsa da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi.

Fadar shugaban ƙasar Ferdinand Marcos ta ce tsohon shugaban na fuskantar tuhumar kisan ɗimbin jama’a a lokacin mulkinsa, wanda ya fake da yaƙi da masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

A lokacin dai ya sha alwashin kawar da fataucin miyagun ƙwayoyi, amma ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’dama sun ce lamarin ya rikiɗe zuwa wani abu daban, inda ake zargin ’yan sanda da kashe dubban mutane, ciki har da waɗanda da ba su ji ba ba su gani ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji sun ceto mutum 7 daga hannun ’yan bindiga a Filato 
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 10 da raunata 2 a Kaduna
  • Da amincewar Buhari na fice daga jam’iyyar APC — El-Rufai
  • ’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani a Katsina
  • Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Na Cigaba Da Ba Da Rarar Kudi Ga Alhazan 2023
  • ’Yan sanda sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga a Abuja
  • ’Yan sanda sun ceto mutum 30 daga hannun ’yan bindiga a Katsina
  • Tsohon shugaban Philippines ya faɗa komar ’yan sanda
  • Ficewar El-Rufai Daga APC Babban Rashi Ne – Tsohon Hadimin Buhari