Me Ya Sa Jama’ar Turai Ke Adawa Da Sayen Kayayyaki Kirar Amurka?
Published: 14th, March 2025 GMT
A wani bangare na daban kuwa, dole ne ’yan siyasar Turai su yi tunani cewa, jama’arsu sun dauki irin wannan mataki ne ba ma kawai bisa bukatunsu na sayayya ba, har ma ya kasance mataki ne na nuna adawa da babakeren Amurka, da bukatunsu na dogaro da kansu a bangaren manyan tsare-tsare.
Huldar Amurka da Turai ta wannan fuskar ta yi hannun riga da ainihin ma’anar zumunci, inda lamarin ya yi rauni matuka, kuma tabbas matukar Turai ba ta nemi dogaro da kanta ba, za ta yi asara daga barazana da kalubalen da Amurka take haifarwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Tarayyar Turai ta yi barazanar sake kakaba wa Syria takunkumi
Jami’ar kula da manufofin ketare ta Tarayyar Turai, Kaya Kalas, ta tabbatar da cewa, EU za ta iya sake kakaba takunkumi kan kasar Syria, idan aka samu tabarbarewar lamurra, tana mai nuni da yadda ake cin zarafin fararen hula a gabar tekun Syria.
Kaya Kalas ta shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, “Muna shirye-shiryen mayar da takunkumi kan Syria, idan muka ga tabarbarewar lamurra na ci gaba, inda ta jaddada cewa, dole ne mika mulki ya kasance cikin lumana da kuma hadin kai, kuma dole ne a kare fararen hula a kowane hali.”
Ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki na waje da su mutunta hadin kan Syria, da kuma iko da iyakokinta.”